Hannah part 22

388 56 3
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣2️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

*Assalamualaikum dear fans inaso in d'anyi wani tsokaci game da cmmnt d'in da fans suke ina mai bawa duk Wanda bana mayar masa da reply Koda yaushe hakuri musamman na group dan Allah a ringayin azuri groups din da yawa saika rasa Wanda zaka amsa sannan in kace ko wanne saika bishi daidai da daidai ka amsa Masa wata sabuwan wahalace ga wahalar typing ka gama hannu yana zafi amma insha Allah zanyi kokari duk bayan lokaci ina amsawa ina fata zaku fahimceni ngd*🥰

Tana fita mk ya fizgo hanny da take jifansa da wani murmushi tana kas kas da gum ganin yana shirin magana yasa ta jefa bakinta cikin nasa ta shiga kad'a harshenta a cikin tana Masa salo daya birkitashi, kissing d'insa take tamkar zata cinye masa baki saida sukai kusan 15m sannan ta janye bakinta daga nasa ko wanne Yana sakin numfashi da sauri da sauri,
Tashi tai tana kallan tsakiyar idanunsa da sukai canja kala ta wani juya idanu kamar zasu fad'o tace "nasan abinda kake kokarin fad'a baby,na zauna nayi tunanin meye ribana yanzu innai aure? Shikkenan fa na Zama ko yaushe a kulle banda izinin kaina sai Wanda aka ban ,a yadda nake rayuwata ma bana tunanin wani aure saina gama cin duniyata da tsinke ,dan haka ka ajiye wancan maganar da mukai mu cigaba da rayuwarmu kamar da matukar inkai aure bazaka rabu da daniba"
Tsura mata ido yay yanaso ya tantance gaskiyar abinda take fad'a kamar tasan abinda ke ransa ta dawo kan cinyarsa ta zauna tana shafa kyakykyawan sajensa tace "haba baby kokwantan me kake a kaina? Kamar yadda na fad'a maka hakane a zuciyata ni yanzu ba batun wani aure a tsarina ,kawai muci gaba da rayuwarmu a haka muddin baza sa6a alkawari ba" ajiyar zuciya ya sauke ya kaiwa kumatunta kiss yace "good girl ashe kin gane abinda nake nuna miki,kikai aure yanzu ae kin tauye kanki ne ba wani yanci a rayuwarki sai wahala da bauta lokaci d'aya zaki tsufa ki rasa mamora"  hmmm hanny tace a ranta banda zaginsa ba abunda take fari ta sakar masa tana yauki tace " yawwa baby amin transfer inason zuwa siyan kayan kwalliya"
Wayarsa ya dakko batare da yay magana yay Mata transfer 300k ,
Tanajin alert ta sakar masa kiss ta wuce tana jifansa da wani kallon zakasan koni wace,
Yana zaune gaban senate a katafaren parlournsa su biyune  senate yace "kasan yau alkawarimu ya cika ko? Kun daidaita ko kwa Yaya?"
"Eh daddy mun daidaita harma iyayenta sun amince na turo" senate wani farin ciki ne ya ratsasa zai aurar da only son d'insa cikin jin dadi yace "Masha Allah suwaye iyayenta" jimm yay can yace "babanta kanin Alhaji abdullahi fagge ne" cikin mamaki senate yace "kana nufin Alhaji abdullahi dana sani ko wanne?"  "Eh shi daddy" mk yace yana kas da Kai ,daddy yace "ok tashi kaje ba damuwa nasanshi ma zanje na samesu" mk ya russuna yace"to daddy Allah ya Kara girma" daga haka ya fice daddy yad'au wayarsa yana dialling d'in wata number,
Ta bangarensu big daddy duk binciken da sukai an tabbatar musu da mk mutumin kirkine (kunsan fa yawanci ba komai yake bayyana a bincike ba musamman lamarin aure ,duk yadda kakai ga bincike ka Kuma tsananta addu,a dan wani halin ba bayyana yake ba sai zama yay Zama daga baya azo ana dana sani shiyasa a koda yaushe akeso ka nemi zabin Allah kafin ka yanke hukunci)
Ranar Friday dad din Sameer ya iso Kano shi kad'ai, Sunday senate sukazo neman auran hanna cikin mutunci akai komai aka gama,kudin aure 30k sai set din akwati na nagani inaso guda 6 haj sara tai bajinta ta zuba Kaya na kece raini musamman da taji yarinyar da zai aura Yar masu shine,
A takaice a ranar aka tsaida biki wata 3 masu zuwa, baki sai zuwa ganin Kaya suke friends din mamii dana aunty,mum din fannah tazo itama,yayinda fannah ta shiga tsananin tashin hankali sbd tasan yadda yayanta yake tsananin son hanna,
Tunda mami ta nunawa haydar kayan hanna bai kara kallan idan suke ba daga karshema d'akinsa ya shige ya kulle kofa,
  Kwanciya yay ya dinga juyi gaba d'aya ya rasa me yake damunsa , lokaci d'aya kansa ya fara ciwo a daddafe yay wanka ya kwanta yana juyi dan sam baccinma ya kasa zuwa,
  Koda ya tashi kin sakkowa yay sai bayan magriba , a kofar shiga parlourn sukai kici6is da hanna da sauri ta matsa kasa kasa tace "Ina wuni Yaya"
