Hannah part 29

396 37 4
                                    

💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
        2️⃣9️⃣

*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*
*Whattpad@OumRamadan1*

Hajiya zainab mom din Hanny ce ta fara fitowa a rikice tace "lafiya alhaji irin wannan Kira" ko kallanta baiba ya cigaba da kwala Hanny kira, fitowa tai kanta tsaye dan tuni ta shiryawa duk wani qalubale da zata fuskanta duk da yadda gabanta yake dukan tara tara haka ta k'araso parlourn ,kallanta yay fuska murtuk yace "kinsan Dan gidan tsohon sanata ? Sanata kabeer ?" Ta gyada kai kamar munafuka,kirjinsa ne ya doka da karfi cike da tashin hankali yace "abinda mahaifinsa ya fad'i tsakaninki da d'ansa gskyne kenan?" Ja baya ta dingayi tana sosa keya gabanta na fad'uwa tace "eh dadd,,," kafin ta k'arasa tuni ya d'auke ta da wani mahaukacin mari hagu da dama,ihu ta fasa ta juya zata gudu ya kamota a fusace ya shiga dukanta ta ko Ina ,Hanny na ihu hajiya zainab na ihu Saida yay mata lis ya saketa yana huci ya juya a fusace Saida ya daidaita kansa kana ya shiga wajen su senate,
  Kunya ta hana ya kallesu da bakin ciki  da takaicin halin da yarsa take ciki bai sani ba , a haka suka gama tsaida maganar bikin duk da alhaji lawan yaso a kara kodan fad'awa Yan uwansa hujjojin da senate ya bashi da kuma illar d'aga auran yasa ya amince ,inda senate yace ya d'auki nauyin komai da za,aewa hanny na kayan d'aki duk da shima ba laifi alhaji lawan da nasa rufin asirinsa,
  Bayan tafiyar senate daddyn hanny yasa aka kwashe kaf akawatunan da aka kawo aka shigar dasu parlourn hajiya zainab zama yay akan Kujerar ya kwalawa hajiya zainab Kira ,fuska d'aure ta fito dan ba karamin jin haushin dukan da yay wa yarta taiba,
   Fuska murtuk ya yace "jeki kiramin haneefa" juyawa tai tana kallan akwatunan da suke jibge waje guda a haka ta kamo hanny da jikinta yake Mata ciwo danba karamin dakuwa taiba ,
  A jikin mom d'inta ta kwanta cike da takaici alhaji lawan yace "wlhy kinci sa,a uban abokin shashancin naki ya zo nemarwa dansa auranki ,da ni da kaina na gano halinki me gadi zan aura wa ke shashahar yarinya kawai" fuska d'aure hajiya zainab tace "waini alhaji ban ganeba ,dazu kazo ka mata mugun duka yanzu Kuma kazo ka rufeta da fad'a baka fad'amin abinda taima ba,yau ko wani abu Hanny taima ka rangwanta Mata karka manta itafa kad'ai gareka a duniya"  wani mugun kallo yakebinta dashi a fusace yace "Naga alamar kema kike d'aure mata kugu,a gidannan na kafa doka nace karki ringa barinta tana fita ko Ina ashe barinta kike tana gantalinta a titi tana watsewa da samarin banza ,inacan ina nemar muku abinda zan rufa muku asiri ni kuna tonamin nawa a gari, kinsan Allah banda yaron zai aureta sadakarta zan bayar hankalina zaifi kwanciya da irin rayuwar da take, ga kayan lefanta Nan da kudin sadaki nan da kwana 3 za,a d'aura Mata aure" daga haka ya mike ya fice a fusace, zaro ido hajiya zainab tai tanabin akwatunan da aka jibge da sunan lefen yarta kallan Hanny tai da tunda taji auranta da mk ya tabbata ta wartsake tuni ta nemi ciwon da takeji ta rasa, "Hanny dan gidan wa kika samo Mana" hajiya zainab tace tana janyo akwatunan ta shiga bud'e wa baki ta bud'e tana kallan uwar dukiyar da hajiya Sara ta narkar , "dan ubanki nace danwa Kika samo Mana" hajiya zainab ta sake cewa cike da rudewa idanu a waje , murmushi hanny ta saki tace "mom kinsan tsohon senate dinnan Senate kabeer?" Gyad'a kai tai Hanny tace "to d'ansa ne"
Wata uwar guda hajiya zainab ta saki ta mike ta shiga taka rawa ko takan maganar da alhaji lawan yay Mata bata biba tuni ta dauko waya ta shiga Kiran Yan uwanta da kawayenta tana sheda musu abin arzikin daya samu 'yarta ,
