Hannah part 31

445 53 15
                                    

💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
        3️⃣1️⃣

*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*
*Whattpad@OumRamadan1*

*Haydar yace baisan haka yake da dumbin masoya da magoya ba,yace yana Miko sakon godiya Lodi Lodi tunba Yan Group d'in Hanna fans Group 1&2 ba da sauran Groups da suke support d'insa,duk dani dai wannan had'in ya kaini bango danni ta hannun damar mk ce gsky Kuma munanan zamu d'au matakin daya dace*🤪😝☹️

"Idan ka kukusara kai wani abu na rashin hankali ka kunyatani a gaban jama,ata wlhy saina fito maka da asalin fushin da nakeyi dakai,Kuma idan ka kukusara kai wani furuci akan aurannan wlhy saidai ka nemi wani uban bani ba mustapha "
  Senate yace dashi cikin kakkausar  murya inka gansu zaka d'auka tamkar wata magana yake masa mai muhimmanci ,mutuwar zaune mk yay wani irin duhu da juya ya ringaji yana hajijiya dashi yana zaune kallan kowa yake musamnan liman da yake aikawa mugun kallo, idanunsa sun kad'a lokaci d'aya sunyi wani irin ja ,jijiyoyin kansa sun tashi rudu rudu yanajin wani irin tashin hankalin dabai ta6a riskarsaba zuciyarsa ce yaji tana wani irin suya ga Kuma wani bakin kishi daya turnuke ransa,
  Baisan sanda ya mikeba tsintar kansa kawai yay yana tafiya yanaji abokansa na masa magana bai kula da suba tun a kofar masallacin ya cire hular kansa da da babbar rigar yay wurgi dasu a mugun fusace ya shige motar da suka zo da ita ya tadata da karfin tsiya ya wuce ,
  Dama tunda haydar yaji an d'aura ya juya ya kalli gabas yay sujjada ,lumshe ido yay yanajin wata kwallar farin ciki tana niyyar zubowa ba Wanda yabi takan mk dan tuni lokacin wajen ya gauraye da hayaniya anata gaisawa da yan uwa da abokan arziki , farouk sai kallan haydar da bakinsa yaki rufuwa yake yana dariya shima ya Kai masa duka yace " mun gama rigimar Kai Kuma Kai wuf da ita ko?" Wani murmushi ya saki Sameer yace "Dan iska ba ,dama kallan mu yake shima sonta yake ya tsaya girman kai ," dage gira haydar yay cikin salon rainin hankali yace "toh ya ranku guy's?"
  "Wlhy fari tass dan iska" farouk yace yana d'aga hannu sama a tare suka fashe da dariya abokansu na tayasu daga nan hotel suka nufa inda angwayen suka shirya kwarya kwaryar walima,
  Cikin gida kuwa anata hada hada kowa ka gani fuskarsa kunshe da fara,a ,tun sanda mami taji an d'aura auran ta rumgume hanna tana hawayen farin ciki, itama hanna kukan ta fashe dashi duk da har yanzu batasan da Wanda aka d'aura aure ba , ba karamin burge mutanan wajen sukai ba dan tuni sukasan dawa aka d'aura auran hanna ce kawai bata saniba ganin kukan bana karewa bane aka shiga rarrashinsu mamice ta fara zare hanna daga jikinta tana share mata hawaye ,itama hannu tasa tana sharewa mamin , murmushi take Allah ne kad'ai yasan irin kaunar da takewa hanna a haka angwaye suka shigo haydar ne ya tako har gaban su mami ya zauna a tsakiyarsu suka jeru waje guda , had'e hannayesu Mami tai wasu sababbin hawayen farin ciki suna zubo mata a hankali ya had'asu waje guda ya rumgume su yana maida kwallar da take zuwar masa hoto aka shiga d'aukarsu masu vedio nayi masu dariya da guda nayi,
  Hannun haydar mami ta kama ta had'a dana hanna waje guda dukansu Saida sukaji wani yanayi a jikinsu yayinda haydar ya lumshe ido daga safiya zuwa yau baison yawan tasbihin da yayba ,
  Hanna kuwa sai bin mami take da ido cike da rashin gane inda ta dosa , kallan haydar mami tai tace "dazu ka tambayeni me zakaimin dazan dawwama cikin farin ciki ko?" Gyad'a kai yay yana murmushi mami tace "ka rikemin yarinyata da amana da gaskiya karka cuceta haydar,karka wulakantamin 'yata ka maidata mace Yar gatan miji banaso tai kukan rashin miji ka sauke duk wasu hakkokin dake kanka ka kulamin da ita ka sata farin ciki kayi hakuri ,ka Zama me hakuri da ita a ko wane hali"
  Da iya gaskiyarsa ya damke hannun hanna da karfi har saida ta d'an saki Yar Kara ya janyota jikinsa ya zauna dirshan a gaban mami hanna sai mutsu mutsu take cike da tashin hankali muryar haydar taji yana magana da wani irin tone yace "na Miki alkawari mami insha Allah zaki sameni me cika alkwari zan kasance me biyayya ga abinda kika umarceni mami" ya k'arashe yana kissing d'in hannun hanna idanunsa a kanta,
