Hannah part 5

452 32 1
                                    

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣5️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@oumramadan1

Mamii tana kwance kan bed d'inta, ta lullu6e jikinta da duvet kanta ne kawai a waje ,big daddy yana tsaye a kanta cike da damuwa yace "ya jikin hajiya"  mamii ta yunkura ta mik'e a hankali tace "da sauki alhaji,najima sauki kawai rashin kwarin jikine"
  Jijjiga kai big daddy yayi sai lokacin hankalinsa ya kwanta yace "to babu abinda kike bukata madam"  tace "eh"  yace to "zan wuce office zan kiraki anjima inji yanayin jikin naki"  "to" kawai tace daidai lokacin hanna ta shigo d'auke da warmers a hannunta, d'an murmushi ta saki tace "ina kwana daddy"
  "Lfy lau hannatu ya karatu"  yace mata ,6ata fuska tai kamar zatai kuka tace "daddyy" ficewa yayi yana murmushi ta k'arasa kuka da mamii fuska d'auke da damuwa ta yaye duvet d'in jikinta tace "ga farfesu na miki mami "  bata jira cewartaba ta d'akko plate ta zuba mata tasa cokali daidai lokacin haydar ya shigo sanye da suite as usual hannunsa rike da jakar laptop ,
  Gadon da mamii take ya nufa cike da damuwa ya durkusa yace "ya jikin naki mamii"  murmushi mamii tai tace "da sauki haydar zaka wuce "
Zama yayi yana kallan hanna tana gaidashi tana turo baki ta6e baki yayi ya amsa ciki ciki,hanna ta kalli mami ta marairaice tace "mamii kici karya huce"  ta d'ebo a cokali a hankali takeba mamii har sai da taga taci da d'an yawa sannan ta 6allo magungunanta ta bata haydar yana zaune yana kallansu ta k'asan ido, tissue tasa ta goge mata baki ta jinginar mata da pillow ta yanda zataji dad'in zama ta kwashi plate d'in ta sauka downstairs,sai sannan haydar ya d'ago ya kalli mamii yace "zan wuce office mamii ba abunda kike bukata"  murmushi tai tace "eh bkm ALLAH yayimaka albarka ya tsareka"  tashi yayi a hankali yace "ameen mamiina"  daga haka ya fice a stairs suka had'u da hanna ,hararsa tai ta gefen ido k'asa k'asa tace "mugu kawai"  ta murgud'a baki ta wuce bedroom d'in mamii,
  Jin alamar tana bathroom yasa hanna ta gyara d'akin fess ta feshesa da air freshner mai d'adin kamshi,aunty ce tai sallama ta shigo daidai lokacin da mamii ta fito, aunty tace "ya jikin naki mamii" 
"Da sauki maryam"  aunty tace "to ALLAH ya k'ara sauki "  amsawa tai sannan suka fice daga bedroom d'in, bathroom hanna ta shiga ta wanke tass ta gyara gidan sai kamshi yake mamii tana murmushi tace "ALLAH ya miki albarka Daughter "
  Yana zaune a office yaji  ana knocking sai da yaja kusan few seconds sannan ya bada izini ,leemat ta shigo fuskarta kamar duwawu tsaban 6acin ran da take ciki murya a cunkushe tace "sir kanada bakuwa" 
  Sosai yayi mamaki batare daya d'agoba yace "ta shigo"  fuuu ta fice kamar kububuwa ta kalli siyama a wulakance tace "zaki iya shiga"  siyama ta ta6e baki batako kalletaba ta shiga babban office d'in,
  Ajiyar zuciya siyama ta sauke tuni taji wata nutsuwa ta saukar mata kura masa ido tai cikin tsananin kaunarsa da begensa ,cikin nutsuwa ta taka kujerar da tagani ta zaman baki sassayan turarenta ya fara masa iso lokaci daya ya sake tamke fuska, murya a sanyaye tace "brk da aiki haydar ykk"
  Still yayi yana saurarenta can yace "lfy"  lokaci ďaya taji hawaye ya ciko idanunta murya na rawa tace "dama zuwa nai mu gaisa naji ko lafiya ina kiranka bakai picking ba"  tausayintane ya kamasa jin tana kuka sai sannan ya d'ago dakai ya kalleta sau d'aya yad'an tausasa murya yace "lfy aikine yasha kaina "  ba karamin dad'i taji ba yadda yayi mata magana taji ta samu karfin gwiwa narke murya ta sakeyi tace "ohk dama magana nakeson muyi nayi nayi dakai mu had'u kaki bani dama pls haydar ko yayane kabani lokacinka"
