Hannah part 15

383 33 2
                                    

💥 *Hannah* 💥

        1️⃣5️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

*Nagode sosai da addu,oinku jiki Alhamdulillah thank 4d love and care*

Riga da sket ne a jikinta na shadda yellow da akaiwa aiki ja kwalliya tai sosai tamkar ka saceta ita kanta aunty Saida ta furta Masha Allah sbd ba karamin kyau taiba aunty tana murmushi tace "auta sai Ina" zama tai kusa da aunty tace "kin manta yau  zamu wunin Yar ajinmu a islamiyya" aunty tace "oh haka nefa to kardai ku Jima ku dawo da wuri" Mikewa tai tace "Tom aunty" bedroom ta koma ta dakko mayafi ja da takalmi sai wata karamar jaka itama ja ta fito taiwa aunty sallama,
  A compound d'in gidan ta tarar da farouk da sameer, gaba d'aya Sameer ya zuba mata ido yana sakar mata murmushi tun daga nesa waya ya dakko ya fara mata hotuna ita Kuma sai sakin murmushi take daya karawa hotunan kyau,tuni ruwan da farouk yakesha ya kwaresa ya shiga tari  direct wajensu ta dosa tana juyawa taga haydar yana Mata wani mugun kallon daya kad'a yan hanjinta ba Shiri ta juya  zuwa side d'insu fannah, Sameer ne ya mike zaibi Hanna haydar da karasowarsa kenan ya rike hannunsa fuska d'aure ya komar dashi shima ya zauna,wata ajiyar zuciya farouk ya sauke da duk Saida suka kalleshi ya d'auke Kai yana shafa keya,
  Tare suka fito da fannah itama tai kyau sosai ,suna niyyar ficewa haydar ya daka musu wata tsawa yace "kuzo Nan" hanna ta kalli fannah cikin rad'a tace "nidai wlhy bazani ba" fannah da tsoro ya kamata tace "gsky gwara muje Kar anjima ya dakemu" tsaki hanna ta saki tana satan kallan inda suke cikin miti 1 ta bud'e get ta fice kamar walkiya fannah ta bita da gudu,
  Wata dariya Sameer ya  fashe da ita, farouk kuwa murmushi kawai yay  yayinda haydar ya saki baki yana bin kofar get d'in da kallo ransa a 6ace kwafa ya saki cikin ransa yana cewa zaku gamu dani,
zaune suke a cafeteria ita da rauda ta kwantar da kanta a hankali tana lumshe ido sbd murd'awar da mararta take mata ,rauda ta sunkuyo inda take tace "sannu friend"
Kusan mintuna 2 ta d'ago tana murmushin karfin Hali tace "yawwa friend naji ma sauki" rauda tace "Allah ya Kara sauki,kin kuwa ji lecture da akai yauma kuwa?"
  "Wlhy rauda ban fuskanci komai sbd a lokacin sosai yakemin ciwo amma yanzu Alhamdulillah"
Unexpected sukaji ance "idan baku fahimci abinda aka koyar da kuba ku ringa tambayar malamin" da sauri suka juyo suna kallan Barr mk baki bud'e,
  Kujera yaja ya zauna ,ma,aikacin wajen ya taho cike da girmamawa yace "yalla6ai me za,a kawo maka?" Kallansu yayi yace "me kukeson ci?"
Rauda tace "jallop rice"
Kallan hanna yayi yace "kefa?" Satan kallansa tai suka had'a ido ta girgiza kai baice komai ba yace "kawo mata snack nida ita" gaba d'aya mutanan cafeteria sukai shiru suka zubawa Barr mk idanu cike da mamakinsa, yammatan da suke cafeteria d'in tuni suka maida idanunsu kansu cike da tsana ko wacce zataso ace ita Barr mk ya Kula,
Kwata kwata hanna kasacin snack d'in da aka kawo mata tai jinta take a takure musamman daya kasance duk ta d'ago idanunta Sai sun had'a ido da Barr mk yana sakar mata murmushinsa Mai kyau da yake fad'ar mata da gaba,
  Da yaga takici take away yasa akai mata na snack kala kala ,mikewa hanna tai ganin rauda ta gama cin abincin kamar munafuka ta fice daga cafeteria d'in batare da ta kalli kowa ba, wajen wasu Kujeru ta zauna tana jiran fitowar rauda,