Hotuna kawai abokan haydar suke d'auka wasu Kuma vedio matan kuwa sai sakin guda suke masu lika musu kudi nayi dan ba karamin burge mutane sukai ba ,fizge jikinta hanna tai ta wuce upstairs da gudu tana wani irin kuka , a d'akin ta zube ta dinga rusa kuka basma ta biyota da sauri tace "hanna kukan me kike?" Ta dakatar da kukan da takeyi tace "ni bangane duk wasu abubuwan da suke faruwa ba ya basma kaina ya kulle zuciyata tsinkewa take bangane maganganun da mami takeba na kasa fuskantar komai" shiru basma tai tana tunanin ya kamata ta sanar da Yar uwarta abinda ke faruwa duk da dama tasan yau za,a sanar mata amma ya zama dole ta fitar da ita daga kokwanton da take numfashi basma ta sauke a hankali tace "kanwata" ta d'ago da idanunta da sukai ja ta kalleta batace komai ba basma tace "hakikanin gsky bada mk aka d'aura miki aure ba" mikewa tai cikin tashin hankali bakinta na rawa tace "bangane ba ya basma ,me kike nufi?"
  Rik'o hanunta tai cikin sigar lallashi da kwantar da murya tace "ki zauna ki nutsu ki saurareni zan fad'a miki  duk abinda ya ya faru" kasa zama tai sai basma ce ta zaunar da ita a hankali ta fad'a mata abinda ya faru da dalilin da yasa aka fasa auranta da mk aka maida kan haydar ta d'ora da cewa "inaso ki fahimci ba karamin gata iyayenmu sukai miki damu baki d'ayaba ,ki cire wannan mayaudarin daga ranki ki manta kin ta6a saninsa ki fuskanci rayuwarki ta gaba kiyiwa mijinki biyayya ki cire komai a ranki karkisa damuwa tazo ta haifar miki da  wata matsala ,kamar yadda mukai biyayya muka kar6i za6in iyayenmu hannu biyu kema inaso ki biyayya kisa a ranki haka Allah ya rubuto mana,kina kallo nida fannah kiranmu akai akace an badamu bamuyi musu ko tashin hankali ba muka amince sbd iyayenmu bazasu ta6a mana za6en da bazai zamar mana alheri ba kuma insha Allah zamuga ribar biyayya" ita dai hanna Banda hawaye ba abunda take numfashinta har wani sama yake tsabar 6acin rai da tsanar mk datake nema ta danne soyayyar da take masa, wata muguwar tsanarsa taji a ranta da haushinsa, ta bud'e baki zatai magana Mami ta shigo mikewa basma tai fice zama tai kusa da hanna ta rik'o hanunta cikin sanyin murya tace"daughter"  kanta na k'asa ta amsa da shakakkiyar murya,"d'ago ki kalleni" Mami ta sake ce mata cikin taushin murya ,dakyar ta d'ago da kanta ta kalleta ,ha6arta mami ta kamo tana kallan idanunta tace "daughter ki fad'amin gsky bakyason dan uwanki? " Rintse ido tai cike da jin haushin kanta ita wace irin mutum ce da zata kalli jinin mami tace bata sonshi,ko takalmi mami takeso tana sonshi barantana jininta danta da tafi so a rayuwa, "karji kunya daughter ki fad'amin inhar bakya ra,ayin wannan auran saina sa an warw,,," rufe mata baki tai tana girgiza kai juyawa tai ta shagwa6e murya tace "Toni nace miki banaso" murmushin jin dad'i mami ta saki ta leko kanta tace "da gaske kinaso?" Boye fuskarta ta sakeyi ta gyad'a kai rumgumeta mami tai cikin tsananin farin ciki tace "Allah yay Miki albarka daughter, Allah ya albarki auranku ya baku zuri,a " can kasan zuciyarta ta amsa tana share hawayen da suka zubo mata,
  Kamata mami tai ita da basma ta wuce dasu part d'in aunty dama directly parlourn abbansu ta nufa ta kirawo aunty tace "toh Maryam gasunan na kawosu kiyi musu fad'a kinsan anjima ba wani isashshen lokacin da zaki ke6e dasu" aunty ta had'e rai tace "haba mami,danasan kiran da kikaimin kenan da bazan zoba wane fad'a zan musu Wanda baki musu ba ?"
  "Duk da haka dai Maryam a matsayinki na mahaifiyarsu kina bukatar ke6ewa da su "
Juyawa aunty tai tace "kema mahaifiyarsu ce mami dani dake duk d'ayane abu d'ayane a wajensu, abinda zan musu kin musu to me zance 'ya'yankine duk abinda kikai daidaine" daga haka ta fice tana goge hawayen da suka zubo mata tana jin rad'adin rabuwa da yaranta lokaci d'aya,saidai farin cikin da take ciki na aurar dasu ya shafe mata komai koba komai tasan irin mazajen da suka aura hankalinta a kwance yake tana Kuma binsu da addu,ar Allah ya zaunar mata dasu lfy a gidajen mazajensu .

*#HH*
*#Hanna_Haydar*
*#Oum Ramadan*
*#oneluv*

Kar a manta da vote da following 😘

HannahWhere stories live. Discover now