Hannah part 8

408 24 0
                                    

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣8️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Bugun duniya mamii tayiwa haydar amma shiru tuni hankalinta yayi mugun tashi gashi sai wani irin nishi taji yana tashi a d'akin ,jiki na rawa ta sakko kallo d'aya hanna taiwa mamii ta fashe da kuka tace "wayyo mamii meya samu yaya"  mamii bata kalletaba ta dauki wayarta har zata kira big daddy taga kamar zata d'aga masa hankali, juyawa tai hanna ta rufa mata baya da sauri ,
  Inda suke ajiye spare key ta duba ta dade sosai sannan ta lalubo key d'in dakinsa ,hannunta na karkarwa ta bud'e akai sa,a kuwa shine da sauri suka kutsa kai cikin d'akin lokacin tuni wani wahalallen bacci ya d'auke haydar, da sauri mamii ta karasa kuwa dashi ta juyasa dakyar ajiyar zuciya ta sauke me karfi ganin baccinsa yake amma kaida gani kasan bana dad'i bane ,cike da tausayi mamii ta zare masa takalmin kafarsa ta gyara masa kwanciya  ac ta kunna masa ganin irin gumun da yake kamar wanda ya fito daga rana sanyaye suka fito daga dakin mamii ta wuce kitchen hanna tad'au littattafan ta ta wuce side d'insu,
  Tana shiga aunty tace "harkin dawo?"  A sanyaye tace "eh aunty "  aunty tai shiru tana kallanta nadan second can tace "hanna meyake damunki"  tai raurau da ido tace "yaya haydar aunty bashida lfy kuma mamiina tana cikin damuwa"  tana gama fad'a ta fara hawaye ,aunty ta danne damuwarta tace "to kuma sai akace kiyi kuka,addu,a zaki masa ya samu sauki"  hanna ta ta6e baki tace "inyiwa mamiina dai dama alhakinmune ya kamasa jiyafa mun kusa 1h muna kamun kunne" 
  Cike da takaici aunty tace "kedai wannan yarinyar bakida hankali wlhy ,saikin fara abu kamar wata nutsatstsiya saiki kare da shirme 6acemin da gani "  tana turo baki ta wuce bedroom d'insu,
  Harara aunty ta watsa mata ta shiga daki ta dakko hijab tana fitowa basma tana dawowa daga makaranta basma tace "aunty ina zaki"  tana tafiya tace "zani in dubo yayanku bashida lfy"  bin bayanta basma tai suka tafi tare,
  A zaune suka tadda mamii tana ganinsu ta dan saki murmushi ta budewa basma hannu sosai takeson yayan yar uwartata musamman hanna da takejinta kamar ita ta haifeta, aunty ta kalli mamii cike da damuwa tace "maamii ya jikin yayan nasu" mamii ta d'anyi murmushin karfin hali dan komawarta d'akin sau biyu ta tadda bai tashi ba tace "da sauki baccima yake,ina ganin ba wata babbar matsala bace gsky"  aunty tace "to ALLAH ya bashi lfy "  sun d'an dade sosai sannan sukai mata sallama suka fice,
  Haydar kuwa sai da yad'auki 3h yana bacci kafin ya farka a kasalance ya zuro kafafunsa daga Kan gadon yanajin kansa na juyawa bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower me sanyi sosai ,tsaye yayi yanajin yadda ruwan yake dukan kansa har yanzu yanajin mararsa na murd'a masa sai dai ba sosai ba wanka yayi a nutse ya fito sanye da farar bathrobe fara ,
   Kai tsaye gaban mudubi ya tsaya ya  warware igiyar rigar wani farin towel yasa ya goge jikinsa tass sannan ya shafa cream d'insa me kamshi ya gyara sajensa had'e da taje sumar kansa turaruka kusan kala 5 ya fesa ya d'akko kananun kaya bakake yasa glass baki ya manna a fuskarsa ya d'au wayarsa miss call din siyama ya gani kusan 15 gajeran tsaki ya saki ya sanyata a aljihu ya fito daga d'akin a hankali yake sakkowa ,
