Hannah part 19

334 34 3
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
1️⃣9️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Barr mk suna gama magana da abba yay wani murmushi yana cilli da wayar hannunsa,ada baiyi niyyar auran taba ko kad'an sosai ya kashe kirshirwarsa a kanta dan sosai yake bala,in sha,awarta bai fito Mata Kai tsaye ba sbd yasan ita ba Yar hannu bace,
Cikas din daya samu da daddynsa ya matsanta Masa shiyasa ya yanke shawarar auranta sbd kaf cikin yammatansa ya gama gamawa dasu a awaje bazai iya auran suba yafi so ya auri virgin Kuma koba komai Yana Sha,awarta zai ringa biyan bukatunsa kafin ya samu wacce yakeso ya aura ,
Washe gari sukuku hanna ta tashi duk jikinta a sanyaye haka suka kammala aekin gida tana satan kallan aunty data had'e rai dan gaisuwarta ma dakyar ta amsa hakan yasa suna aikin tana sharar hawaye,
Basma duk ta damu itama bedroom d'in aunty ta shiga ta zauna kusa da ita a hankali tace "aunty dan Allah kiyi hakuri in wani abu hanna Tai Miki tun jiya take kuka Kuma taki fad'amin komai" harara aunty ta gallawa basma tace "gafaracan sakarya Nan nace ki sawa kanwar taki ido dake ke shashashace kin saki baki tanacan tana soyayya da malaminsu baki sani ba,kuna kwana tare a daki d'aya ki kasa gano dawa take waya to tunda abinda ta zaba abbanku yayi magana da yaron tunda aure takeso ae shikkenan"
Tunda aunty ta fara magana basma ta saki baki da hanci tana kallan ta, ta kasa cewa komai dan mamaki harara aunty ta sake watsa Mata tace "maza ficemin kema hadda laifinki ae,ni zanwa Abba magana ma duk ya had'e daku a huta"
Da sauri basma tace "Dan Allah aunty kiyi hakuri hakan bazata sake faruwa ba" ta6e baki aunty tai ta fice daga d'akin,
Tana kwance ita kad'ai a daki tunda sukai breakfast ta dawo ta kwanta tana ganin Kiran Barr mk tak'i d'agawa haka kawai takejin haushinsa,
Hijab tasa ta wuce part d'in mami a parlour ta tadda haydar cikin sanyin murya tace "Yaya Ina wuni" kallanta yake cikin mamaki batare daya amsa ba ganin tana niyyar wucewa ya Kira a tausashe yace "zonan" dawowa tai kusa dashi ta zauna kusan minti 3 taji yace "me yake damunki?" Shiru tai ta kasa magana ya juyo yana kallanta da kyau a nutse yace "bazaki fad'amin ba? Meyake damunki" kamar jira take ta fashe da kuka harda shehssheka tace "aunty ce take fushi dani Yaya" shiru yay can yace "toh haka kawai zatai fushi dake ,kodai kin mata wani laifine?"
Cikin kuka tace "nifa ba abunda nai mata Yaya" d'aure fuska yad'anyi kad'an yace "ok so kike inje da kaina in tambaye ta ko? Kinsan in baki fad'amin da kanki ba hukuncin da zan miki ni kad'ai na sani" a tsorace tace"in,,dama,,dama yaya wlhy wani malamin mune yake kirana muna gaisawa Kuma fa daga gaisuwa ba wata hira muk,,," kasa karasawa tai sbd wani mugun kallo da yake jifanta dashi a tsorace take ja baya ganin yadda lokaci d'aya idanunsa sukai ja kafin ya ankare ta falle da gudu a miliyan tana komawa side d'insu tai wulli da hijab din ta kwanta gabanta na dukan 9 9,
jin karar bud'e kofa yasa ta juyo basma ta gani tsaye tace "Hanna kizo ya farouk yana kiranki"
Mayafi ta yafa a kanta gabanta na fad'uwa ta fito duk ta d'auka yaji zancan shida kullum yake Mata kashedin kula samari ,
A parlour ta taddashi zauna da trolley a gabansa zama tai tana kokarin boye damuwarta tace "ya farouk Ina kwana"
Yana kallan ta bai amsaba yace "baby me yake damunki?" Murmushi ta kirkiro tace "ba komai ya farouk kainane yake ciwo" ta fad'i hakan dan da gaske kan nata ciwo yake ,
Tuni ya rud'e yace "kinsha magani? Ko mu tafi hospital?" Girgiza Kai tai tana dariyar yak'e tace "Kai ya farouk nafa ji sauki Kuma nasha magani" ajiyar zuciya ya sauke yana kallanta yace"sannu baby , Allah ya sawwake,tafiya zanyi baby" zaro ido tai tace "ina Yaya farouk?"
