Hannah part 35

481 42 8
                                    

💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
        3️⃣5️⃣

*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*




Karfe 8 na dare  motarsa ta shigo gidan parking d'inta yay ya fito hannunsa rik'e da leda saida ya tsaya suka gaisa da maigadi sannan ya wuce ta bayan wani corridor yabi da zai sadaka da k'ofar parlourn,
   Kai tsaye mukulli yasa ya bud'e k'ofar parlourn can k'asa yay sallama ya shigo zama yay akan Kujera ya ajiye ledar hannunsa yana sauke ajiyar zuciya,hanna kuwa dama tunda ya fita take bak'i sai gab da yamma suka sarara mata tashinta kenan daga parlourn ta wuce upstair ,tunda taji karar motarsa ta haye sama da sauri dan haka kawai inta tuno abinda ya faru da safe duk sai taji wata muguwar kunyarsa ta kamata, ganin kusan few minutes da shigowarsa bai haura sama ba yasa ta mike kamar me tsoron tafiya ta sakko,
  Kamshintane ya fara sanar dashi zuwanta saida ta kusa zuwa inda yake cikin siririyar muryarta tai sallama a hankali Saida ya lumshe ido ya bud'e su fes a kanta tayi kyau sosai cikin shigar atamfa riga da sket tayi wani d'ass da ita duk daba wata kwalliya taiba tai kyau sosai,
  Bud'e mata hannu yay yana binta da wani kallo ta mak'e kafad'a ta shagwa6e fuska tana turo baki a hankali ta fara takowa saida ta kusa zuwa gab dashi ta zagaye da d'an gudu ta shige kitchen tana kyalkyala dariya,
  Murmushi ya saki kad'an yana binta da kallo harta shige kitchen d'in,mintuna kad'an ta fito hannunta rik'e da plate da ruwa da cup da drink , a gabansa ta ajiye ta 6alle murfin robar ruwan ta tsiyaya masa a cup ta mika masa, kar6a yay ya shanye ya mike mata cup d'in ta ajiye ta mike zata kwashe kayan yasa k'afa ya tad'iyota ta fad'o jikinsa a rikice ta fasa ihu kad'an kana jinsa kasan na shagwa6a ne ,bakinsa yakai daidai kunnenta cikin rad'a yace "haka akeyiwa miji sannu da dawowa" rufe fuska tai tak'i magana ya sake cewa " uhm ina jinki,koda yake ban koya miki wannan lesson d'in ba ko? " Mutsu mutsu ta fara cike da shagwa6a tace"nidai yaya ka daina banaso"  cizon kunnanta yay a hankali ta saki wata k'ara sakamakon wani bakon yanayi daya ziyarci gangar jikinta ya kuma cewa "a bani abinci  baby yunwa nakeji"
  Mikewa take kokarin yi yak'i sakinta ta marairaice fuska tace "toh ka sakeni mana"
"Toh ki d'agani mana" ya kwaikwayi muryarta shima a shagwa6e,batasan sanda ta kyalkyale da dariyaba harda kwanciya a jikinsa cikin dariya tace "ta6 ka ganka kuwa yaya" zaro ido yay kamar wani yaro yace "me kika gani" ta sake fashewa da dariya tace "ta6 ba ruwana nidai baza,aji a bakina ba" ya had'e rai yace "saifa kin fad'amin zan barki ki wuce "  turo baki tai ta juyar da kanta gefe tad'an murguda baki tace" nifa bah komai Yaya" ya sake had'e rai kamar gaske yace "saifa kin fad'amin zaki tashi" marairaice fuska tai tace"toh ka cikani saina fad'a maka" sassauta rik'on da yay mata yay dama tanajin ya motsa hannunsa ta kwace jikinta da sauri ta mik'e tana d'an murmushi har wani gwalo take masa tace "na  rantse na maka wayo" ta6e baki yay baice komai ba itama ta juya kai tsaye dinning wuce ta zuba masa abincin da mami ta aiko musu na dare shinkaface da miyar kaji sai had'in salat dasu cucumber ta zuba masa had'in zo6o dayaji kayan kamshi da abarba a cup kallansa tai tace "ga abincin"