  Hangosu tai sun taho da Barr mk direct wajen da take suka nufa ya zauna Kujerar da take kallan tasu ganin yadda yaci serious yasa suka shiga hankalinsu ,cike da kwarewa ya koya musu lecture da yay saida ya tabbatar sun gane sannan ya mike daidai inda take ya tsaya ya ajiye mata take away d'in k'asa k'asa yace "ki tabbatar kinci kinsha magani"
  Baki bud'e take kallansa harya juya ya dawo wayarta da ta manta a cafeteria ya ajiye mata yayi wucewarsa, wani kallo rauda take binta dashi Sai Kuma ta saki dariya, harara ta gallara mata tace "ke Kuma lafiya?"
Bude hannu tai tace "lafiya kawai dai abin boyene yake Neman fitowa fili" tabe baki tai bayan ta bude take away d'in tace "aefa saikiyi tayi kuma" tace tana gutsiran samosa, "ae abunne da d'aure Kai friend,wai kinsan yadda yammatan skull d'innan sukebin Barr mk ya kulasu kuwa,ko kallo basu isheshi ba ke cafa akai in yarinya ta cika takura masa carry over yake bata" Hanna tace"to ni Kuma me hadina da wannan zancan,Kinga ki barni naci abincina malama kin dameni"
"Gskyne abincin masoyi dadine dashi" rauda tace tana dariya dundu ta kaima a cinya tana galla mata harara tace "koba masoyiba" sosa cinyar tai tana yamutsa fuska tace "mudai muna zuba ido,ni dama nasan ba banzaba,kuma dukan da kikaimin zan rama"
"Zadai ki rame yarinya"
Sauran snack d'in ta saka a jaka bayan ta dibarwa rauda sukai sallama ,tsaye ta tadda basma tana jiranta tana zuwa ta shige mota da sauri kafin basma tace komai ta zuro dakai tace "ya basma kefa nake jira" takaici ya ishi basma ta kasa cewa komai, kyalkyalewa d dariya tai ta kamo hannunta bayan ta shiga mota tace "afwan ya basmata" kunnenta ta rike tana dariya tace "toh ya zanyi dake hanna tunda kin gama rainani,Kinga makwancina"
Murmushi kawai tai sbd tsikarawar da mararta tai,har sukaje gida bata sake cewa komai ba ,zuwa lokacin banda juye juye ba abunda take basma duk ta rud'e,
  A haka suka karasa gida dakyar ta zuro kafafunta waje kafin basma ta zagayo inda take tuni ta fito fuskarta duk hawaye wani nabin wani, rikota tai tana mata sannu a compound suka gamu da haydar Yana Sanye da jallabiya bai amsa gaisuwar da basma take masa ba yace "ita wannan kukan me take?"
"Batada lfyne Yaya" basma tace a hankali ,"me yake damunta?" Inda inda ta shigayi ta rasa me zatace masa ,kallansa ya maida kan hanna da take rike da mararta tana kuka ya d'auke kai ya wuce ta gabanta,
  A parlour ta taimaka Mata ta kwanta ,tagumi aunty tai  bayan ta cire Mata hijab d'in jikinta tana kallanta tana Shirin mikewa haydar yayi sallama hannunsa rike da ledar drugs,
  Murmushi aunty tai ta amsa sallamar basma ya kalla yace "dakko mata ruwa" da sauri ta dakko ruwa da cup ta zuba mata ledar ya bud'e ya ballo magungunan ciki ba yabo ba fallasa yace "tashi kisha"
Dakyar ta mike tana yamutsa fuska ya bata maganin tanasha ta koma ta  kwanta ,ledar ya mikawa basma yace "anjima in taci abinci tasha "
Sallama yayi aunty ta rakashi har kofa tana godiya ,bacci ne ya kwashe ta sai gab da magriba ta farka  sosai taji  dadin jikinta, wanka ta farayi tasa pad tana zaune gefen gado taji wayarta na ringing kamar bazata d'aga sai Kuma ta mike kafin ta isa inda wayar take Kiran ya katse, harta juya ta sake jin Kira ya shigo wayar ta dakko zaro ido tai tanabin sunan dake jikin screen din wayar da kallo baki bude.

HannahWhere stories live. Discover now