Hannah par 10

413 32 5
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
       1️⃣ 0️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

*DEDUCTED TO HANNAH FAN's GROUP 1 WANNAN PAGE D'IN NAKUNE KUYI YADDA KUKE SO DASHI INAJIN DADIN CMMNT DINKU OVER*😍🥰

*Yan whattpad Amin afuwa rashin lfy nai na Dakatar but Alhamdulillah yanzu na dawo zan cigaba da post ina fata zaku gafarceni.

Yau ta Kama Monday a ranar Kuma Hanna zata Fara d'aukar lecture,tsaye take a dining Tana fifita tea da sauri ,aunty ce ta fito rike da warmer ta ajiye a dining d'in tace ,
  "Saurin me kike haka? A tsaye kikecin abinci?
Marairaice fuska tai tace "aunty na kusa latti fa Kuma time table d'in 8 daidai ne gashi yanzu 7:30 tayi"
  Ta6e baki aunty tai tace "kinsan da haka Kika koma bacci" kamar zatai kuka tace "Allah bansan sanda ya daukeni ba daga azkar fa" itadai aunty ci gaba da jera dinning d'in tai batace komai ba ,Hanna kuwa a gaggauce Tasha tea sama sama tai sallama da mutanan gidan Dan basma batada lecture rannan,
  Banda duban agogon hannunta ba abunda take a hanya ,karfe 8 daidai ta iso Yusuf Mai tama sule ,ko sallama Bata tsaya yiwa driver ba ta wuce Kai tsaye zuwa harabar makarantar ,
  Saida tadan tsaya ta tambayi hall din da zasu lecture ta wuce da sauri Dan lokacin 8 ma ta gota,
  Tun data doshi hall din taji tsit Sai tashin wata murya da takeji cikin cool voice dinsa Yana zuba musu turanci,
  Kai tsaye ta doshi kofar shiga ba tare da wani shakku ba a nutse tai sallama cikin siririyar muryarta,
  Lokaci d'aya taji kamar ta kifa ganin yadda duk Yan hall d'in suka zuba mata ido, da kyar ta daure fuska ta tsare gira ,da karfin Hali irin nata ta wuce sit d'in da ta hango wata mace ita kadai Sai da ta zauna  taji ance ,
" Get out"
Dago da Dara daran idanunta tai ta zubasu akan matashin saurayin da bai wuce 32 a duniya ba fuskarsa tamkar hadari hakan bazaisa ka kasa gano kyansa ba , kyakykyawane sosai dogo yanada faffadan kirji kalar fatarsa chocolate ne da kana kallanta zakasan Hutu ya ratsata,
  Ganin yadda ta zuba Masa ido tana kallansa ya sake hassalasa cikin tsawar da tafi ta dazu yace ,"I said get out now"
A firgice ta Mike sbd razanar datai ta Bata fuska tuni hawaye ya Fara ambaliya akan fuskarta ta kwashi handout dinta cikin tsananin takaici da wata tsanarsa data shigeta ta wuce fuu ta gabansa,
Dogon tsaki yaja ya koma gaban hall din ya cigaba da abinda yake,
Karkashin wata bishiya ta zauna ta dinga rusa kuka Sai da tai Mai isarta ta share hawayen Banda tafasa ba abinda zuciyarta take , ta dad'e a wajen Tana sake sake a hankali take sauke ajiyar zuciya tana kalle kalle,
  Tana zaune taga fitowarsa daga hall din ,wata harara take zuba Masa ta gefen ido kamar idanunta zasu fad'o, Sai  da taga ya kusa zuwa gab da ita ta d'auke Kai ta had'e rai,
  Baiko kalli inda take ba ya wuceta ta raka bayansa da harara tana Jan tsaki,. Jitai an dafata a firgice ta waiwayo yarinyar dazu ce da ta zauna a sit d'in da take,
  Hanna batace mata komai ba harta zauna kusa da ita tace "sunana rauda alkasim kefa"
A takaice takaice tace "Hanna Yusuf"
