Hannah part 26

407 42 6
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣6️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Ko 30mt mk baiyiba ya k'araso tun daga nesa yake kallan hanny da mamaki ganin yadda take hawaye a haka ya karaso mikewa hanny tai tana kallansa ta fashe da kuka tace "yanzu mustapha da gaske aure zakai ka barni?" Ya had'e rai bayan ya zauna ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace "na zata mun riga mun gama wannan maganar dake ko?" Ta sake fashewa da matsanancin kuka tace "why mustapha meyasa ka yaudareni da cewar zaka aureni ka rabani da budurcina ka maidani karuwa ,meyasa ka shigo rayuwata ka tarwatsamin farin cikina ?" Wani murmushi yake saki yana kallan hanny can ya fashe da dariya yace "gsky kinada abun dariya hanny meye aciki danna kar6i budurcinki a waje? Sha,awarki nake Kuma nake biyan bukatar kaina nake biya Miki taki,look hanny banason hauka nasha fad'a Miki ko nayi aure bazan rabu da keba zamu cigaba da mu,amalarmu kamar da" tsugunnawa hanny tai ta rike kamar mk tana wani kuka kamar ranta zai fita tace "wlhy mustapha ina tsananin sonka karkamin haka karka azabtarmin da zuciya mustapha ka yaudareni da kalamanka na karya kace zaka aureni ka kawoni nan ka rabani da mutuncina yanzu kace ka fasa aurena wata zaka aura? Hanny cefa da kake bala,in so kasha furtamin ni kad'ai zaka iya aura ,na yarda dakai na baka amanata amma yanzu ka gujeni lokaci d'aya? Me zan cewa mijin dazan aura idan ya sameni disvirgin ? Yakamata kamin adalci mustapha ka rike amanar dana baka" ta k'arashe cikin wata raunanniyar muryan da dole ta baka tausayi ,
  Lokaci d'aya ransa yay mummunan 6aci ya fizge kafafunsa har Saida hanny ta wuntsila mikewa yay ya fizgota yana huci yace "ke baki isa ki d'agamin hankali ba ,wacece Kee cikin yammatan da nake mu,amala dasu? Yammata nawa nai disvirgin saike ce kadai zaki bani matsala, kinsan yammata nawa nake  kwanciya dasu basu ta6a d'agamin hankali ba saike ,inada ire irenki sunfi a kirga sbd haka inna rabu dake kece da asara ada nayi niyyar cigaba da zamanmu tare amma tunda haka kika zaba Koda wasa kika nuna kin taba sanina saikinyi dana sanin sanina saina wulakantaki kin zama abar gudu" jefar da ita yay zai wuce ta rarrafa ta Kuma riko kafafunsa tana wani irin kuka tace "karka tafi ka barni mk karka barni a wannan halin ka tuna fa har cikinka nayi na zubar duk dan farin cikinka ni meyasa bakason nawa farin cikin?" Ball yay da ita yana niyyar ficewa yaji tace "Zanje na sanar da sirikanka irin mugun halinka na yaudara mustapha wlhy saina fad'a musu bara gurbin da zasu aurawa yarsu"  cak ya tsaya ya juyo ya tako har inda take yana wani murmushi yace " idan Zaki kwana rantsuwa bame yadda dake hanny sbd kaf d'insu kallan mutumin kirki sukemin kuma kinsan waye mahaifina da irin matsayinsa karma ki wahalar da Kanki ki 6atawa kanki lokaci dan aurena da hanna ba fashi"  yana gama fad'a ya fice a fusace,
Yana fita zeey ta fito tasa stop a vedion da take ta kamo hanny da take kwance akan tiles  lokaci d'aya hanny ta fashe da dariya harda kwantawa zeey na tayata Saida tai dariya me isarta kana ta kalli zeey tace "kawata ya kikaga shirin nawa?" Zeey ta jinjina kai tace "gsky kawata duk yadda na d'auke ki kin wuce nan, drama kamar wata Yar film?"
