Hannah part 7

414 31 0
                                    

💥 *Hannah* 💥

        0️⃣7️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramada)*
Whattpad@oumramadan1

Tahowarta kenan daga part d'insu tana sanye da gown ash clour da adon red ta yane kanta da veil na rigar sosai tai wani mugun kyau jikinta yana fidda sanssanyan kamshin da saika kusantota zakaji,part d'in mamii ta nufa da zata rakata unguwa cikin shiri ta samu mamii da wani dakakken lace me kyau kana ganin shigarta kasan ta manyan matane,
  Kallanta mamii tai tace "masha ALLAH Daughter kinyi kyau "  lumshe ido tai tace "thank mamii "  mamii tace "jeki kiramin yayanku a sama " turo baki tai ta hau upstairs, kwankwasa d'akin tai ta kusa minti 3 sannan yace bata izinin shiga,
  Tsaye ta samesa yana d'aura agogo farar shaddace kall a jikinsa sai shek'i take jikinsa sai fidda wani irin kamshi yake ,turo baki tai tace "mamii tana kiranka"  baice komai ba ya d'au wayarsa ya wuce ta gefenta ta6e baki tai ta harari bayansa  tabi bayansa tana murgud'a baki,
  Tun daga k'asa mamii take kallansu ta saki ajiyar zuciya sanda suka k'araso ta kalli haydar tace "mu wuce ko"
  Fita yayi yana karkad'a key har suka k'arasa parking space.
  Mami ta bud'e back seat ta shiga hanna tana niyyar shiga ya katseta cikin had'e fuska yace "na miki kama da driver?"  Turo baki tai ta bude gaba ta shiga mamii ta tabe baki tana d'an murmushi har suka k'arasa g,r,a, fitowa sukai a tare banda haydar daya gyara zama mamii tace "Bazaka fito kayiwa haj rukayyan sannu ba? "  fitowa yayi yana shafa kansa a hankali ya gallawa hanna harara da take dariya k'asa k'asa,
  Kayataccen parloun haj rukayya suka shiga kwance suka sameta akan kujera tad'an kashingid'a gabanta wani kyakkyawan table ne dake shak'e da kayan kwalama irin na marasa lafiya, tana ganinsu ta saki murmushi tana musu lale, bayan sun zauna mamii tace "ya jikin haj rukayya, kin gammu sai yau nima fama nai da nawa jikin amma yanzu Alhmdllh "
  Haj rukayya tace "da sauki haj rabi ALLAH ya kara mana lfy "  hanna tad'an rusuna cike da ladabi tace "ina wuni hajiya ,ya jikin"  tana kallanta tace "lfy lau yammata ya karatu"  amsawa tai a hankali ,haydar ya harerata yana tamke fuska ya gaida haj rukayya, tace "masha ALLAH haydar ya aikin"  a takaice yace "Alhmdllh "  fita yayi ya koma mota ya zauna duk da haj rukayya taso yaci abincin da har aikinta ta kawo musu,  hira suka d'an ta6a kad'an sannan mamii tai mata sallama kayan kwalliya masu kyau da tsada haj ta had'awa hanna mamii tai mata godiya sosai,
  A hanyarsu ta dawowa ana zuwa  daidai wani eatery hanna ta kalli mamii ta shagwab'e fuska tace "mamii pls yunwa nakeji"  mamii tace "shine dan sakarci kikak'i ci gidan haj ,ki bari in mukaje gida kyaci" ta marairaice murya tace "kunyafa nakeji mamii dan ALLAH a tsaya anan a siyamin burger kinji" 
  Haydar yanajin haka ya k'arawa motar wani mugun gudu,mamii ta saki murmushi tace "kabi damu a hankali malam" ta kalli hanna ta dake turo bakinta sai kunkuni take dan tasan da gayya yayi mata haka kuma tana sane dashi duk abinda yamata saita rama,
  A fusace ta fice daga motar tayi part d'insu mamii tabita da kallo tana dariya tabi bayanta a hankali,
  Zaune ta sameta akan carpet tana kuka aunty sai fad'a take mata rai 6ace tace "ke karamar yarinyace da ba abunda kika iya saiki sani agaba kinamin kukan shagwab'a ki ringa d'agamin hankali ,dan ubanki shi yayan naku bawankine dazai tsaya sai miki wata burger bakida aiki sai a siyo miki burger keba had'a jini kikai da larabawa ba,uban wa ya hanaki cin abincin iyee"  tana ganin mamii ta fad'a jikinta,mami tace "haba maryam meye haka zakisa yarinya a gaba da fad'a kamar zaki daketa, yunwafa takeji"  aunty takaici ya hanata cewa komai ,basma dake tsaye a k'ofat bedroom tun shigowar hanna tai dariya ta koma daki, mamii ta kalli hanna tace "tashi muje ,dole ko baiso ya siyo miki share hawayen"  aunty tana kallansu suka fice ta ta6e baki cike da takaici,