Dama ita Hanny ta gama shirya event din da zatai waya ta dakko ta kira aminiyarta zeey tana d'agawa tace "kawata komai ya kammala  yanzu haka maganar da nake Miki har an maido da lefe gidanmu Kuma biki Nan da 3days" ihu zeey ta fasa a rikice tace "inanan tafe kawata" kashe wayar Hanny tai tana tsallen murna,
Kan kace me tuni kawayen hajiya zainab da Yan uwanta sun cika gidan anata shewa da kirga kayan lefe masu gulma nayi masu hassada nayi da masu mugun fata,
Tuni masu decoration suka gama tsara wajen kamun daya kayatu matuka a compound d'in gidansu hanna, Kota Ina  ka juya yammatane da sukai ankon wata atamfa yellow da tsarin ja da fari hatta head d'insu kalan jane, yayinda iyaye Mata sukai ankon lace yellow da akaiwa ado da red and black, gefe ga Yan kidan kwarya Nan sunata wasa manyan mata ana zuba musu liki wasu daga cikin yammatan suna tsakar filin rawa suna juyawa,
  Aunty da mami da mum din fannah da mum din Sameer sai sistern su mami ankon wani dakakken lace sukai dark blue da akaiwa adon pich clour hatta da mayafi iri d'aya sukai yayinda aka nad'e amaren cikin lifaya me asalin kyau da tsada  sunsha make up dole su burgeka in suka ganka , a haka aka fito dasu har wajen da aka tanadar musu ana musu ruwan liki masu kidan kwarya suna musu kirari, a haka aka gudanar da kamun cikin kayatarwa da burgewa taro ya tashi lfy inda aka rarraba jakunkuna cike da kayan arziki a ciki,
  The next day ya kasance event d'in mother's day wannan karan a meena event center akai kawayen amaren kad'anne sai manyan mata iyaye dama shiga iri d'aya wannan karan mami tai daga ita sai  aunty lace ne daya amsa sunansa kana kallansa basai an fad'a maka Mai tsada bane sbd tsabar kyansa ,
tawaga guda hajiya sara tai ita da matan sanatoci da manyan Yan kasuwa  sunyi shiga ta kece raini gwala gwalai kamar zasuyi magana, sudai su Mami basu nuna musu komai ba haka suka tarbesu ba yabo ba fallasa,
  Farin lace hanna tasa dinkin riga da sket da akai masa adon gold sket d'in irin me step step dinnan ne  daga gwiwa komai na jikinta farine tas sai d'aukar ido take hatta da siririn sarkar ta farace tasha make up tamkar ka saceta ka gudu ,
  Yayinda basma tasa lace ash clour fannah tasa kalan light brown dukansu sunyi kyau Masha Allah,
  Ado Gwanja yana gefe yana wake manyan mata ana zuba masa ruwan kudi,
  A tsarin event d'in ko wace amarya zata fito danginta suyi mata liki ,hanna aka fara kira inda ta tsaya a filin rawa ita kad'ai wakar gwanja sai tashi take , hajiya Sara da tawagartane suka fara shiga notice d'in Yan dubu dubu hajiya sara ta 6alle ta shiga yiwa hanna liki masu take Mata baya suna tayata sunayi suna d'an takawa tuni masu vedio da pic suka shiga aikinsu liki sosai sukai sannan suka fito, su Mami da aunty da Yan uwa suka shiga suna Mata liki cire kunya Mami tai ta rumgumo hanna tana juyi da ita a hankali tana yar rawa dariya aka saki aunty ta fara musu liki tare haka sauran Yan uwa da friends din Mami da aunty sukai liki sosai sannan suka fita ,
  Fannah aka fito da ita mum din Sameer da Yan uwanta da kawayenta Suma suka shiga yi mata liki ana hotuna sannan sannan su mum d'inta da Yan uwanta suka shiga Suma sukai nasu likin,
Basma ce karshe daganan duk aka had'u akai liki kusan karfe 6 aka tashi bayan an raba manyan gift dan bayan Wanda su Mami sukai hajiya sara ma tayo wani na musamman me d'auke da tambarin hoton amarya da ango aka rarraba sudai su aunty basu kar6a ba sai ido da suke binta dashi haka dai taro ya tashi lfy kowa ya tafi da abun arzikin sa a hannu.

HannahWhere stories live. Discover now