Hannah part 12

437 31 2
                                    

💥 *Hannah* 💥

1️⃣2️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Sanye take da riga da sket na wani yadin material coffee colour ya mugun karbar jikinta bata d'aura dankwali ba tay rolling d'in mayafi peach ba wata kwalliya a fuskarta amma tayi kyau sosai,
A parlour ta tadda aunty da basma ,kallanta aunty tai tace "kije bedroom d'ina ki dakko wata Leda a bedside ki Kai mata"
"To aunty" tace bata jimaba ta fito rike da ledan tai musu sallama ta zura plate shoes ta fita harta yi hanyar apartment d'in mamii ta juya ganin motar ya farouk ,da sallama ta shiga side d'insu direct kitchen ta nufa jin motsin mutum ,mum ce da Yar aikinta suke girki cikin Fara,a tace "yan makaranta kinyi wuyar gani keda kawar taki" tana murmushi tace "wlhy mum in muka fita tun safe Sai yamma yauma mun tashi da wurine"
"Masha Allah to adai maida hankali Banda Kula samari" hanna tace "insha Allah mum,ya farouk yana ciki ko?" "Eh Shima bai Dade da dawowaba".
"Ok Sai anjima" daga haka ta fito daga kitchen d'in ta nufi dakin farouk,kusan knocking d'inta 3 sannan yace a shigo" yana kan gadonsa yanata faman aiki ba tare da ya d'agoba yace "wayene?" Tura baki tai ta zauna kan stoll tace "ni tunda bazaka d'ago ka ganni ba to sai anjima" da sauri ya ture laptop d'in dake gabansa ya rik'o hannunta ya marairaice fuska yace "karki tafi baby pls bakisan nayi kewarkiba kwana biyu fa rabon dana ganki,"
Ta had'e rai tace "ni Allah ba waninan kawai bakaso ganinaba" murmushi ya saki yace "toh yi hkr ya hanna na tuba bazan sake ba" a tare suka fashe da dariya hanna tace "Allah ya farouk duk ka kirani da ya hanna ji nake kamar naima wata katuwar kyauta da zatasaka farin ciki" hannunta dake cikin nasa ya damke cikin wani yanayi mai dadi yace"Nan gaba zan fad'a miki kyautar da zakimin ,idan har kikamin ita zan dawwama cikin farin ciki zan kasance cikin jerin mutanan da suke da sa,a da nasara a rayuwa " kallansa tai kafin ta zare hannunta ta mike tace "to meyasa bazaka fad'amin yanzu ba?"
"Lokaci baiyiba"
Yace mata yana kallanta Bata kawo komai ba ta ta6e baki tace "nidai na tafi Sai anjima" da kallo yabi bayanta harta rufe kofar ,ya jingina jikinsa akan pillow ya dafe saitin zuciyarsa Yana sakin murmushi Shi kad'ai kasa kasa yace "insha Allah ke tawace ni nakine" laptop d'in ya dakko ya cigaba da aiki yana sakin murmushi Shi kad'ai,
Kai tsaye part d'in mamii ta wuce da sallama ta shiga mamii tana zaune a parlour da gudu ta wuce wajenta ta fad'a jikinta tace "nayi missing d'inki mamii na" tuni fuskar Mami ta Kuma fadada da Fara,a tace "Nima haka dota kinyi wuyar gani ya makaranta" "lfy Lau mamii" tace Tana sake lafewa a jikinta ,hira suke mamii tana jefo mata tambayoyi akan makaranta tana amsa mata still tana kwance a jikinta,a haka haydar ya shigo ya samesu yatsina fuska yay yana kallan hanna yace "mamii duu ke kike Kara shagwa6e wannan yarinyar jifa yadda ta wani lafe a jikinki kamar wata mage ,"
Hararasa Mami tai tace "sannu sarkin Yan korafi inace cakai jikina ba nakaba ko? Ka bari duk ta rabi jikin naka Sai kayi korafi" da sauri ya wani zaro ido kamar yaga wani abin tsoro yace "what? Mamii jikina fa ,"
Hararta yayi ya wuce upstairs hannunsa rike da jakar laptop d'insa, Saida taga wucewarsa ta gallawa bayansa harara cike da jin haushinsa,
Bata koma bangarensuba suka shiga kitchen tare da mamii,lafiyayyan dambum couscous hanna ta had'a da yaji yankakkiyar hanta da kayan lambu Sam hana mamii aeki tai sai dan taimaka mata da take da wani abun, ta had'a fruit salad da kunun aya kana tayi farfesun k'oda gaba d'aya kitchen d'in ya gauraye da kamshin girkinta,
6:30 suka kammala ta wuce dakin mamii anan tai wanka wardrobe d'in mamii ta bude ta dakko wata gown me roba data lafe a jikinta ta mata kyau sosai , already dama tayi alwala hijab kawai tasa ta shimfid'a dadduma ta tada sallah,
Bata sakkoba Sai da akai sallar Isha,i a sannan ta sakko,
Mamii ta tadda a dining Sai mus,ab Yana danne danne a waya,bayansa tazo ta tsaya tace "hii"
"Hi parrot yane" Kujera taja ta zauna tace "kalau ya mus,ab baka gajiya da danna waya"