Mikewa yay batare dayace komai ba yana karasowa taja masa Kujera ya zauna hakan datai yay bala,in masa dad'i kamar me ciwon baki yace "thanks"
Kokarin barin wajen take yace "Ina zaki?"
  "Parlour zan koma" ta basa amsa tana d'auke idonta daga kallan da yake mata, badan shine d'in dai data saniba da sai tace me kamar sane sbd tasan a gida kallo bai damesaba sai kazo wajensa ka gama magana bai d'aga kai ya kalleka ba idanunsa nakan waya,amma yanzu motsi kad'an ya zuba mata idanunsa masu dafi dan duk yana mata irin wannan kallan saita ringajin wani irin abu yana ta6a mata zuciya da gangar jiki,
  "Daga yau indai ina gida tare zamu ringa cin abinci , lesson 2 indai Ina gida koda yaushe ya zama kina kusa dani banaso ki tashi indai ba wani muhimmin abu ba" taji ya katse mata tunanin da take,shiru tai tana jinjina rashin ta ido irin na maza kallan da yay mata ne yasa ta ja Kujerar kusa dashi ta zauna tana turo baki, spoon yasa mata a gabanta yad'au nasa yay Bismillah ya fara ci,
  Har yay loma 3 batai d'ayaba sai juya spoon d'in take,yana kallanta ta k'asan ido abincinsa ya cigaba da ci har saida yay rabi juice d'in data zuba masa ya d'auka yasha har wani lumshe ido yake sbd dad'insa tissue yasa ya goge bakinsa ya juyo inda take dakyau ya kar6i spoon d'in hannunta a hankali ya d'ebo shinkafar yakai bakinta girgiza kai tai tace "banajin yunwa da yamma naci abinci"
  "Open" ya sake fad'a mata a tak'aice kamar zatai kuka ta bud'e bakin ya fara bata bata ci da yawaba ta marairaice fuska tace ta koshi bai takura mata ba ya mik'e yace "je ki had'amin ruwan wanka"  mikewa tai tace "toh bari na kwashe kayan"
  Bata rija cewarsaba ta shiga kwashe kayan shi kuma ya wuce sama, a bedroom d'insa ta taddashi ya cire kaya dagashi sai boxers da sauri ta kauda kanta daga inda yake gabanta na fad'uwa ta wuce toilet d'in da sauri ta had'a masa ruwan wankan ta zuba turaran wanka a ciki ta fito,
  Karo suka kusayi taja baya da sauri murya na rawa tace "sorry bangani ba"  "ki fitomin da kayan da zansa" yace mata yana shigewa toilet d'in yana kallan yadda jikinta yake rawa so yake ta saki jiki dashi su shimfid'a kyakykyawar rayuwa shi mutum ne me son kulawa bayason wani boye boye ko kunya tsakaninsa da matarsa yanaso ya janyota a jikinsa ta daina d'ari d'ari dashi , ajiyar zuciya ta sauke bayan ya kulle k'ofar ta dafe kirjinta da yake dokawa  da karfi jiki a sanyaye ta bud'e wardrobe d'in ta kai minti 3 tana tunanin kayan da zata d'akko masa daga karshe ta za6o masa wasu riga da wando na shan iska ta feshesu da turare ta ajiye masa akan gado ta fice,
  Kayan da sukaci abinci ta fara wankewa ta gogesu tass ta ajiye a ma,adanarsu ledar daya shigo da ita ta bud'e gasashshiyar kazace da fruit a ciki ta cire kazar tasa a fridge ta wanke fruit d'in ta dakko wani bowl me murfi garai garai ta yanyankasu kananu ta fasa madarar ruwa pink ta juye akai takai had'in fruit d'in fridge ta rufe tana fitowa shi kuma Yana sakkowa hannunsa rik'e da loptop  akan kujera ya zauna ya d'ora loptop d'in akan center table tana tsaye tana kallansa harya kunna ta bayansa ta biyo ta zauna tana satan kallansa ta gefen ido,
