Hannah part 9

419 31 2
                                    

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣9️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

A cikin kwanakinnan gaba d'aya kan hanna yad'au zafi sbd jarabawarsu ta ssce da suka fara, cikin nasara da kwanciyar hankali suka kammala  jarabawarsu  sosai sakamakon yayi kyau, jamb suka zana inda hanna ta samu 256 fannah ta samu 198 ,
  Suna zaune a parlourn big daddy haydar yana zaune sai Farouk da shigowarsa kenan ,hanna da fannah suna zaune kan carpet gyaran murya big daddy yayi yace "masha ALLAH kunyi kokari sosai kuma naji dad'in hakan harma takwici da zan baku"  kwalin waya me kyau da tsada Samsung s9 ya  d'akko ya mika musu da tsananin farin ciki hanna tace "mun gode daddy ALLAH ya kara budi "  fannah ma tai masa godiya ,amsawa yayi ya kalli hanna yace "wane course kika cike?"  A hankali tace "law"  haydar ya d'ago da kansa da sauri baisan sanda ya saki karamin murmushi ba yace "wace zata karanci law d'in? Waike haka kawai kije kisa mutane asarar kudi,an gaya miki karantar law na dakikaine" Farouk kallansa yake ya had'e rai fannah ta rufe baki tana dariya ,hanna kallan daddy tai ta had'e rai tace "nidai daddy kace ba abinda ya shafesa dani,kuma wlhy ina kokari nifa nake zuwa 1p a makaranta kuma ka tambayi fannah,"   tai kasa da murya sosai ta yanda haydar bazaiji ba  sbd tana gab dashi tace "kuma ni ba dakikiya bace"  karaf a kunnensa danshi mutum ne da ALLAH ya yisa me saurin ji,kallanta haydar yayi cikin 6acin rai da takaici yana tunanin abinda zai mata,daddy ya dan d'aure fuska yace "ya isa badai shi kika cike ba" ta gyada kai yace "to insha ALLAH zaki karanci law nan nada jimawa ba zaki koma Barr hanna "  murmushi mai kamada dariya ta saki cikin jin dadi haydar kuwa ta6e baki yayi daddy ya kalli fannah yace "Daughter ke kuma me kika cike?"  Tana dan murmushi tace "medicine " murmushi daddy yace yace "to ALLAH ya taimaka" nasiha yayi musu a takaice sannan ya mik'e ya sallamesu, tashi hanna tai haydar yasa mata kafa luu ta tafi zata kifa Farouk ya tarota a jikinsa ya bata kyakkyawar rumguma ,fasa ihu tai a tsorace ta cukwikwiye Farouk da kyau ,Farouk wani irin kallo yakewa haydar daya d'auke ido daga kansu fuska tamke ya fice,  hanna ta d'ago tace "yaya Farouk kaga muguntar da yayimin ko"   d'an murmushi ya saki yace "kema fa naji rashin kunyar da kikaimai"  hanna ta saki baki tana sai kuma ta fara kukan shagwab'a, tuni ya rikice mata a sanyaye yace "srry my angel kinji "  ta turo baki tace "ni dai mun 6ata dakai tunda kaima kabi bayansa"  Farouk ya marairaice mata a hankali yace "to nacefa kiyi hkr sai biyu kenan kinji angle d'ina" ya langwa6ar da wuya, fannah tuni ta fice nunawa mum dinta wayar,
  Mak'e kafad'a tai ta juya masa baya,Farouk ya zubawa bayanta ido a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'esu ya juyo inda take yace "to jeki shirya na kaiku shopping ki za6i abinda kikeso"  sai sannan ta saki fuska kad'an tace "tom bari nazo" tana gama fad'a ta fice ya bita da kallo yana sakin ajiyar zuciya d'an murmushi yayi ya juya aya fice daga parlour,mamii ta fara kaiwa ta gani mamii tace "inyee Daughter angode daddy"  hanna tace "to mamii saura kefa"  mamii tace "ai Kijira zakiga nawa"  murmushi tai ta fice zuwa part d'insu,aunty ta nunawa tai godiya sannan bassam ya saita mata komai, cikin kankanin lokaci hanna ta samu admission a Yusuf mai tama sule university (northwest kano)  wato inda basma take fannah kuma bata samu admission anan ba sai aka nemar mata  buk, sabuwar mota abbansu ya sai musu itada basma sai tsohuwar aka barwa fannah ita,
