Hanna 43

194 23 0
                                    

*HANNA*.......💥

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

   *43*

Daidai wani super market yay parking bayan ya kashe motar yace " ki jira na fito ko" make kafad'a tai tace "nidai zan shiga yay,,," shiru tai ganin kallan da yake mata ta saki murmushi tace "nidai inason shiga baby" murmushi yay yaja dogon hancinta yace "ohk"
   Da kansa ya fito ya bude mata murfin motar bayan ya taimaka mata ta fito ya gyara mata hijab din dake jikinta ya wanda duk akan idon Mk ne da yakejin zuciyarsa kamar tai tsalle ta fito sbd kishi ,
   Kai tsaye ya fito bayan ya sa glass me duhu  yana wani taku cikin fushi ya shiga super market d'in ,
   Ta bakin glass din dake idonsa yake kallan duk wani motsinsu, yana kallo hanna ta dagawa haydar hannu ta shige wata corner na kayan zaki kala kala , cikin nishadi ta shiga daukar duk sweet d'in datai mata tana jefawa a kwandon dake hannunta , daidai ta dora hannunta kan wani biscuits shima ya dora nasa hannun,
  Da sauri ta d'aga kai ta kallesa, gabantane yay wani mummunan faduwa ta saki kwandon da ta kusa cikashi da sweet tana zaro Ido a firgice, cikin azama ta juya zata wuce ya janyota da karfi kiris ya rage ta fad'a kan jikinsa  daidai shi kuma haydar ya sanyo kai wajen , still yay a wajen zuciyarsa tana dokawa da karfi , da wani irin fushi Hanna ta d'aga hannu ta sauke masa lafiyayyan mari har sau biyu kafin ta fizge jikinta tana sakin wani kukan takaici da bakin cikin tsanarta, ta juya da sassarfa zatabar wajan ta had'a Ido da haydar idanunsa sun kad'a sunyi jajur,
  Wani irin tsinkewa zuciyarta tai ta tsaya cak ganin yana tahowa inda take , rintse ido tai jikintaa na karkarwa tana jiran taji saukar mari ,  hannunta haydar ya kamo ya janyota jikinsa yana aikawa da Mk da ya kame tun marin dayasha wani irin kallo ,
  Sakinta yay ya taka gaban Mk da wani irin amo yace " zan buga mata last warning daga yau I mean daga yau inda matata take ka sake kallo billah sai nayi shari,a dakai , akuyancinka ya tsaya wajen marasa tarbiyya irinka , ba shawara nake bakaba gargadine inka d'auka fine ka taimaki kanka"
  Daga haka yaja hannunta suka bar wajan , har sukaje gida bai sake kallan inda take ba shi kad'ai sai huci yake , sanda suka iso kai tsaye dama ya kashe motar ko kallanta baiyiba ya fito ,cikin sanyin jiki da damuwa ta kwaso ledojin da suke bayan motar ta biyuso tanajin me gadi yana musu sannu da dawowa bata samu damar amsawaba ,
   Har kusan karfe 10 na dare bata sake za haydar a idonta, tana zaune shiru sai ajiyar zuciya take saukewa kana kallanta kasan taci kuka ta koshi, tana zaune taji sakkowarsa ta d'aga kai,had'a Ido sukai ya dauke kansa kamar bai gantaba ya wuce ya kashe kayan kallo ya kuma hayewa , ta bisa da kallo wani hawaye na sakko mata ta tashi da sauri ta bisa ,
  Gab da zai shiga bedroom dinsa ta cimmasa a sanyaye tace "Dan Allah baby ka saur,,," da sauri ha dakatar da ita a fusace yace "leave me pls banason hayaniya" daga haka ya shiga bedroom din ya barta tsaye tana hawaye cike da  takaici,  dakinta ta shige ta koma ta saki wani irin kuka me cin rai , saida tai me isarta sannan tai shiru tana ta juye juye ,karo na farko kenan za suka Fara raba makwanci tun bayan auransu ,dakyar ta samu wajen karfe d'aya na dare baccin ya dauketa ,
   Washe gari kamar yadda ta saba ta kammala breakfast dinta tai tai wanka tasa wani riga da sket , rigar iya mamanta ta rufe sai sket din daya kasance mini sket ne , batai kwalliya ba sai turarukanta data fesa ta sakko downstairs tanajin wani bacin rai da takaici ,
  Dan da asuba koda tai sallah har dakinsa ta shiga da niyyar bashi hakuri ya katseta a fusace ko gaisuwar da zatai mai bai bari tayiba yace taje yana bukatar hutu,
   Tana zaune tana kallo ya sakko cikin shirinsa na fita office batare data kallesa ba fa mike ganin ya zauna a kujerar dinning ta zuba masa duk abinda tasan zaici tabar masa wajen , ta gefen Ido ya kalleta ya dauke kai ya faracin abincin data zuba masa,
   Yana kammalawa ya goge bakinsa da tissue ya dau briefcase dinsa bai kalletaba yace " na tafi"
  Batare data kallesa ba itama tace "ohk" juyowa yay Jin yadda tai magana ya dauke kai ya fice tabi bayansa da kallo kamar zatai kuka.

HannahWhere stories live. Discover now