Hannah part 37

453 44 12
                                    

💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
        3️⃣7️⃣

*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*




Mami ce ta bud'e k'ofar tana kallan hajiya binta da d'an murmushi ta bata hanya ta shige,gwiwa a sanyaye tasa kai cikin parlourn kujera mami ta nuna mata bata zauna ba saida ta kawo mata ruwa da juice akan tray ,
  Hajiya binta batasha komai ba sai tagumi data zabga a sanyaye suka gaisa hajiya binta tace "nasan baki sanni bako?" Mami  tace "eh" numfashi ta sauke tana kallan mami ta rasa tayaya zatai mata bayani tuno halin da tabar siyama yasa ta bud'e baki dakyar tai mata bayanin halin da siyama take ciki, fuskar mami cike da tausayi tai mata yame jiki sai dai jin bayanin daya biyo bayane yasa mami ta saki baki tana kallan ikon Allah,
  Wani irin kallon ta6a6u takewa hajiya binta kafin ta girgiza kai tana murmushin takaici tace " wace irin uwace ke da baki koyawa yarki yadda da kaddara ba ,anya kuwa kinyi tunani kafin kizo Nan? Yaron da ko 1week baiyi da aureba kizo da wani irin magana ta wata maganar auran? Toh nidai ko a tarihi banta6ajin Wanda yay aure kwana 3 aka fara wani zancan auran ba ," hajiya binta taji wata muguwar kunya ta kamata bata ta6a tunanin bai dad'e da aure ba da tasan hakane bazatai gaggawar zuwa ba , fuska d'aure mami tace "toh yarinyar da d'ana yake aure 'yatace Rabin rayuwarta a wajena tayita ,akwai saurayin da take bala,in so wanda kwana 3 saura biki aka fasa aka d'aura mata aure da yarona ba tare da sanintaba kinsan ko sbd me yasa?" Hajiya binta dai ta kasa magana mami ta cigaba da cewa "sbd mun isa da ita munsan bazata bamu kunyaba ,ki auna tunaninki da fahimtarki ya mutum zaiji a rabashi da Wanda yakeso rana tsaka a maye masa gurbi da wani, wlhy tallahi hajiya ko haydarne yazomin da wannan maganar saina nuna masa asalin fushina ni bazan hanashi abinda Allah ya halattaba amma bazan ta6a amincewa ya jajubo wani aure nan kusaba bai isaba ki koyawa yarki yadda da kaddara tasan ba komai ake nema a samu a rayuwa ba yakamata ta koyi hkr da dangana a rayuwarta Allah ya bata lfy na kuma gode da soyayyar da takewa d'ana amma tayi hkr aure bazai ta6a yuwuba gsky" daga haka mami ta wuce cike da takaicin son rai da zuciya irin na wasu mutanan kwafa ta saki tana jiran zuwan haydar taji inshi ya turo azo a mata wannan zancan,
   Dakyar hajiya binta ta mik'e duk duniya sai taji ta muzanta kana kallan fuskarta zaka hango zallar 6acin rai motarta ta shiga ta tayar, kai tsaye room d'in da aka kwantar da siyama ta nufa tana shiga d'akin ta kalli siyama dake zaune bata kula da mutanan dake d'akinba tace "wlhy tallahi siyama bada yawuna  ba kika kuma kula wannan yaron koshi kad'aine namiji a duniya insha Allah kin barshi har abada idan Kuma kika nace toh saidai ki za6a koni koshi" daga haka ta fice cikin tsananin takaici da 6acin rai,
A cikin kwana biyar hanna ta fara sakin jiki da haydar duk kallan da take masa ada sai taga ba haka yake ba , komai tare suke suci abinci tare aikin gida tare suke wanke wanke ya maidata tamkar kawarsa wanka ma tun tana kunya harta d'an fara sakewa duk da bata wani sakin jiki sosai haka ake wankan tana mak'ale a jikinsa bacci kuwa ta riga ta saba inba a jikinsaba bata iyawa dama gata da son jiki,
   Haydar kuwa ba karamar dauriya yake ba a yan kwanakinnan dakyar yake samu yay bacci izuwa yanzu hakurinsa nema yake ya k'ure dama so yake ta gama sakin jiki dashi a yanzu ji yake bazai iya cigaba dasa mata ido yana kallanta tana giftawa ta gabansa ba , numfashi ya fesar yana kallanta ta k'asan ido ,
 

*Duk yadda naso na karasa muku  page dinnan kasawa nai wlhy yau kwana 2ina kokarin in muku banida lfy ayi hkr da wannan insha Allah innaji sauki zaku ganni a Koda yaushe ngd da addu,o,inku a kara tayani da addu,a*🤲🏼

HannahWhere stories live. Discover now