  Mamii da mum din fannah da tashigo dubasa ya tarar suna hira sama sama ,mamii ta kallesa sanda ya karaso sosai taji hankalinta yayi mugun kwanciya mum tace "jiki yayi kyau haydar ALLAH ya kara afuwa"  a saman la66ansa ya amsa bayan ya gaidata tashi mum tai taiwa mamii sallama tana fita mamii ta dawo kusa dashi tace "meyake damunka haydar?"  Lumshe ido yayi ya cije lips d'insa ,baisan me zai ce mata ba duk da yad'an saba jin feeling but amma nayau dabanne dan bai ta6a jin irin saba ,mamii ta shafa kansa taji ba nrlm yake tace "kayi shiru haydar me ya sameka ka dawo gida haka kamar ba,a hayyacinka kake ba"
  Shiru ya sake yi can yace "dan ciwon cikine amma yanzu na daina"  mamii tace "kasha maganine"  yace "eh mamii"  tace "to ALLAH ya sawwake gobe kaje kaga likita"
  Tashi yayi yace "to mamii"  yana gama fad'a ya fice karo sukaci da Farouk da tahowarsa kenan hannu Farouk ya mike masa yace " man ya jikin? Ashe bakaji dadi ba yanzu mum ta fad'amin"  shafa kansa yayi a hankali yace "naji sauki"  tafiya suke suna hira jefi jefi duk da Rabin hirar Farouk ne ke yinta ,a masjid suka had'u da small dad(abban farouk)da abba dukansu sannu suka ringa masa tamkar wani wanda ya kwanta ciwo , haka daya dawo gidama mamii a gaba ta sashi  sai da taga yaci abinci sosai sannan ta rabu dashi,
  Aunty ce tsaye akan hanna fuska d'aure tace "wato hanna bakyajin magana ko? Ba wanda baije duba yayankuba saike sai anyi magana kice kinje ina kula dake duk yau baki fita daga gidannan ba"  hanna ta turo baki tace "aunty nifa na fara masa sannu ALLAH ko kin manta har d'akinsa fa naje kuma ki tambayi mamii"  aunty tai shiru tana kallanta can ta ta6e baki ta juya ta fita,
  Hanna ta gyara kwanciyarta tana dariya kasa kasa tace "mugu alhakinmune ya kamaka"
Ta murguda baki tana hararar d'akin,
  Siyama kuwa ba karamin tashi hankalinta yayi ba kallan wayar take banda hawaye ba abunda take ji take kamar wani abu ya samu haydar d'inta har mum d'inta ta shigo bata saniba saiji tai ta dafata,a sanyaye ta juyo tana ganin mum d'in nata ta fad'a jikinta ta fashe da kukan da take rikewa ,haj binta shafa kanta take cike da damuwa tace "ina kula dake siyama tunda kika dawo bakya cikin nutsuwar ki meyake damunki?" Cikin matsanancin kuka siyama tace "mum banace miki yau zaku had'u da haydar ba?"  Haj binta ta dafe kanta cike da takaicin halin yar tata na san wanda baison ta ta danne takaicinta tace "eh kin fad'amin"  siyama tace "wlhy mum ko magana bamuyi ba ya fara rashin lfy gashi inata kiransa bai d'agaba mum tsorona kar wani abu ya samu haydar"  haj binta tai k'asake tana kallanta yarta cike da tausayi ta rumgumota tace "ya isa kukan ,ba abunda zai sameshi insha ALLAH, siyama ki dage da addu,a ALLAH ya rage miki son wannan haydar din bansame me kika gani kika like masa ba duk irin yadda samari yayan attajirai suke sonki kin shafawa idonki toka kince sai haydar,siyama burina na aurar dake hankalina zaifi kwanciya shekararki 25 yaci ace kin fidda manemi  keba saurayi kika rasaba gasunan har yanzu nema suke ki basu dama amma kinki bansan wane irin so kikewa wannan haydar dinba"
  Siyama ta lafe a jikin mum din nata cikin sanyin murya tace "mum ki tayani da addu,a wlhy ni kaina bansan irin son da nakewa haydar ba kuma mum insha ALLAH  tunda ya amince muka fara had'uwa watakil shima ya fara sona kiyi hkr mum insha ALLAH nan bada jimawaba zan kawo miki haydar a matsayin wanda zan saura"  tagumi haj binta ta zabga tana kallan siyama har takai aya,ajiyar zuciya ta sauke ta mike tace "to yayi kyau ki fito kici abinci"  siyama tabi mum dinta da kallo harta fice kafin ta mike a sanyaye ta shige bathroom ta wanke fuskarta ta fito parloun.

#Vote
#commt
#share
#oumramadan❤️

HannahWhere stories live. Discover now