Wata dariya ta saki cikin jin dadin komai yana tafiyar mata daidai tace "toke ya Kika gani kawata,akwai mahaifin da zaiga  wannan ya yadda ya aurawa yarsa shi? " Ta mike tana wani murmushi tace "inamai tabbatar miki jibi jibinnan za,a fasa wannan bikin wannan alkawarinane ki rubuta ki ajiye wannan auran kaina zai dawo" zeey tace "toh yanzu idan kikasa aka fasa bikin ta Yaya zai dawo kanki?" Mikewa tai bayan tad'au handbag dinta ta dafa kafad'ar zeey tace "kawata kawai kisa ido kiyi kallo,Kuma ki fara Shirin bikin babbar kawarki danni tuni shirye shirye sunyi nisa a wajena" jijjiga kai zeey tai tace "Allah yasa" ficewa sukai daga gidan zuciyar hanny kamar takadda,
  Karfe 7 na dare mk yay parking kofar gidansu hanna wayarsa ya dakko ya kirata yace ta fito yana waje har yanzu ransa a mugun bace yake yana kuma mamakin Hanny lallai saiya d'au babban mataki akanta kafin ta zame masa karfen k'afa,
  A sace ta fito batare da mami ta saniba,tafiya take kamar mara gsky Saida ta tura get ta fita sannan ta saki ajiyar zuciya,can nesa kad'an ta hango motar mk cikin nutsuwa take tafiya harta karasa knocking taiwa glass d'in motar, murfin motar ya bud'e mata jim tai nadan second can take shiga tabar murfin motar a bud'e,
  Wata ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamshin jikinta na hawa masa kai matsowa yay gab da ita kamar zai shige jikinta ya rufe murfin motar gabantabe taji ya fad'i sbd haduwarsu waje guda,
  Juyowa yay yana kallanta sosai yace "Amarya ya shirye shirye?" Tana wasa da zoben hannunta bata d'ago ba tace "Alhamdulillah" ya sake matsowa daf da ita cikin rad'a yace "badai har kin fara kunyataba" dan matsawa ta sakeyi kad'an tanajin bugun zuciyarta na karuwa ,gaba d'aya kamshin da take yana mugun tayar masa da hankali wayarsa ya dakko ya fizgota jikinsa ya rumgumeta tsam ya d'auke su hoto, da karfi ta fizge jikinta kamar zatai kuka tace "sir ba kyaufa" murmushi ya sakar mata yana kallan hoton yace "sorry partner na kasa jurewa idan ina ganinki kusa dani bana iya control d'in kaina" had'e rai tai taki magana ya nuna mata hoton da yay musu saika rantse ta zama matarsa sbd kusancin da suka samu gashi fuskarsu tana manne data juna tana kokarin karbar wayar ta goge ya d'auke wayar yasa a aljihu yana kallanta kasa kasa bud'e motar tai ta fice a fusace ya rik'o hannunta ya marairaice fuska kamar zai kuka yace "baby nace kiyi hkr kinsan ba halina bane koh? Ni kaina ba,asan raina na rumgumeki ba ke d'in ce ta daban beauty ina jinki fiye da yadda baki tsammani kullum sainaga kamar kara canzamin ke ake shiyasa nake susucewa idan kina waje" numfashi ta sauke tad'an saki fuska kad'an ganin yadda ya marairaice mata tana hango nadama a idanunsa tace "toh shikkenan zan shiga ba,asan na fito ba"
"Ok karki kashe wayarki zan kiraki anjima" batace komai ba ta d'aga kai ta wuce ya bita da kallo yanaji kamar yaje ya rumgumeta a jikinsa su dawwama a haka,
  Tunda ta shiga Mami ta had'e rai tace "daga ina kike?" Inda inda ta fara tana sosa keya tace "am ,,,,dama mami sako naje na kar6a" hararta mami tai tace "Amma nace Kun daina fita ko? Ga Yan uwanki can su ba inda suke zuwa saike ce Zaki dau k'afa ki fice ba tare da kin sanar dani ba" shiru tai ta kasa magana Mami ta miko Mata wani abu a cup tace "maza kar6i ki shanye" kamar zatai kuka ta kar6a tana dandanawa taji da dadi ta shanye duka cup d'in ta mikawa mami ta wuce dakin da ake musu gyaran jiki,
  Tsaff Hanny ta shirya cikin dogon hijab d'inta daga ita sai wayar hannunta da yar post zeey ma cikin hijab take Kai kace wasu mutanan kwaraine,
  Karfe 6 na yamma suka dira gidansu hanna daya fara cika da yan biki duk inda ka wulla ido a  harabar compound d'in mutanene kowa na sabgar gabansa,
  Bangaren mami da yake nanne matattarar amaren sai shewa ke tashi su rauda da Zahra da sauran  friends d'in su na skull dana islamiyya duk sunzo kasancewar gobe za,a fara even,
  Rike kugu Hanny tai tacewa zeey "nifa banazo bane in shiga cikin gida wajen mata,mahaifinta nakeso nagani ko wani daga cikin iyayen gidan dan abinciken danayi naga su 4ne iyaye maza a gidan" zeey tace "ni kuma nazata matan mutum 1 ne danaga gida 4 a jere" ta girgiza kai  tana tunanin mafita can ta hango farouk yana tafiya da sauri ta k'arasa wajensa  cikin ladabi ta gaisheehi ba yabo ba fallasa ya amsa zai wuce yaji tace"Dan Allah inasonyin magana da daddy" kallanta yay ya d'auke kai yace "meya faru kikeson ganinsa"  ta marairaice fuska tace "wata muhimmiyar magana nake tafe da ita dan Allah" 
"Zaki iya fad'amin koma menene na sanar dashi" 
Rantane taji ya fara 6aci tadai d'aure tace"dan Allah ka hadani dashi maganar me muhimminci ce" hango abba tai ya fito daga mota bata sake kallan farouk ba ta wuce da sauri ta zube a gaban abba tana gaidashi ,
"Daddy akwai wata muhimmiyar magana da nake tafe da ita" shiru abba yay yace "toh ina jinki yarinya" juyawa tai ta kalli inda suke tace "daddy inba damuwa mu samu wani waje daba mutane ina neman wannan alfarmar" shiru yay can yace "ok biyoni"

HannahWhere stories live. Discover now