Hanna 50

242 18 0
                                    

*HANNA*.......💥

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

   *50*
*THE END*

Karfe  8:30 na safe haydar ya sakko hannunsa rike da briefcase, dayan hannun kuma yana rike da hanna  ya zagaye cikin , a nutse suke  sakkowa bata  yarda  ta barshiba saida  ta rakasa har bakin kofa ta dawo ,
  Dakyar ta zauna tana yamutsa fuska , dan  tun  da asuba mararta ke  murda mata d'aurewa kawai take sbd kar hankalin haydar ya tashi ,
   Baba mairo ce  ta fito daga dakinta da aka sauketa ta zauna kan carpet cikin nazarin  hanna  tace "Uwar dakina lfy kike  kuwa? " Hanna ta sake yamutsa fuska tace "wllhy baba marata ke  ciwo , amma ba wani abu bane dama na saba" baba ta girgiza kai tace "aa yar nan gwara muje asibiti a dubaki , gani  nake  kamar haihuwace"
  Hanna tai wata dariya kana ganin dariyar kasan ta karfin halice tace" ba komai fa baba, kuma edd dinama bai cikaba " badan  baba tasoba ta kyaleta saidai tana hankalce da duk wani motsinta ,
   Tun  Hanna na daure ciwo harta fara salallami sbd jin ciwon take yana gaba, durkushewa kasa  tai sbd  jin kugunta yay wani irin  sarawa kamar zai balle  , baba dama tun dazu ta kira mami da wayarta ,  kusan minti  30 mami da aunty suka iso lokacin tuni Hanna ta had'a Uwar zufa sai yarfe hannu take ,
   A rikice mami ta kamota , tana ganinsu ta bude baki zata fara kuka  aunty ta girgiza mata kai cike da tausayinta , aunty CE ta tuka  motar  mami da Hanna suna baya akabar baba mairo a gida,
  Suna zuwa akai labour room da ita  , haydar kuwa tunda ya isa  office yakira Hanna as usual,  saida yay mata few miss called bata  dagaba , tuni hankalinsa ya tashi ya kira baba mairo , baba mairo ta sanar masa tuni an wuce da Hanna asibiti bai jira  ta karasaba ya d'au mukullin motarsa ya wuce da sauri  ,
   Zaman jugum jugum akai a asibitin dan  har sannan Hanna bata haihuwaba sai salati take , haydar yana bakin kofar idanunsa sun kad'a sunyi jajur , kana kallansa zakasan ba,a nutsuwarsa yake ba , abinci kuwa ba wanda  ya kalla baran tana yabi ta Kansa,
  Kimanin awa  5 Hanna ta d'auka tana labour kafin Allah ya sauketa lfy ta haifi sunkuceciyar babynta dake  kama da babanta sak, sai hasken mamanta data dakko, tunda haydar ya rike Babyn bai saketaba sai kallanta yake yana zuba murmushi , dakyar Farouk ya karbi Babyn yana nunawa basma ita ,
  Tuni haihuwar ta zaga family , da yake daga ita  har babyn lfy suke awa biyu suka k'ara akai discharged dinsu, direct gida aka wuce  , tuni mami ta sille katuwar jajiriyar baba mairo ta gasawa hanna  jiki  da ruwan zafi ,
   Haka yan uwa da abokan arziki suka dinga tururuwa zuwa barka , a haka har ranar suna ta zagayo inda  baby taci sunan mami za,a ringa  kiranta da *hanan*,
  Mejego Hanna da babynta hanan da uban gayyar haydar sunyi mugun kyau na fitar hankali, kudi sosai haydar ya fitar yaywa baby hanan da Hanna siyayya  sosai ,
Haka mami ba karamin kudi ta kashewa Hanna da takwarartaba , aunty da bassam mus,ab  farouk da basma ba ko wanne ya taka rawar gani,
  Daddy ko kyautar wani dankareran gida yaywa sabuwar amaryarsa kuma jika ta farko a wajensa , mutan Lagos ma sunzo suma sosai suka taka rawar gani abindai sai sam barka ,
  A gurguje hilis😎
3yrs ltr
Cike gidan yake da jama,a , ta ko ina ka hango gilmawar mutanene a makeken compound din gidan , gefe ga masu kid'an kwaryanan sai wasa manyan  mata suke  ana cashewa , bikin mus,ab da bassam ake , mus,ab wata yar kawar mami ya aura yayinda bassam ya auri yar cousin dinsu aunty ,
  Shagali sosai akai a bikin  kafin dare tuni mutane sun kama gabansu wasu sun tafi dakko amarya sai yan uwa na nesa da zasu sake kwana  .
  Hannace ta fito zata apartment din mami , hannunta rike da hanan da take ta zuba mata shagwaba , jin wayarta na ringing ta fiddota daga cikin jaka  , sallama tai daga can bangaren haydar ya langwabe murya yace "sweet aji dani pls , tunda aka fara bikinnan bakida lokacina ko?"
  Kamar zatai kuka tace " wllh habibi wannan hanan din CE duk ta dameni ,taki yarda ta zauna wajen kowa " murmushi yay yace "oh sorry sweet munyi laifi ba,amu sake ba, amma  ki rarrasheta mana sweet ta daina rigima kinji" ya karasa shima a shagwabe , murmushi tai tace "Allah baby duk kai hanan ta gado , kaimafa shagwababbene Allah" murmushi shima yay yace "duk shagwabarmu batakai ta sweet ba , any way ki samu ki kaiwa mami ita ko taho parking space ina  jiranki " daga haka ya kashe wayar ,