Murmushi rauda tai tace "kiyi hkr da abunda Barr Mk yayi Miki duk da Yau na Fara zuwa makarantar Nan naji ana fadarsa bayan fitarki baya ta6a yadda ki shiga hall d'in da yake matukar ya shiga ki ringa zuwa da wuri kinji"
  A hankali tace 'toh ngd"
Amma a ranta Sai maimaita barr mk tace lokaci d'aya taje wani mugun haushinsa ya dirar mata,rauda ce ta katse mata tunanin da take tace "yakamata mu koma hall nan da few minutes zamu shiga wata lecture"
Mikewa Hanna tai batace komai ba suka Fara tafiya ,a nutse rauda take d'an janta da Hira duk da sama sama Hanna take amsa mata a haka suka k'arasa hall d'in.
  Karfe 1:30 suka fito a gajiye Kai tsaye masjid suka nufa Saida sukai sallah sannan rauda tace "muje cafeteria muci abinci ko?" To kawai tace  , a hankali suke tafiya har suka karisa,
  Karfe 2daidai suka fito a tsaitsaye rauda ta koya mata lecture d'in datai missing ta malam Mk duk da itama bawai ta gane dukaba  kafin su shiga wata lecture d'in,
  A gajiye ta fito daga mota tayi wani wujiga wujiga da ita Sai sakin tsaki take tana turo Baki ta wuce part d'insu a parlour tai watsi d handout d'in ta wuce bedroom d'insu da sauri ,
  Da kallo basma ta bita tana dariya kasa kasa ta tsallaketa ta wuce toilet,
Kimanin minti 10 ta d'auka ta fito d'aure da towel ta fad'a Kan gado a hankali tace "wash Yaya basma na gaji "
Basma ta tuntsure da dariya tace "tun yanzu ?" 6ata Rai tai a gaggauce ta shirya ta wuce bedroom d'in aunty bata same taba jin motsin ruwa a toilet ya tabbatar mata da tana ciki,
  Kwanciya tai akan gadon auntyn tana tuno malam Mk dogon tsaki taja tana cije lips d'inta har yanzu takaicin abinda yay mata take,
  "Lafiyarki kuwa kike tsaki ke kad'ai?" Cewar aunty data fito daga toilet, yamutsa fuska tai tace "wlhy aunty gajiyace kawai nai" Zama tai a getenta ta kamo ha6arta tana kallan kyakykyawar fuskarta tace "bansan autata da karyaba gayamin me ya faru kike tsaki?"
  Cikin takaici tace "ba wani malamin mu bane ya hanani shiga lecture sbd nayi latti , Allah aunty duu na tsanesa bakiji tsawar da yamin ba"
Had'e rai aunty tai tace "kull na sake jin kince kin tsani wani,barantana malaminki,laifi kikai ya hukuntaki sauran da suka rigaki zuwa ya koresu" girgiza Kai tai aunty ta sassauta fuska tace "toh ki kiyaye kinji autata karna sake jin makanciyar wata magana tsakaninki dana gaba dake ba ruwanki da kowa indai ba karatune ya had'akuba ki rike mutuncinki da tarbiyarki"
  A hankali tace "to aunty" daga haka ta kwanta tana lumshe ido alamar bacci.
  Sai gab da magriba ta tashi sallah tai ta wuce part d'in Mami,haydar ta samu zaune a akan Kujera kamar zata wuce Sai Kuma ta dawo ta zauna kusa dashi cikin shagwa6a tace "ya haydar" kallanta yay ta gefen ido ya d'auke kai yana jiran yaji me zatace jin tayi shiru ya juyo da kansa ya tsurawa fuskarta ido yace "kinzo kimin fitsarar ne?" Dariya ta kyalkyale da ita ta mike da gudu ta nufi stair Saida tahau tace "dama kawai so nake kamin magana " Sai Kuma ta shagwa6e fuska ta turo baki tace "Kuma kowa yamin siyayya amma banda kai ko Yaya?" Shidai baice komai ba sai kallanta yake tace "Kuma Allah Yaya saina fad'awa mamii" tana gama fad'a tai wuce da kallo ya bita a hankali ya saki wani murmushin da saika dad'e bakaga irin saba.

HannahWhere stories live. Discover now