   "Ohk zan kiraki,ina aiki yanzu"  dad'i taji sosai tace "Ohk ngd sosai haydar ALLAH yasa ka cika alkwari,ina fata zaka wuni cikin koshin lfy" 
  "Thanks" kawai yace mata yacigaba da aikinsa,handbag d'inta ta rataya batadamu da yanayinsa sbd tasan haka yake ta fice ,a kofar office tai kici6us da leemat tana ganinta ta koma wajen zamanta,siyama ta ringa kallanta cike da mamaki can ya ta6e baki ta wuce ,wani dogon tsaki leemat ta saki tana neman hanyar da ko magana haydar yayi mata ko zata samu saukin feeling d'in da takeji a kansa,
  Zumbur ta mik'e ta gyara fuskarta ta fesa turare me uban kamshi ta zazzago da rigar jikinta me roba roba ta kwankwasa office d'in ,Shiga tai bayan ya bata izini ta lankwashe murya tace "sir kanada bukatar wani abune"
  Girgiza mata kai yayi ,ta sake lankwasa murya tace "a kawo maka coffee sir"  a d'an tsawace yace "nace miki bana bukata"  jiki na rawa ta fice  cike da kunan zuciya ,siririn tsaki ya saki yace "stupid "
  Tana tsaye a kitchen tana wanke kayan data 6ata mamii ta shigo tace "sannu yar albarka " murmushi hanna tai tace "yawwa mamii ya jikin naki"  "naji sauki Daughter ,bari na tayaki"  hanna ta zaro ido ta shagwab'e murya tace "nidai aa mamii na gama komai ki koma ki huta"
Murmushi mamii tai ta fice ,ta gama wanke komai ta goge kitchen d'in ,upstairs ta haura ta shiga bathroom d'in mamii tai wanka ta sauya kayan jikinta zuwa riga da wando pakistan jajaye sosai sukai mata kyau ta fesa bodyspry masu dadin kamshi,Jin ana kiran sallah yasa ta tada sallah magriba tana sallah mamii ta shigo itama ta d'auro alwala ta tada sallah suna idarwa karatun alqur,ani sukai tare har akai isha,i sannan suka sakko downstairs,
  Daidai lokacin big daddy da  haydar da mus,ab suka shigo dawowarsu kenan daga masallaci, parlounsa ya nufa mamii ta tashi tabi bayansa,  haydar kuwa dining ya nufa kai tsaye ya shiga zuba abincin da kamshinsa yayi mugun tafiya dashi ,sakwarace da miyar ganye da busashshen kifi sai couscous da akai da nikakken naman kaza ,
  Yana cikin ci hanna da mus,ab suka k'araso kujera ta jaya mus,ab tace"kuma yaya kaci saikaban tukwici "
  Dariya yayi yana zama yace "to ALLAH yasa kar jagwalgwalo kikai mana"  6ata fuska tai ta turo baki daidai sanda mamii ta iso tace "mamii aidai na iya girki ko,kusan kulluk fa ni nakeyiwa aunty"  murmushi mamii tai tace "kwarai ma kuwa ae yau duk abinda kukaci ita ta dafa" haydar yayi shiru yanajinsu can ya ajiye cokali yana yatsina fuska yace "yanzu mamii dama jagwalgwalon wannan yarinyar naci yau?"
Bude baki mamii tai tana kallansa hanna kuwa tuni ta fara kukan shagwab'a tana dire kafafu dan ta tsani tayi abu a kushe,mus,ab ya rufe baki yana dariya k'asa k'asa mamii tace "to sannu honorable saida ka cinye tass zakazo kana hurawa mutane hanci,inace dazu har kirana kai kace a ajiyemaka ragowar kunun gyada ko ba,ae haka ba"
  Haydar ya had'e rai yana hararar hannah data fara dariya juyawa yayi ya fice yana jinsu suna masa dariya .
  Sai can dare ya sakko kusan karfe 10 yana sanye da jallabiya dining ya nufa ya zuba couscous d'in a plate ya fara ci dan dama dazu sakwara kawai yaci, jiyai ana kyalkyala dariya a bayansa yayi shiru na kusan minti 1,hannah ta k'araso dining d'in tana dariya  dan dama in mamii batada lfy sai tayi sati a part d'inta tana tayata aiki kasancewar batada yarinya kuma batason yar aiki,sanye take da kayan bacci masu kauri hakan bai hana dirinta fitowa ba zama tai a kujerar ta karkata kai ta dakko plate tsaban tsokana irin na hanna ruwa ta fito dauka amma ta wuce dining ta kunce bakinta ganin wani mugun kallo da yake aika mata,ta janyo flask din couscous d'in ta zuba kad'an cikinta a koshe yake haka ta ringa tsakuwarsa, ajiye cokalin haydar yayi cike da mugunta ya juye wanda ya faraci fuska d'aure yace "ki tabbatar kin cinyesa duka"

HannahWhere stories live. Discover now