  Ba wata hira sukeba illa aiki da yakeyi a loptop d'in,kusan 9:30 ta mik'e ta shige kitchen ta dakko bowl d'in datai had'in fruit ta janyo karamin center table d'in d'akin ta dora akai ta bud'e tasa spoon a ciki kallansa tai tace "Yaya ya fruit d'in"
  Bai kalletaba yace "ohk" tuni ta farasha saida tasha da d'an yawa shima ya fara sha rufe bowl d'in tai takai kitchen kai tsaye ta wuce upstairs tana zuwa bedroom d'inta ta wuce wanka tai tasa wasu sleeping dress taiwa jikinta 6arin turare ta kwanta dan wani irin bacci takeji,
   Sai kusan karfe 11 ya gama aikin da yake ya kashe duk wasu kayan wuta na parlourn ya wuce sama,
   Karfe 9 na safe siyama tana kwance me aikinsu ta shigo ta tsugunna a ladabce tace "ranki ya dad'e kinada bakuwa a parlour" cike da mamaki siyama tace "bakuwa Kuma? Jeki ce mata wacece" mikewa tai ta fita bata jimaba ta dawo tace "Wai tace kawarkice maganace me muhimminci take tafe da ita" mikewa tai kanta ba dan kwali ta fice tunda ta shigo parlourn ta d'aure fuska tanabin leemat da wani mugun kallo, cikin tsawa tace "ke uban me ya kawoki gidannan?" Murmushi ta sakar mata tana shanye ragowar juice d'in hannunta tace "haba ke kuwa ko sannu da zuwa babu sai tmby?"
A fusace tace"dake da sannun kunci abu takazan ubanku,minti 2 na baki ki fice daga gidannan idan har ba ubanki bane ya siya ba" tuntsirewa tai da dariya duk da ranta ya 6aci ta mike tace"meye na tada jijiyoyin wuya Kuma, Wanda muke rigima a kansa ya riga ya kusa kubce mana zuwa nai mu had'e kai mu nemi mafita amma naga alamar bazaki bani had'in kaiba"  katse ta tai a tsawace tace "in had'e kai da shashashan mace irinki ballaga Yar iska yar tasha ca akai miki bansan abinda nake ba to maza maza ki fice kafin nasa security su fitarmin dake duk kin cika mana parlour da wari" zuwa lokacin tuni leemat tazo iya wuya huci kawai take tana cije lips d'in ta a fusace tace"eh ba shakka zaki fad'amin duk abinda kikaga dama gidanku nazo amma zakizo ki sameni har inda nake  anan zan nuna miki ni tantiriyar yar tashace " handbag d'in ta ta d'auka harta fara tafiya ta juyo tana wani murmushin mugunta tace "duk wannan haukan da kike akan haydar ina tabbatar miki bazaki ta6a samun saba ,haydar yanacan ya angwance da zankad'ed'iyar amaryarsa yau kwana 2 kenan,na zata ke me hankali ce mu had'a kai mu cire kishi dan mu cimma burinmu bansan ked'in mara tunani bace na barki lfy amma muddin ina raye keda haydar sai kallo ,ni dama ba bukata na aureshi ba so bazan damu da wata matarsaba abinda nasani duk runtsi saina biya bukatata akansa"
  Wani irin duhu siyama ta fara gani da k'arfi ta ta finciko leemat dake kokarin ficewa a rikice tace "me? Bangane ba wane haydar d'in ne yay aure" dogon tsaki ta saki ta fizge jikinta tana watsa mata wulakantaccen kallo tace "sai kuma kiyi haydar d'in da kika lik'ewa dai ya auri wacce yakeso sai Kuma abi wani sarkin " daga haka ta wuce da sauri ,wata dariya me had'e da kuka siyama ta fashe da ita kamar muhaukaciya ta shiga cewa "no badai haydar dinaba haydar bazai ta6a auran wata inba niba inaaaaa" ta fad'a cikin ihu duhu ta fara gani a hankali ta sulale ta zube a wajen numfashinta ya d'auke cak.

*Afuwan Amin uzuri ban samu reply d'in da akaimin na Groups ba inata kokarin inga na muku typing ne ngd sosai da addu,o,inku inajin dad'in kulawar da kuke nunamin ku sani oum Ramadan tana musu son so fisabilillah.*

HannahWhere stories live. Discover now