  Tsadaddun kaya da set d'in hijab mamii taiwa hanna kusan kala 10 sannan taiwa fannah kala 5 na ,Farouk kuwa shopping ya kaisu kamar yadda yayi alkwari kayan make up  da turaruka sosai suka hado dan hanna akwai son kwalliya ,
  Rik'e da kayan da sukai shopping ta shigo ta ajiye a tsakiyar parloun ta zame mayafin data nad'a akan doguwar rigarta zama tai  ta mike kafafunta tana yatsina fuska ,bassam da yake zaune yana danna laptop ya saki dariya yace "autar aunty yar jami,a "  murmushi ta saki ta koma kusa dashi tana kallan yadda yake operating loptop d'in tace "ya bassam wai tsonakata kake"  aunty da fitowar ta kenan daga kitchen  tace "ba dole a tsokaneki ba hanna kinbi kin wani firgice kin kasa zama waje d'aya sbd zaki shiga jami,i"  langwa6ar dakai tai tace "kai aunty haddake, nifa kawai shirye shirye nake kar naje a rainani"  bassam baisan sanda ya fashe da dariya ba yace "lallai parrot zakisan shirye shirye kike, daga randa kanki ya fara d'aukar zafi zaki mance ya ake shirye shirye"  ta zaro manyan idanunta tana kallansa atsorace "ya bassam" ganin yadda ta tsorata sayashi yin wata dariyar yace "ke bafa wani abun bane "  kwa6e fuska tai tace "ALLAH nidai ka gayamin"  ya daina dariyar ya had'e rai yace "nace miki ba komai"  tashi tai a sanyaye ta wuce d'akinsu ta baje shopping d'in da sukai tuni ta manta da wani tsoro sai sakin murmushi take tana shiwa Farouk albarka.
   Suna zaune daki ranar lahadi aunty ta shigo ta zauna Kan Stoll cikin nutsuwa ta kalli hanna tace "gobe zaki fara zuwa makaranta ko?"  Hanna ta gyara zama ganin yadda auntyn tai magana tasan maganace ta mai muhimmanci tace "eh"  aunty tace "to madallah ,abinda nakeso dake hanna ki kama mutuncin kanki,banasan ki ringa mu,amala da ko wace kawa nasanki da rawar kai da nuna kowa nakine ita jami,a kowa ya iya allansa ya wankene,makarantace data had'a mutanen kirki da mutanen banza bance karki kawance da kowaba amma ki zauna ki nutsu kiga yanayin kowa sannan kisan irin zaman da zaki dasu,ba ruwanki da abota da maza ban amince miki ki ringa mu,amala dasu ba indai ba harkar karatu ce ta had'a kuba,dan ALLAH hanna karki canza daga tarbiyyar da muka baki ki bari kawa ta 6ata miki ita,kiji tsoron ALLAH ki kame mutuncin kanki ke macece ki kame kanki karki shiga hakkin kowa kuma ki rage wannan rashin kunyar taki ALLAH ya baku sa,a yasa " 
   A sanyaye hanna ta amsa tace "insha ALLAH na miki alkwari aunty zan kiyaye duk abinda kika fad'amin"  aunty tace "ALLAH yasa " Kallan basma tai tace "ke kuma ki ringa kula da ita da kuma nusar da ita abinda bata saniba dangane da makarantar"  basma tace  "insha ALLAH "  fita tai ta basu waje suka cigaba da abinda suke,
  Da dare abba yana zaune a parlounsa hanna da basma suna kan carpet aunty tana zaune kusa dashi tasha simple make up sai kamshi take bakace ita ta haifesu ba, bassam ne yayi sallama ya shigo kansa a kasa ya zauna ya gaida abba da aunty,nasiha sosai abba yayi musu sannan yace "gobe drivernku zaizo sbd haka saiku maida hankali akan karatunku "  basma tace "abba nafa iya jan mota"  aunty ta kalleta da sauri ,abba yace "yaushe kika koya"  tace "ina ganifa in ana driving kuma zan iya"  hanna ta saki dariya tace "ALLAH yaya basma bazan hau motar da zakijaba kawai kije ki kayar damu" hararta basma tai abba yace "ya isa za,a ware lokaci driver ya ringa koya muku in kuka kware sai ku fara ja ku kadai"  aunty dai batace komai ba harya sallamesu suka fita.

HannahWhere stories live. Discover now