"Ke Kuma baki gajiya da tambaya da da tsegumi ko?" Ta had'e rai tace "ya mus,ab nice nake tsegumi ko?" Dariya ya saki ya ajiye wayar yace "dalla zona nuna Miki wani Abu Kuma saura ki fad'awa wasu" ta washe baki ta matso kusa dashi wayarsa ya Mika mata kasa kasa yace "kalli"
Kallan pic din daya nuna mata take wata yarinyace da bazata wuce sa,ar taba kyakykyawa da ita Masha Allah, "wow ya mus,ab wace wannan?"
Dan hararta yayi yace"kefa kin fiye shirme babynace" Dariya ta kyalkyale da ita har mamii ta juyo tana kallansu tace "lafiya?" Da sauri mus,ab yace "kalau mamii Hira kawai muke". Ta6e baki tai ta ajiye warmer d'in data dakko,
Warce wayar yayi yace "Kuma saura naji kinba wani labari" dariyar ta daina tace "amma tanada kyau wlhy a ina take" fuska ya saki yace "haba saima kin ganta a fili a sani me nagge suke" kasa ta sakeyi da murya tace "to yaushe zaka kaini wajenta mu gaisa" shigowar daddy da haydar ne yasasu yin Shiru,
Mamii ta zubawa daddy Hanna ta zubawa haydar da mus,ab farfesun ne da tazo kan haydar ta kewaye ta zuba nata dana mus,ab ta koma ta zauna, wani kallo yake mata ta kasan ido banda daddy na wajen ba abunda zai hanasa fizgota ya sheka mata Mari ba, gashi banda kamshin farfesun ba abunda yake dukan hancinsa, kallansu yayi yaga hankalinsu yanakan abinci a hankali ya janyo flask d'in Yana satar kallansu zai zuba caraf ta rike Masa hannu tace "au sorry yaya na rantse nazata bazakaciba shiyasa ban zubama ba "
Mus,ab ya kusa sakin dariya ganin irin kallan da yake mata ,hanna kuwa ta fuske dama tana sane tai Masa haka tasanshi da son farfesu data tashi saita zuba masa baifi yanka 5 ba ta koma ta zauna tana rufe baki sbd dariyar da takeson kamata,
Ta k'asan ido ya ringa kallanta kallo Mai cike da Zaki gamu dani bai yarda ya kalli farfesun ba yacigaba dacin dambun shine farkon tashi bayan ya goge bakinsa da tissue,
Ta gabanta ya wuce yasa takalminsa ya murje mata k'afa ,wani uban ihu ta fasa ta zube a wajen ta shiga rusa kuka ,tsallaketa yayi ya wuce Yana murmushin mugunta da sauri ya fice jin Mami na kwala masa kira ,tuni wajen yayi ja abinka da farar fata, mamii ce ta mike da sauri ta tarota tace "subhanallah dota garin Yaya?" Kasa magana tai Sai kuka da take ga wani radadi da takeji a kafar ,
Man zafi mamii ta shafa mata ta rakata har bangarensu Banda Allah ya isa ba abunda takeyi Saida mamii taga ta samu bacci sannan ta fito aunty dama tunda taji abinda ya faru tasan za,a rina Kota kanta bata biba tai wucewarta daki.
Washe gari tana tashi part din mamii ta nufa bayan ta boye wani magani a hannunta , a kitchen ta tadda mamii tana breakfast, murmushi mamii tai tace "dota harkin tashi? Ya kafar taki" karbar kayan da mamii take tai tace "eh mamii naji sauki Ina kwana" "lfy Lau dota" mamii tace daga Nan suka shigaba da had'a breakfast d'in,da farar jallabiya haydar ya sakko ya karaso kitchen din yana kallan hanna Sai Kuma yacewa mamii "mamii a hadamin coffee pls fita zanyi yanzu akwai meeting d'in da zamuyi"
Mami tace "ohk amma ka tsaya Kai breakfast ko" girgiza Kai yay yace "aa mamii zanyi late innaje can nayi" muryar Hanna yaji tace "Yaya Ina kwana" Saida ya kalleta yace "lafiya ," Yana fad'a ya wuce d'akinsa, coffee d'in mamii ta had'a a mug ta dora akan tray tace "dota maza kaiwa yayanki d'akinsa" saboda tsabar dadi har murmushi ta saki tace "to mamii"
Kar6a tai ta wuce tana sakin murmushin mugunta, Saida ta tsaya ta bud'e maganin ta balli guda 2 ta zuba a ciki ya narke sannan ta kwankwasa d'akin kusan 2mnt sannan yace ta shigo,
Harya shirya cikin army green suit kallansa tai tace "Yaya gashi mamii tace na kawoma" bai kalletaba yace "ohk" ta Kuma cewa "Ina zan ajiyema Yaya" hararta yay yace "ki ajiye a kaina"
Turo baki tai tace"nidai Yaya Mami fah tace karna fito saika shanye" ta6e baki yay ya kar6i mug din ya zauna ya farasha a hankali,tsura masa ido tai tana murmushi da ita kad'ai tasan ma,anarsa harara ya galla Mata yana Miko Mata mug d'in yace "saiki fice tun kafin ki cinyeni da wannan kwala kwalan idanun naki" dariya tai bayan ta kar6a Saida ta bud'e kofar ta fita ta leko da kanta tace "na rantse kaima kwala kwalan idon ne dakai,daka harareni ma na zata idon horo ne" da gudu ta sauka tana kyalkyala dariya ganin yadda ya zaro ido murmushi ya saki Yana girgiza Kai ya rataya jakar laptop d'insa ya sakko hannunsa rike da mukullin mota,

HannahWhere stories live. Discover now