Hannah part 27

403 39 6
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣7️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Farar Kujera Abba yaja ya zauna a kofar parlourn sa  yana kallan Hanny yace "ina jinki"
  Hawaye hanny ta fara tana matsar kwalla daga karshe ta fashe da kuka shidai Abba kallanta kawai yake Saida tai kuka sosai cikin sheshsheka tace "kafin na farawa cewa komai abba zanso in maka wata tambaya shin kunsan hakikanin halin Wanda zaku bawa yarku? Ina nufin mustapha kabeer" Abba ya d'aure fuska yana kallanta ta cigaba da cewa "kamar yadda na fad'a maka mustapha ba mutumin kirki bane,fuska biyuce dashi mafi girman kuskuran da zakuyi shine ku aurawa mutum irin mustapha yarku wlhy kunjefa kanku da yarku a bala,i Kun sata a gidan da zata dawwama cikin bakin ciki da danasanin rayuwa, mk mayaudarine macuci azzalumi fasiki mazinac,,," katseta Abba yay cikin tsawa yace "ke yarinya banason zancan banza da wofi anan wajen nai miki kama da sa,anki da zakizomin da wannan banzan zancen?" Hanny tabe baki tai daga tsugunnen da take ta d'ago fuskarta da duk hawaye ya 6ata tace "wlhy tallahi abba duk abinda nake fad'a maka gsky nake fad'a bazan taba bari mk ya cuci wata yarinyar kamar yadda yadda cuceni ya wulakantamin rayuwa ba ka yadda dani abba mk ba irin mutumin da zaku bawa yarku bane" ta fashe da kuka ta fiddo wayarta daga jaka ta kamo vedion da zeey ta daukesu itada mk ta kunna ta mikawa abba tace "ka kalli wannan vedion nasan shi kad'ai ma zai isa yasa ku gane bala,in da zaku jefa yarku" ba musu abba ya kar6i wayar yana kallo tun daga farko, salati kawai abba yake cikin tsananin tashin hankali da mamaki Hanny tana kallan reaction d'in abba taji kamar ta daka tsalle kana kallan fuskarsa zaka hango zallar 6acin rai,a haka yacigaba da kallo zufa tana keto masa,
  Wayarsa ya d'auka ya tura vedion bai kalletaba ya Mika Mata wayar cikin sassarfa ya nufi bangaren big daddy,
  Wani irin murmushi hanny ta saki tana juya ido wayar ta maida cikin jaka tazo inda tabar zeey ta kalleta tace "kawata na gama da nan gidan Kuma aiki ya kammala" jinjina Kai zeey tai tace"to yanzu Kuma sai Ina?"
  "Gidan senate" ta bata amsa Kai tsaye, zeey ta zaro ido tace "kawata kina ganin ba wata matsala ?" Had'e rai tai tace"ki daina kiramin matsala gsky banso ," numfashi zeey ta sauke tace "toh kina ganin securityn gidan zasu barmu mu shiga?kinsan fa can ba irin Nan bane" 
"Kedai kawai ki zuba ido zeey sau nawa Ina shiga gidan,abinda security d'in wasu duk sun sanni muje da Allah karbu 6ata lokaci" cikin nishad'i Hanny da kawarta suka fice daga gidan,
  Abba kuwa kai tsaye parlourn big daddy ya nufa acan ya sameshi dagashi sai haydar da small dad ,hankali tashe ya shigo zama yay ya kallesu yace "to an yankabta tashi ,wannan auran bazai ta6a yuwuwaba" dukansu kallansa suke cike da mamaki small dad ne yay karfin halin magana yace "wane aurene bazai yuwuba Yusuf" wayarsa abba ya ciro ya kamo vedion ya kunna musu bayan ya kure volume,salati  suka saki cikin tsananin kaduwar abunda sukeji haydar yana zaune sai sakin murmushi yake shi kad'ai yana kad'a Kai,
  Shiru dukansu sukai cike da jimami big daddy ne yay karfin halin magana yace" innalillahi wa inna ilaihirraji,un Alhamdulillah hakika mun gode Allah day nuna mana gsky tun kafin me afkuwa ta afku, amma wannan yaro yazo mana da cuta da yaudara ya Kuma ha,incemu ban ta6a tunanin zai aikata wadannan mugayen halayenba da wanine ya fad'amin ba lallai bane na yarda duba da yadda yake da tsantsar ladabi da girmama mutane" Abba yace "ni kaina da a wani waje naji ba lallai na yaddaba,ina ganin kawai gwara a mayarwa da mahaifinsa kudinsu da kayan da suka kawo zaifi sauki" Small dad yace "ae ayau basai gobeba insha Allah zamu mayar musu da tsiyarsu yaro ko had'a ido baya iyayi da mutane ashe duk munafuncine" mikewa big daddy yay ya kalli haydar da yakejin ba Wanda ya kaishi jin dadi kaf duniyar yace " dama kayan sunanan bangarena ka fita ka kirawo driver ya tayaka kwashewa a sasu a mota "  mikewa yay yace "toh daddy"  daga haka ya fice yana sakin wani lallausan murmushin da saika dad'e bakaga irin saba, waya small dad ya dakko ya Kira papa ya sanar dashi halin da ake ciki,
