Hanna 47

170 19 0
                                    

*HANNA*.......💥

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

   *47*

Hannu yakai ya bubbuga filon da take kai da karfi , bud'e ido tai tana sakin tsaki ta kalleshi a fusace tace  "Malam lfy ina baccina zakazo ka wani tasheni, bashi kake  bina kome?"  Hade  rai yay dan  kar taga warginsa fuska ba walwala ya mika mata card din hannunsa , wani tsakin ta kuma saki ta fizge da karfi ta bude ta fara karantawa , "kan ubancan," ta furta tana hantsilowa daga  kan gadon ta cakumosa da karfi tace  "wllhy tallahi uban  kuturuma yay kadan  balle  na makaho, ni  zaka yaudara mk? Ni zakaci amana ?" Ta fad'a tana nuna kanta ,tai wani dariya tace  "billahillazi sunan wannan auran lalatacce , kamar yadda na rusa wancan haka zan rusa wannan ,in zaka nemi aure sau  dubu saina  lalata sau  dubu , saina  zamar maka bakar Inuwa wllhy baka isa  kamin kishiyaba da ajina d,,," bata  karasaba ya wanke fuskarta da wani mari ta bude baki tana kallansa ya sake zabga mata wani marin, ihu ta fasa  da karfi ya fizgota a fusace yace  " zan buga  miki  last warning wllhy tllh naga kafarki a gidansu Jidda saina  kusa sumar dake  kinji na fada miki stupid kawai " ya hankadata yay wucewarsa daga dakin,
   Wata irin dariya tai kaida ganin dariyar kasan ta takaici da bakin  cikice ,card din ta dakko ta duba address din gidan , wata figalalliyar gown ta dakko tasa ta yafa vail  a kanta ta d'au mukullin motarta ta fice daga gidan bayan tasa wani bakin glass da kana ganinsa kaga na rashin mutuncine,
   Kallan gidansu Jidda take cike da kunar  nai ta cije lips d'inta  tai parking din motarta ta fito a fusace , da karfi take bubbuga get din gidan tana kunduma duk zagin da yazo bakinta , me gadin Yana budewa dama ta hankadashi ta shige ,
   A compound din gidan ta tarar da Jidda ta rako wata kawarta suna magana , kallanta hanny tai ta zare glass din idonta ta nufi inda suke  a fusace tace  " wacece Jidda anan?" Jidda da tun da tazo wajen itama ta d'aure fuska cikin rainin wayo tace "ga Jidda nan , uwarme Jidda tai ake nemanta" hanny ta shaka a fusace ta kunduma mata zagi tace  " ke karamar yar  iska, yar  tasha ballaga zuwanai nai miki  kashedi akan mijina , wllhy in baki fita harkar mijina ba  nice ajalinki , mijina yafi karfinki ta kona nafi karfin na had'a kishi da wata ya mace a duniyarnan , ba boka ba malam zan wulakanta rayuwarki idan kikai kuskuran sake kallan mijina,ya rage naki kiyi tunani in kuma kin shirya mutuwa yanzu to bisimillah" wata shewa Jidda ta saki kafin ta kalli hanny tace  " shin uwarki data tashi auran ubanki bai sanar  da ita  mata 4 aka halastawa namijiba ? " bude baki hanny tai cikin tafasar zuciya ,Jidda ta cigaba da cewa "idan matsiyaciyar uwarki baka koya miki tarbiyya ba toni Jidda zan koya miki ita  , gidanki kuma kamar na shigo na gamane idan har  dabanci kike  takama dashi to ni nan na takeki na cinye , nida aka haifa a bariki har  kya nunawa karuwanci da burga ? To ki shiga  hankalinki Jidda tafi karfinki wllhy ba Sa,ar  yinki bace ni , zan bambamce miki aya da tsakuwa , gidanki kuma ki shirya inan  tafe insha Allah da duk kalan zaman da kikeso ayi , shege ka fasa"
   Hanny ta kai hannu zata cakumota da sauri  Jidda ta kankadata ta kife  a wajen sukai wucewarsu itada kawarta bayan sun tofa mata miyau,
   Dakyar ta mike cikin tsananin tashin hankali ta shiga  motarta sai  sannan ta saki kuka , irin  mugun kudurin data dauka akan Jidda ita kadai ta barwa zuciyarta , saita wulakantata kamar yadda ta wulakantata yau  ,
 
   Bangaren Hanna ko tuni ta warware , dan  dama  cikin bamai laulayinnan bane sosai sai kwadayi data Karo, kusan kullum mami sai tai mata abin kwadayi driver yakai mata , hakama aunty takan kirata taji ya jikin nata  yake  , uban gayyar ko ba,a maganarsa dan wani sabon  tattali da kuluwa  da yake  bata  , dan  cikin nata sai yazo mata dasan sex sosai Wanda hakan ba karamin dadi yaywa haydar ba dan  ko be nemtaba da kanta take nemansa ,  ,dama inya dawo gida  ko k'ofar get bai sake lekawa indai ba masallaci  zashiba , da daddare suna makale da juna tana jikinsa suke  komai , saidai zatashi zai ajiyeta wai  kar babynsa hanan ta wahala ,
  Hanna ko tuni ta sake baje kolin shagwabarta son ranta  , sai abinda takeso haydar  yake , tattalinta yake  sosai ,
   Da yake  week end ce  yau  tunda suka tashi ta saka masa  rigimar ita  gida  takeso , tana kwance a jikinsa sai kuka take kana ganin kukan kasan  zallan shagwabace , cikin lallashi yace "haba  sweet kinsan  banason fita  week end ki bari ran Monday saina  kaiki in na dawo daga office saina  biyo na d'aukeki ko?" Turo baki tai ta mak'e  kafad'a tace  "aa  nidai yau  nakeson zuwa gsky" "pls banda yau  sweet kinji" ya sake fad'a mata a hankali , tuni ta sake makalkaleshi dan  yanayin yadda yay maganar taji tsigar jikinta na tashi ta sake sakin  wani kukan , dariya yay a hankali yace "yanzu naji batu yarinya kice  kawai jarabartakice ta motso shine zaki isheni da kukan gida" hararsa tai tace  " eh din naji , aidai sadakina nake  mora ko?" Lokaci d'aya ya fashe da dariya yace "eh fa lallai sadakinki , ki mori abunki dakyau yarinya " filo ta d'auka ta jefa masa  ya cafe yana dariya  , ta hade rai ta koma kansa  ta ta dinga kai masa  kanan duka a kirji dan  kanta ta gaji ta bude baki zata fara sabon  kuka ya hade bakinsu tsaf Yana kallan tsakiyar idanunta dake kara jefata a wani yanayi.

HannahWhere stories live. Discover now