Hanna part 42

195 18 0
                                    

*HANNA*.......💥

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

   *42*

Kusan karfe 9 na dare hannace kwance tayi matashi da cinyar haydar , banda lumshe Ido ba abinda take dan sosai takejin dadin yadda yake shafa dogon gashinta da yake fidda wani irin kamshi,
  Jin shirun yay yawa yasa haydar leka fuskarkarta, yaja dogon hancinta yace "bacci zaki sweet" ta gyada kai tana sake lumshe Ido , ya danyi murmushi yace "toh  tashi ki karashe fruit dinnan saimu tafi bedroom ko" a shagwabe tace "nifa na koshi yaya " ya had'e rai yace "ni ba yayanki bane Malama,"
  Ta ware manyan idanunta da suke cike da barci tace "Allah kai yayane" ya sake had'e rai baiyi mata magana ba, ganin yadda yay yasa duk taji ba dadi , a hankali tace "yay,,," sai kuma tai shiru can tace "baby" tana fad'a ta rufe fuska , da sauri ya juyo ya d'agata cak a sama yana murmushi yace "me kikace sweet" ta turo baki still idanunta a rufe ta make kafad'a ",, " Say it plsssss sweet" yay maganar cikin wani shauki , a hankali tace "baby"
"Omg " yace yana juyi da ita cike da tsananin farin ciki , bude fuska tai tana dariya sosai , saida ya gaji dan kansa ya sauketa yana murmushi yace "zona k'arasa feeding dinki saimu kwanta koh" ta marairaice fuska tace "Allah da gaske nake na koshi" bai sake cewa komai ba ya kashe kayan kallon da ya dauketa cak da bibbiyu yake taka steps d'in ta wani kafe ajikinsa tana shakar kamshin jikinsa , Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce da ita ya kwantar da ita kan sofa , wasu nighties na couple ya fito dasu farare tass ya feshu da turaruka , tanaji ya zare mata yar guntuwar rigar jikinta yasa mata wanda ya dakko  da sauri ta juya ganin yana cire na jikinsa a ranta tana mamakin wai su dama haka maza suke basuda kunyane , itafa har yanzu inyay wani abun mamaki da kunya takeji inta tuno yaya haydar dintane dako magana saiya gadama yake barintana sakin fuska ,
  Ajiyar zuciya ta sauke Jin yanda ya kwanto a jikinta , ta lumshe Ido tana sauraran yadda zuciyarsa ke bugawa , a haka ya tafi da ita kan gadon ya kwantar da ita ya koma ya kashe kwan dakin ,
  Daran ranar bai mata komai ba danya kula ba karamar gajiya taiba saidai tana nanike a jikinsa sukai bacci me cike da farin ciki da walwala,

  Yau ta kama watansu biyu  da aure , izuwa lokacin tuni Hanna ta gama haddace karatun da  haydar yake mata , ko kusa yanzu ta ajiye  kunyarsa a gefe soyayga suke zubawa kamar gidan Indiyawa , kafin ya fita office ta kammala masa breakfast me rai da lfy , ta tsuke cikin kananun kaya masu azabar kyau, haka da yamma ma kafin ya dawo ta shirya masa kanta cikin kyakykyan shiga me daukar hankali,
  Tuni haydar ya sake ajiye kumatu jikinsa yay bulbul alamar kwanciyar hankali har wani fresh ya kara dan inya shigo gida kwata kwata baison fita sbd yadda hannarsa take kashehi da gayunta me daukar hankali,
  Ta bangaren farouk da sameer ma zamuce Alhamdulillah dan ko wannensu ka kalla zakasan yana cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin , sun rumgumi matansu hannu biyu suna basu kulawa da soyayya yanda ya kamata ,
  Mk kuwa har yanzu zuciyarsa tana kulafucin Hanna , ya riga ya gama tantance lokacin tafiyar haydar office da lokacin dadowowarsa tuni ya shiga shirin yadda zaiga sanyin idaniyarsa wato hanna , ba karamin missing kyakykyawan fuskarta yay ba a wata biyunnan , ji yake kamar shekara biyu biyu yay bai gantaba , duk wani motsi nasa hanny tana hankalce dashi zamansu ba abinda ya sauya maganar arziki kwata kwata bata had'a su dashi , sai in jarabarta ta ciyota ta faki idonsa ta  zuba masa desire table yana gama biyan bukatarsa ta jibgeta wani lokacin ta rama wani lokacin ta bishi da zagi a haka zaman nasu ya kasance ,
  Kusan mintinsa arba,in da parking motarsa can kusa da gidan Hanna, agogonsa ya duba cike da matsanancin kishi yana ayyana mintunan za haydar ya dauka a cikin gidan bai fito ba,
   Wata katuwar ajiyar zuciya ya sauke ganin motar haydar ta fito ya bita da kallo yana sakin murmushi , lokaci daya fuskarsa ta had'e da wani irin kishi da fushi ganin hanna a gaban motar sai kallan haydar take tana zuba shagwaba da alama wata maganar yake fada mata  ,
  Cikin tsananin bacin rai da fushi ya tayar da motarsa yabi bayansu har wani huci yake fitarwa na bacin rai.

Oum Ramadan💥

HannahWhere stories live. Discover now