"Chaina zani ba dadewa zanba baby 3week kawai zanyi na dawo" a sanyaye tace "to ya farouk Allah ya tsare zanyi missing d'inka over" ta fad'i a shagwa6e,hannunta ya rike idanunsa sun fara canja kala yace
"Nima haka baby ,zanyi kewarki fiye da yadda kike zato ,ki rikemin kanki kinji ba ruwanki da kula samari idan Allah ya dawo dani lfy akwai muhimmiyar maganar da zan fad'a Miki"
Murmushi ta kirkiro gabanta na fad'uwa tace "toh ya farouk Allah ya tsare" trolley ta ja masa bayan yay wa aunty sallama hanna da basma suka rakashi parking space inda haydar ne zai kaishi airport da yake week end ne, hannu ta dinga d'aga masa harta fara hawaye zuge glass yay shima yana kallanta kamar zai kuka ,da gayya haydar yaja motar da gudu bayan ya tabbatar an bud'e musu get yana tsaki,
A parking space d'in ta zauna taci kukanta ta koshi tana niyyar mikewa wata lafiyayyar mota ta shigo bayan mota ta d'an boye tana leken Wanda ke ciki saidai kafafu kawai take gani sbd na motar har yanzu bai fito ba,
Kusan suman tsaye tai ganin barr mk ya fito cikin wata dakakkiyar shadda ruwan zuma sai maiko take,kansa sanye da hula tangaran da akai mata adon zare coffee haka takalminsa da agogon hannunsa duka coffee kasa d'auke idanunta tai daga kansa dan wani kyau taga ya mata bata ta6a ganinsa da manyan Kaya ba Sai yau,
Tana kallo ya wuceta ya nufi part din big daddy ,zama tai a wajen gabanta Banda dukan 9 ba abinda yake gaba d'aya mamakin lamarin mk take ko Taya ma akai yasan gidansu?,
Kasa komawa cikin gidan tai ta koma can wajen wasu shukoki ta zauna akan kujerun wajen,
Barr mk kuwa a parlourn big daddy ya zauna a kan carpet big daddy da small dad sai abbane kawai a parlourn, cikin tsananin ladabi mk ya gaidasu gaba d'aya ya kasa had'a ido dasu saika rantse wani mutumin kirkine,
Hakan da yayi ba karamin burge su abba yay ba koba komai hankalinsu ya Fara kwanciya big daddy ne yay gyaran murya ya shiga tambayarsa alakar dake tsakaninsa d hanna sosai ya sake kass da Kai yace "sonta nake da aure daddy ,maganar da nake muku ma daddyna yana batun zuwa wajenku neman,,,ehm " ya shiga shafa kai yana sosa keya ya kasa karasawa,ajiyar zuciya Abba ya sauke daddy yace "to madalla waye mahaifin naka?"
" Alhaji kabeer rano shine mahaifina tsohon sanata ne yanzu haka muna zaune a Jan bulo first gate"
Daddy cikin mamakiyace "Wai kabeer rano shine mahaifinka?" Mk yace "eh daddy" big daddy yace "Masha Allah fad'uwa tazo daidai da Zama kabeer rano abokinane kaje zan nemeshi idan munji ta bakin yarinyar"
Cikin ladabi ya russuna yace "to daddy Allah ya saka da alkhairi ya Kara girma" daga haka yay musu sallama ya fice Yana sakin wani murmushin da shi kad'ai yasan ma,anarsa,
Tsaye yay yana karewa compound d'in gidan kallo,tafiya yake yana wurga idanunsa a ilahirin gidan, motace ya hango ta shigo gidan daidai lokacin hanna ta fito a tunaninta mk ne ya fita ,
Ido suka had'a ta zaro ido da sauri ta koma inda ta fito, murmushi mk yay ya juya yana kallan haydar daya fito daga mota fuska d'aure ya wuce apartment d'insu yana danna waya,
Inda yaga hanna tai ya nufa hangota yay a tsugunne ta boye a bayan wata fulawa,
Ta bayanta ya biyu a hankali ya zubawa bayanta ido sunkuyo da kansa yay yaja Mata jelar gashinta da take lilo,
Ihu ta fasa a tsorace ta mike tana Shirin guduwa ya rike hannunta Yana dariya,

HannahWhere stories live. Discover now