Hanna 46

186 15 0
                                    

*HANNA*.......💥

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

   *46*

Dariya Dr fateema take ganin yadda haydar ya rude lokaci d'aya, bakinsa kwata kwata ya kasa rufuwa sai kallan hanna yake data juya baya cikin wani irin kaunarta da soyayyarta da take sake shiga lungo da sako na jikinsa ,
   Drugs Dr fateema ta rubuta musu ta kuma basu shawarwari yadda zasu kula da babynsa, suna fitowa kiran mami na shigowa ,a compound d'in asibitin suka tarar da take ta umarci haydar daya shiga motarsa su had'u a gida , saida ya tsaya yasai mata duk drugs d'in sannan suka wuce gida ,
  Kusan mintinsu goma da zuwa mami ta k'araso ,  lokacin ya sake had'o mata tea me kauri sai lallabata yake tasha , dakyar tasha ya bata drugs d'in kamar zatai kuka ta karba tasha taba 6ata fuska , kallanta gay cike da tausayi da kaunarta yace "menene sweet" a hankali tace "zuciyata tashi take" cikin damuwa yace "sannu baby , zai daina kinji Allah yay miki albarka " yace yana sake kwantar da ita kan kirjinta yana shafa mata baya ,a haka mami ta taddasu ta kauda kanta tana murmushi ta zauna kan kujera tace "sannu daughter " tashi hanna tai a kunyace ta koma jikin mami tace "mamina Ina kwana " tana shafa kanta a hankali tace "lfy lau daughter ya jikin?"
"Da sauki mami" mami tace "to Allah ya sawwake daughter," mamin tace tana sake nazarin hanna ganin yadda ta kara haske kirjinta ya cicciko ga kuma wasu kumatu data kara ajiyewa duk da dama can hanna ba irin siraran matannan bane tanada jikinta daidai misali, haydar kallansu kawai yake yana sakin murmushi shi kad'ai kwata kwata bakinsa ya kasa rufuwa, kallansa mami tai tace " me Dr tace ?" Sosa keya yay cike da kunya ya kasa magana , harara mami ta sakar masa tace "to yau kuma surukarka na zama Ali? "  dariya yay yana shafa gashin kansa , mami ta tabe baki ta bude ledar drugs d'in ta dakko takardun ciki ta warware dayar taga magungunane ta sake warware dayar da sauri ta d'ago tana kallan haydar bakinta ya kasa rufuwa , mikewa yay da sauri ya wuce upstairs dan wani irin kunyar mami yakeji ,
   Mami har hawayen dadi saida ta zubar tsabar farin cikin da take ciki, yaudai hanna taga wani kalar gata wajen mami ,duk wasu kayan kwadayi saida ta tabbatar tayi matasu kafin ta tafi , zuwa lokacin tuni ta warware sai rashin karfin jiki ,
   Mus,ab ne yazo kusan awarsu daya suna hira yana tsokanar parrot saidai yau ba bakin maida martani sai murmushi, tare suka tafi da mami bayan ta sake jawa haydar kunne ya kula da hanna sosai ,
  Da yamma saigasu farouk da basma ,  fanna kuwa sun koma Lagos itada sameer da yake dan haka sai waya sukai mata ,fanna ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a Kano sbd wayar da sukai da hanna da basma har hawaye saida tai , dakyar sameer ya lallasheta da alkawarin ran Friday zasuzo kano sannan ta kwantar da hankalinta,
   Kulewa sukai a uwar daka sukasha hirarsu da yar uwarta, sosai hanna taji dadin yadda basma ta koma kana kallanta zakasan tana cikin Jin dadi da kwanciyar hankali,
Har tsokanar farouk tai tace "ya farouk me kakeba ya basma tai kumatu haka  ta zama katuwa" hararar wasa yay mata yace " kece katuwa wlhy, nan gaba ma inaga sai an bude duka kofofin gidannan da alama sai sun miki kad'an nan gaba " had'e rai tai ta kalli halli haydar tace  "Baby kaji abinda ya farouk yake cemin ko" sbd dariya har kwanciya farouk yake kan kujera basma ko rufe fuska tai tana dariya kasa kasa dan  har  yanzu tana shakkar  haydar , "baby kaga dariya sukemin ko" Hanna ta sake fad'i kamar zatai kuka  , filo haydar ya jefawa farouk yace "zakabar gidannan yanzu tunda takurawa matata zakuyi wlhy" yana dariya yace "kaifa Dan iskane wlhy daga zuwa abin arziki , dubiyafa mukazo gidan baby" yana fada ya sake fashewa da dariya, sai sannan Hanna ta gano dalilin dariyarsa , sai yanzu itama taji kunya da gudu ta tashi ta shige bedroom tana dariya itama,
   Mk ne tsaye kan hanny , karan farko daya  fara shigowa bedroom d'in ta tun bayan da akai musu aure, kallanta yake yadda take bacci gaba d'aya tayi d'aid'ai da cinyoyinta iskar ac na kadata, a hankali yaji yanayinsa na sauyawa yaji yana bukatar kasancewa da ita  , dakewa yay sanin abinda ya kawoshi, takardar daurin auransace a hannunsa yana juyawa , kusan wata d'aya da rabi  ya hadu  da wata yarinya Jidda , sosai hankalinsa ya kwanta da ita  ya kuma gamsu da tarbiyyarta da kamun kanta , baiyi kasa a gwiwa ba ya nemi address dinta suka fahimci juna ,  saidai ga Jidda abun ba haka bane dan jiddan itama rikakkiyar yar  duniyace , kallan farko da taiwa mk ta gano dan  hannu ne , takune da ita na bala,I ko iyayanta basusan tanabin mazaba , zaka rantse da Allah wata salihar kirkice Jidda , tuni ta amince da mk dan  itama ta gaji da walagigi akan titi mahaifinta dan  kasuwane sosai a kano ba Wanda bai sanshi ba , hakan yasa haj Sara jin dadin auran koba komai zai auro mata yar babban gida  , shiri tai sosai wannan karan ma da kanta taje  Dubai had'o kayan lefe , mk kwata kwata bai sanar da hanny sai yanzu da biki ya rake saura 1week a d'aura aure.

Oum Ramadan

HannahWhere stories live. Discover now