  Wayar tabi da kallo tana    murmushi can ta kalli hanan data tsura mata manyan idanunta cikin shagwaba tace "Ammina" Hanna tace "yes my dear hanan " murmushi hanan tai nan kumatunta suka lotsa  tace "nidai wajen abeiy zani" hanna tace "abiey yace ki zauna wajen mami yanzu zamuje mu dawo ko dear" bata jira cewartaba ta shige parloun mami , can bedroom ta sameta itada kawayenta , kwace hannunta hanan tai ta tafi wajen mami da gudu ta dane  cinyarta , Hanna ta tabe baki tace "dama wajenta zan kawoki ai , bakina ya huta na kwana biyu" dariya mutanan dakin sukai mami tace " itama ta huta da fadanki Hanna , sai kace bake tayo ba " murmushi Hanna tai tace "wlh dan  bakisan hanan bane , dama yaya yace gobe  zai taho mata da kayanta ta kana biyu mu samu mu huta da bari bari" mami ta tabe  baki tana shafa bayan hanan data lafe a jikinta tace "kudai kuka sani ba ruwana , hanan kuma a kawomin kayanta kaff in rike abata , ni bazan gaji da itaba bangaji da uwartaba lokacin datai tashenta baran tana ita dana fi so" Hanna ta hade rai tace "yanzu mami kinfi son hanan a kaina" mami tace "kwarai wacece kuma Hanna?" Juyawa tai ta fice daga bedroom din kamar zatai kuka tanaji mami na kiranta tana dariya ta wuce,
  A parking ta tadda  haydar yana zaune a motarsa yabar murfin motar a bude, kai tsaye ta shiga tana kumbura fuska , kallanta yay yana hadiye dariyarsa ganin yadda take cika tana batsewa, shiru yay sbd yasan yan rigimar suna kusa, motar ya tayar  ya fice daga gidan batare dayace komai ba Wanda hakan ya sake kular da Hanna,
   Suna zuwa gida ta bude murfin mortar ta fice fuuu tana huci , ledojin da suka tsaya sukai take away ya kwaso ya shigo dasu  ,
A parlour ya tadda  ita ya ajiye ledojin ya wuce bedroom ta bisa da kallo ,
  Bataji fitowartaba sai jitai an dagata  sama ta juyo a firgice  dan  unexpected abun yazo mata, kukan da take dannewa ne  ta rushe dashi kamar warce akaima wani abun, baibi ta kantaba ya wuce toilet da ita yana mata murmushi,
Kusan 40m suka d'auka suna wasa kafin su yo wankan tana makale a jikinsa tana zuba masa  shagwaba  , da Kansa ya shiryata cikin wasu tattausan sleeping dress masu  azabar kyau da d'aukar hankali , a kujera ya ajiyeta ya dauki ledojin daya  shigo dasu  ya wuce kitchen bai jimaba ya fito da plate din gasashshiyar kaza  sai Kamshi take da cups ,
  A jikinsa ya zaunar da ita ya ringa bata cike da so da kana itama tana bashi , saida suka koshi tass  sannan ya d'agata sama  yace "sweet zo muje master bedroom na baki wani sako" make kafad'a tai tana turo baki tace "naki wakon" yana murmushi yace "pls mana my sweet dina ,vitamin abcdef,,z fa zan baki duk ke kadai"  dariya ta fashe da ita tace "toh babyna , amma meye master bedroom?" Kallanta yay take moment din daya  wuce 3yr back ya tuno  , wani lallausan murmushi ya saki ya langwabar da kai yace "kinaso kisan  master bedroom?" Ta daga kai a hankali yace "toh zo muje in nuna miki shi ,in kuma baki vitamin din da ake bayarwa acan"  a tare suka kyalkyale da dariya cikin tsananin so yace "I love u Hanna ,I love u so much sweet wife ," kiss ta manna masa  a cikin son mijinta tace " I love u too my sweet yayana, ina  alfahari kasancewarka mijina, ina kuma rokon Allah ya barmu tare ya had'amu a aljanna baki d'aya" can kasan ransa ya amsa da amin kafin ya wuce da ita master bedroom idanunsu sarke cikin na juna suna aikawa juna sako.

*Alhamdulilah nan na kawo karshen wannan buk din mai  suna Hanna  , kuskuran danai Allah ya yafemin , ina  kuma godiya da jiran da kukaiwa wannan buk din bakuyi fushiba ngd ngd sosai*

   Jinjina ga duk daukacin groups din da nake  ciki harma da Wanda bana  ciki masu bibiyar wannan buk din Allah ya hadamu


Sai mun hadu a buk na gaba Wanda bazan fara post dinsaba harsaina kusa kammalawa ma,assalam.

08107942566 gamaison document a satinnan za,a had'a insha Allah ngd

*Maryam Abdullahi OumRamadan*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 27, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HannahWhere stories live. Discover now