   Ana Kiran sallar magriba Hanny ta k'arasa gidan senate bata wani sha wahalar tambayoyi ba da yake sund,an santa takan biyo mk wataran zeey ce dai duk yadda taso ta shiga suka hanata sai a bakin get ta zauna jiran hanny,
  Saida ta tambayi security suka tabbatar mata da senate yana masallaci hakan ba karamin dad'i ya mata ba coz tasan ganin Senate lokaci d'aya saitasha muguwar wahala kuma bata isa ta tunkari hajiya sara da wannan zancan ba dan tasha kamasu tare itada mk,
  Tana zaune har aka idar kusan zaman awa 1 tai sannan senate ya shigo Kai tsaye dama side d'insa ya nufa da gudu ta rifa masa baya tana kiransa cikin raunin murya ,tsayawa yay da dakatar da security d'insa da suke kokarin hanata zuwa wajenta gabansa ta zube kamar gaske tana maida numfashi kamar gaske tace "Abba wajenka nazo Abba dan Allah ka tsaya ka saurareni" senate ya kalli securitynsa yace "ku koma " shiga parlourn yay ta biyosa harta fara hawaye, a kasa ta zube tana gaida senate kamar zata kwanta fuska ba walwala ya amsa yace "wane taimako kike bukata" ta fashe da matsanancin kuka ta sunkuyar dakai cikin rawar murya tace "hakika Kai ubane nagari Kuma shugaba me adalci wa al,umarsa bayan Allah daya hallicemu nasan ba wanda zai iya kwatarmin yancina saikai sai kotu, matsayinka na babban mutum me daraja a kasarnan naga baici ace na maka jininka kotuba naga ya dace na fara zuwa na sanar dakai kafin nakai inda za,a bimin hakkina" jikin senate yay sanyi ganin yadda take kuka yace "ki fad'amin wane zalunci akai miki ni Kuma na Miki alkawarin bi miki hakkinki ko inane" hanny ta kad'a kai tana murmushin nasara ta sake raunana murya tace "Koda kuwa jininkane?" Gyad'a kai yay yace "jinina baifi karfin hukunci yarinya duk Wanda ya taka doka toh doka zatai aiki a kansa"
Ta kalleshi ta gefen ido tace "ina kunyar sanar dakai abinda danka mustapha yay min abba Kai mutum ne me dattako kowa ya shaidi halinka saidai kash albasa batai halin ruwaba" ta sake rushewa da sabon kuka ,gaban senate yad'an fad'i a hanzarce yace "me mk yay Miki yarinya" cikin sheshsheka tace" mk ya cuceni ya yaudareni abba mk yamin alkawarin aure ya gur6atani da mayaudaran kalamansa har lokacin dazai turo iyayen sa ya fad'amin ,daga karshe yace zai kaini na gaisa iyayensa kafin suzo ashe yaudarata zaiyi ya kaini wani gida ya kawomin lemo yace nasha yanzu zakuzo, tunda nasha ban sake sanin inda nake ba sai farkawa nai na ganni cikin wani yanayi " wata razananniyar tsawa senate ya dakawa hanny danshi mutumne me zafi a fusace yace "idan Kika kuskura kikamin karya kika 6atawa zuri,ata suna zan dau mummunan mataki a kanki na rantse da girman Allah" bakaramin tsorata hanny taiba danji tai kamar ta zura da gudu,jiki na rawa ta fiddo wayarta ta kunna vedion bayan ta kure volume rufe ido senate yay yana karkada k'afa jin maganar da mk yake yasa ya budeso da sauri ya kar6i yawar da tunda ta kunna ta miko Masa yaki kar6a runtse ido senate yay cikin tsananin tashin hankali jirine yaji yana neman kayar dashi daga zaune a hankali ya shiga furta innalillahi a ransa ya runtse ido da karfi yana addu,ar inama mafarki yake ace Wai dansane da kansa yake ikirarin adadin matan dayake kwanciya dasu, zuface ta tashin hankali ta shiga tsatstsafo masa zuciyarsa har wani  harbawa ta fat taf.

HannahWhere stories live. Discover now