   Leemat tana tsaye a k'ofar office d'in haydar rik'e da mug d'in coffee sai sakin murmushi take ta tabbata yau insha ALLAH zata cika burinta pill ta zuba masa ta juya ido ta murda handle d'in kofar kasa kasa tai sallama ta tabe baki tana lashe busassun lips d'inta ajiye masa tai a table tad'an rusuna ta yanda karjinta zai fito tace "sir ga coffee "  bai kalleta ba yad'au ka a hankali yake sipping d'insa time 2 time yana duba file ,leemat tana tsaye cike da kaguwa ta kasa fita daga office d'in,
  Karar da wayarsa taine yasashi d'aga kai ya watsa mata wani kallo data duburburce ta nemi nutsuwarta ta rasa idanunsa kad'ai ta kalla sai taji fitinannen feeling ya taso mata ,batare daya sake kallan inda takeba ya kara wayar,jitai kawai yace "ok ganinan"
  Yana gama fad'a ya ajiye mug d'in yayi hanyar fita yana cewa "ki kullemin inkin fita"
  Zaman da6aro leemat tai ta rushe da kukan takaici kusan awa ta d'auka tana kuka ta mike ido jajur ta rufe office d'in, direct gidan saurayinta ta wuce ta rage zafi dan sosai ta kimtsa jikinta yaud'in ta yadda idan haydar ya kwanta da ita zaiji mararin k'ara nemanta,takaicinta uban kudin da ta kashe ta gyara jikinta duk dan haydar din,
  Shi kuwa tun a mota ya farajin mararsa na d'an murd'awa haka ya daure yake driving har ya karasa park d'in da siyama take ,
   A kasalance yake tafiya kamar mara laka can ya hangota zaune tasha kwalliya ta burgewa, inda take ya nufa ya zauna a nutse kamshin da ke tashi a jikinta ya kara saukar masa da wani azababben feeling lokaci d'aya ya taune lips ďinsa da karfi ya zubawa siyama ido da take sakar masa murmushi a hankali,
Ya runtse ido da karfi kafin ya budesu fess akanta siyama ta zaro ido cikin tsoro take kallan idanunsa da sukai wani irin jajur dasu hankalin tashe tace "bakada lfy haydar?" Lumshe idanun yayi da suka fara kankancewa saboda fitina bai yarda ya kalletaba ya mike yana had'a hanya ya nufi inda yayi parking d'in motarsa ,
  Handbag d'inta ta dauka ta bisa cikin tashin hankali harta fara hawaye sbd tsananin tausayinsa daya kamata tana zuwa yanajan motar da wani irin gudu dayasata sulalewa a wajen ta fasa kuka tana kiransa sai kuma ta mike ta shiga motarta tabi bayansa itama da mugun gudu.
  Duk yadda taso ta gano motar haydar kasawa tai hankalinta yayi mugu mugun tashi ba kad'an ba batasan a wane hali yakeba tambayar da taiwa kanta dama bashida lfy yazo? Me hakan yake nufi kenan? Kodai ta fara samun matsayi a wajen haydar ne?  In kuwa hakane zatafi kowa farin ciki  lokaci daya ta saki dariya da hawaye, jikinta ya d'anyi sanyi da tuno halin daya tafi ya barta a sanyaye taje motarta ta wuce gidansu,
  Ikon ALLAH ne kad'ai yakai haydar gida yana d'an rik'e gefen cikinsa ya shiga parloun nasu mamii tana kitchen sai hanna da take karatu dan jarabawarsu ta matso,
   Zaro ido hanna tai tana ganin haydar yana tafiya yana had'a hanya ,da karfi tace "yaya bakada lfy"  mamii ta leko da sauri tanabin haydar da kallo da yake haura stairs a wani irin yanayi yana shiga ya murzawa d'akin key ya bude frigde da sauri ya ciro lime yasha sosai ruff da ciki yayi yanajin kamar mararsa zata fashe,
  Hanna ta kalli mamii cike da damuwa tace "mamii wlhy bashida lfy bakiga yadda yashigoba" mamii tai tsaye rike da ludayi a hannunta damuwa fall a fuskarta ta girgiza kai ta wuce upstairs d'in da sauri.

#Vote
#commt
#share
#oumramadan❤️

HannahWhere stories live. Discover now