Wani mugun kallo yake jifanta dashi har wani huci yake fitarwa tsaki ya saki harya wuce ya dawo ya fizgo gyalanta a fusace yace "Zaki 6acemin da gani kosaina karya kafafunki? Wawiyar yarinya kawai ke ko kunya bakijiba kina zumudi zakije kiga kayan aur,,," kasa karasawa yay ya saki kwafa a fusace yace "innaga kafarki a part dinnan saina kusa sumar dake" tura baki tai ta murguda baki tace "nifa Yaya ba ganin Kaya nazo yiba aunty ce ta aikoni" make bakin yay yace "Zaki 6ace daganan kosai nayi abinda zuciyata take kitsamin?" Juyawa tai tana kuka dan bakaramin zafi tajiba saida tai nisa ta juyo ta galla masa harara kasa kasa tace"Kuma Allah ya inasa" sakin baki yay dan yana ganin yadda bakinta yake motsi yasan abinda zatace kwafa ya saki ta sake hararsa tai wucewarta part d'in su,
Sameer kwata kwata bai samu labarin sa ranar Hanna na saida aka kusa sati dadowarsa kenan daga aiki yana zaune yanacin abinci mum d'in sa tace "Sameer ka Kira yan Kano fa kai musu Allah sanya alkhairi"
"Meya faru mommy?" Ya tambayeta yana cigaba da cin abinci ,mommy tace "af na manta ban fad'a makaba ansa ranar kanwarka,yau sati kenan" 
"Ok shiyasa daddy ya tafi Kano kenan? To Allah sanya alkhairi basma?" Ya tambayi mommy girgiza Kai tai tace "aa hanna dai" abincin da yake cine ya kwaresa tari ya shigayi da karfi tuni idanunsa sukai wani jajur lokaci d'aya, magana yake sonyi tarin ya hana momyy duk ta rud'e ruwa ta bashi yasha me sanyi tana masa sannu, baibi takan sannun da take Masa ba murya na rawa yace "wai mommy wace hannar aka sawa Rana?" Wani kallo mommy tai masa tace "wace hannar ka sani banda ta kano"
Wani mummunan fad'uwa gabansa yay Kujera ya dafa sbd wani jiri da yaji yana neman kayar dashi idanunsa gaba daya rufewa suke neman yi cikin tsananin tashin hankali ya kalli mommy yace "Wai da gaske hanna aka bawa wani mommy,anya kinji da kyau kodai basma ne?" Mommy gaba d'aya lamarin Sameer ya fara bata tsoro da mamaki tace "Sameer lafiyarka kuwa " girgiza Kai ya shigayi yace "ba lafiyaba mommy wlhy ba lafiya ba" ball yay da abincin ya wuce bedroom d'insa cikin tsananin bacin rai da tashin hankali da sauri mommy ta bishi tana kwala masa kira,
Yana shiga ya kulle kofar zama yay akan stoll kuka yake na zuciya ga wani radadi da yake sukarsa duniyar gaba d'aya ta juya masa a hankali ya koma kan sofa hannun sa dafe da zuciyarsa ,idanunsa sunyi wani jajur dasu tamkar garwashi yanajin yadda zuciyarsa take bugawa hawayen daya zubo a fuskar sane yasashi jin dan sauki a ransa ,
Tashi yay ya shiga toilet a gaggauce ya shirya ya manna bakin glass a idonsa wayarsa ya d'auka  ya fito momy data rafka tagumi tana ganinsa ta mike tace "son kana lfy?" Muryarsa a shake yace"eh momy zani Kano " zaro ido momy tai tace "da yammannan wai me yake faruwane Sameer?" Hannunta ya rik'o yace " bkm kimin addu,a momy Kano zani " duu hankalin momy ya tashi gashi sai kiran number alhaji take bai d'agaba momy tana kallo ya fice driveyya kaishi airport ya siyi ticket ,
  Karfe 7 jirginsu yay landing napep ya tara ya shiga sunzo daidai shatale tale wata mota data danno da gudu ta daki napep din da suke ciki,
  Kan kace me mutane sun taru anata zabga salati tuni aka d'auki Sameer da baisan inda kansa yake ba da me napep d'in akai emergency dasu,
  Mom tana zauna taji wayarta na ringing dama tunda Sameer ya wuce hankalinta bai kwanta a sanyaye ta d'aga wayar , lokaci d'aya ta saki wayar ta saki wani razanannan salati ta fashe da matsanancin kuka , a rikice Papa ya sakko yace "hajiya lafiya?" Kuka kawai mom take ta kasa cewa komai Papa yace "hajiya kimin magana me yake faruwa" cikin matsanancin kuka mom tace "Sameer" ta sake rushewa da kuka tana salati gaba d'aya papa ya rikice yanaji wayarsa na ringing ya kasa d'agawa sai Kira na biyu yana ganin number Sameer ya d'aga yace "Sameer"
Daga can bangaren aka ce "Alhaji kana magana da police,me wannan wayar sunyi accident suna kwance a asibiti" salati papa ya saki hankalinsa yayi mugun tashi cikin karfin Hali yace " to to wane asibiti kenan?" Kwatance police din yay Masa Yana kashe wayar ya Kira big daddy ya sanar masa tuni Abba da big daddy da small dad suka wuce asibitin,
  Mom kuwa a zaune ta kwana Allah Allah take gari ya waye su yanki ticket su wuce Kano karfin hali shi kansa papa yake,yana rarrashin mom data kwana kuka da salati.

Whattpad a d'aure a ringa voting da following

HannahWhere stories live. Discover now