Hannah part 14

398 38 6
                                    

💥 *Hannah* 💥

        1️⃣4️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Barr Mk ranar gaba d'aya rasa nutsuwarsa yayi daya tuno surar hanna duk daba wani tsaraici ta fitar ba sai yaji wani irin bakon yanayi da bai tabajiba akan mace,
  Yasan yakanji Sha,awar mace saidai wannan Sha,awar ta bambamta da wadda ya sabaji ,kwanciya yayi akan gadonsa Yana sake sake da haka bacci me ciki da mafarkin hanna ya d'auke shi.
  Da yake yau week end duka family suna gida, Hanna da fannah suna zaune a compound d'in gidan kan wasu fararen kujeru Hira suke Sai kyalkyale dariya suke ,motace ta shigo compound d'in ta wuce parking space a hankali aka zuge bakin glass din motar,
  Mikewa hanna da fannah sukai da mugun mamaki har rige rigen Kiran sunansa suke "ya Samir" bude murfin motar yayi ya fito yana murmushi yace "hiii angle," da gudu suka rumgumeshi suna dariya ya kalli fanna ya lakuce mata hanci yace "lukuta ya naga kin rame" ta 6ata fuska tace "nidai banaso ya Sam" dariya yayi ya kalli Hanna yace "angle kaimin jakata part din mamii kafin a gyara min waccan ,zan shiga na ajiye Kaya"
Jakar ta d'auka shida fanna sukai hanyar da yake part d'insu Yana kusa dana juna,
  Tana shiga parlourn mamii taji saukar wani gigitaccen mari daya kusa sumar da ita, jakar ta saki ta kurma wani uban ihu,
  Mamii data mike a tsorace take kallan haydar bude baki zatai magana mamaki ya hanata,fizgo hanna yayi da take kuka kamar ranta ya nunata da yatsa yace
  "Zan Miki last warning tunda ke mahaukaciya billahillazi na sake ganin kin rumgume wani ko a gidannan saina karya Miki banzayen kafafunki masu kamada rake " yana gama fad'a ya tureta ta fad'i a fusace ya  juya ,
  Da kallo mamii ta bishi da mugun mamaki kafin ta tallafo ta jikinta ta rasa abinda zatace can tace "me kikaiwa yayanku?"
  Cikin sheshsheka tace "  ya Sam ne fa yazo Kuma nida fannah mukaimai sannu da zuwa ya bani jakar sa yace na kawo Masa Nan kawai Ina shigowa ya mareni" ta karashe tana fashewa da sabon kuka,
  Shiru mamii tai kafin ta jata bedroom d'inta paracetamol ta bata tasha ta kwantar da ita kan gado ta sai da taga ta Fara bacci kafin ta sauke ajiyar zuciya fitowa tai ta shiga d'akin haydar,
  Zaune ta sameta har yanzu d alamun fushi a fuskarsa idanunsa har yanzu basu dawo daidai ba, Zama mamii tai bayan ta d'aure fuska ta kirashi a nutse, d'ago da kansa yayi Yana kallan mamii a nutse tace "me hanna taima Kai mata wannan Marin?"
  "Mamii yarinyar Nan batajin magana kwata kwata kamar hanna ce zataje ta ringa rumgumar wasu "
  Mamii tace "wasu kuma?banason shashanci ka fad'amin abunda ya faru"
  "Wasu Mana mamii tunda duk ciki ba muharraminta,rannan fa Ina kallanta ta rumgume farouk yau Kuma ta rumgume Samir mamii yarinyar Nan fa ba karama bace" ya karashe kamar zai kuka, tsura masa ido mamii tai tace "to naji amma meya hana Kai hada Kai musu hukuncin ita d fannah" Shiru yayi can yace "itama zan kamatane "
Mikewa Mami tai Babu alamar wasa tace "Aliyu " da mamaki ya d'ago da kansa kafin yaji mamii ta Kira sunansa ana dadewa "ka fad'amin son HANNA kake?" Da Wani irin mamaki yake kallan mamii kafin ya fashe da dariya yace"amma mamii wasa kike ko"  harara ta gallara Masa tace "kaniyarka nifa na haifa haydar ,kishin hanna na gani a idanunka ka fad'amin in sonta kake zanfi kowa farin ciki"
  Kusa da mamii ka koma ya kamo hannunta yace "mamii kaf cikin yaran gidannan nafison hanna kinsan ko sbd me? Sbd kema kinfi sonta ni Kuma inason abinda kikeso mamii,inawa hanna so irin na Yaya da kanwa ba irin sonda kike nufi ba"
  Numfashi mamii ta sauke kwata kwata bata gamsu da abinda ya fad'a tace "to naji amma wannan ya zama na karshe da zaka ringa kai jiki kan yata bance karkai mata hukuncin ba ,banaso ka saba da dukan mace kadaiji abinda na fad'a ma"
"Toh mamii"
Juyawa tai ta fice bata sake cewa komai ba, kwanciya yayi ya rufe ido yana tunanin maganar da mamii tai masa inya tuno saiya fashe da dariya,daga karshe mikewa yayi ya shige toilet ya sakarwa da kansa shower,
Cikin kananun kaya bakake ya sakko da sukai masa kyau sosai sai uban kamshi yake , a parlour ya tadda mamii tana feeding d'in hanna ita Kuma sai zuba shagwa6a take ,ta6e baki yayi ya wuce dinning kai tsaye ya zuba abinci yanaci,
Da dare shopping Samir ya kwashi Hanna da fannah sai basma ,duk da hanna kanta yana d'an mata ciwo haka suka shirya dukansu cikin shigar dogayen riguna , shopping yay musu sosai sannan suka dawo gida a parking space suka had'u da farouk hannunsa rike da mukullin mota ,
Tafawa sukai da sam yace "dude yaushe a gari" 
Sam yana murmushi yace "wlhy dazu nazo engineer kana lfy" idansa nakan hanna yace "lfy Lau zuwa ba sanarwa"
"Surprise nazo yiwa angle sbd na kwana 2 bangantaba"  da sauri farouk yayi gaba yace "dude zamu had'e anjima Ina zuwa" baibi takan gaisuwar da suke Masa ba yay wucewarsa cikin mota ya tayar ,da kallo hanna tabi motar tana juyowa sukai 4 eyes da sam,murmushi ya sakar mata ta kakaro nata hannu ta d'aga Masa ta wuce part d'insu.

Pls a tayani da addu,a banida lfy

HannahWhere stories live. Discover now