Hannah part 17

397 36 3
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        1️⃣7️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

K'arfe 9:30 suna zaune a parlour d'aga ita sai basma aunty tana parlourn abba,wayarta dake  hannunta tana buga gyme taji Kira ya shigo,ganin sunan da ke screen d'in wayar yasa ta saci kallan basma dake gefenta ganin hankalinta ba,a nan yake ba yasa ta mikewa a hankali ta shige bedroom,
A kufule ta d'aga wayar kamar zatai magana Kuma tai shiru tana jiran yay, shiru barr mk shima yay yana jiran yaji ta fara magana ,mamaki ya kamasa ganin sun kwashe few minutes batare da ko yaji tarin taba,murmushi ya saki mai sauti Wanda har hanna taji ya langwa6ar da wuya kamar tana ganinsa kamar meyin rad'a yace"Ina son mace me aji"
Boyayyan numfashi ta saki tana sake gyara zamanta akan gado,sai dai gaba d'aya yayinta ya sauya tunda yay magana taji gabanta ya fad'i,
"Gimbiya" ya sake kiranta a tausashe har wani lumshe ido yake "kimin magana pls" ya sake fad'a wannan Karan a shagwa6e kamar wani yaro,
Turo baki tai itama cikin shagwa6er da batasan tayi ba tace"toni ka fad'amin waye" barr mk Saida ya kankame pillow dan ba karamin shigarsa shagwa6erta taiba ,yanason mace me shagwa6a sosai shiyasa kaf yammatan da yake mu,amala dasu yafi jin dadin hanny dan ita bataki ta wuni tana zuba Masa shagwa6a ba matukar zai biye Mata,
Muryartace ta katse masa tunanin da yake tace "zan kashe tunda bazaka fad'amin ko waye ba"
"Bakiga sunan da yake jikiba?" Yace mata yana juyi akan katon bed d'insa, ta bud'e hannu kamar Yana gabanta tace "banida masaniya tunda nasan bani nasa ba"
"Toya kenan? Inbake Kika saba waye yasa?" A kufule cikin tsiwa tace "kama malam Sai anjima" tana gama fad'a ta katse wayar,
Shigowar massage wayarta yasa ta bud'e manyan idanunta ta harari wayar da Kira ya sake shigowa d'aga wayar tai bayan ta karanta message d'in ,a nutse taji yace "malamin kine"
Wannan Karan cikin sanyin murya tace"malamaina da yawa wanne daga ciki?"
Mk ya jinjina Jan ajin Hanna a ransa wato dole saiya sauke nasa kenan,Karan farko a rayuwarsa daya ta6a daukar waya ya Kira mace baran tana ya tsaya yi mata dogon sharhi macen ma karamar yarinya "Malam Mk"
Zaro ido hanna tai cikin rawar Baki tace "sir...dama Kaine?"
Narke murya ya sakeyi yace "nine mana kiketa wani kwana kwana bayan Kinga sunana a jiki" boye fuskarta tai kamar yana ganinta murya can ciki tace "to sir ni Banga sunankaba bafa wlhy "
"To ya jikin naki" ya canza hirar , a hankali tace "naji sauki".... "Kinsha magani?" Ya sake tambayarta cike da kulawa,itadai gaba d'aya kunya ta hanata sakat ta gyad'a kai kamar yana ganinta,gyaran murya tai jin zai sake magana tace "ehem sir auntyna tana kirana sai da safe"
Murmushi ya saki kad'an yace "ok ki gaidata bye" batace komai ba ta katse wayar gabanta na fad'uwa ,kwanciyarta ta gyara tana mamakin inda  ya samu number ta ,juyi tai ta kamkame pillow cikin sabon bakon lamarin da ke Shirin ziyartar rayuwarta ,to kodai raudace ta bashi number ta? Taiwa kanta tambayar numfashi ta sauke a a ranta tana tunanin yadda akai Mata saving numbersa harda wani sa happiness,wata zuciyar tace waye zai daukar Miki waya duk fadin makarantar inba raudaba ,tsaki ta saki tace zamu had'u ne wlhy,
jin karar bud'e bedroom din yasa ta tura wayar karkashin pillow da sauri, da kallo basma ta bita tace "bacci kikeji?"
"Eh" kawai tace tama ta shige toilet a tsorace,
  Washe gari a makare ta tashi wanka kawai tai ta zura doguwar riga ta yafa mayafin rigar ta kwashi littattafanta a gurguje take komai ganin tana niyyar fita bataci komai ba yasa aunty tace "dawo ki breakfast bazaki fita haka ba" hanna da hawaye ya kawo idanunta tace "zanci a makaranta aunty nayi latti" d'aure fuska aunty tai tace "tun yaushe basma take tashinki kikaki tashi,ni bansan baccin me kikai ba da har ake tashinki kikaki motsawa gashi ita harta shirya ke take jira "
Marairaice fuska tai tace"to aunty dan Allah innaje can zan karyafa" cikin tsawa aunty tace "Zaki wuce ki karya kosai na taso?" Da sauri ta d'auki tea din da basma ta had'a Mata tanasha tana hawaye dan yau lecture farko ta Barr mk ce ta san inhar tai latti bazai barta ta shiga ba,
  Saida aunty taga ta shanye tea din tass ta barsu suka tafi ,sai karfe 8:40 suka isa makaranta ,jiki a sanyaye take dosan hall d'in a bakin kofa ta makale ta kasa lekawa, can dai  tai shahada ta d'an leka kanta cikin hall d'in,
4eyes sukai da barr mk da sauri ta koma gabanta na fad'uwa,kamshin turaran da taji ne yasa ta d'ago da kanta tsaye ta gansa a bakin hall d'in yana kallanta yace "zoki shiga"
Yana fad'a ya koma ciki,a sanyaye take d'aga kafarta ta shiga hall d'in sum sum ta wuce kamar munafuka tana satan kallan Yan ajin da duk suka zuba Mata ido cikin tsananin mamakin abinda barr mk yay ,
  Fuska d'aure hajiya binta ta shigo bedroom d'in siyama tana kwance tana danne danne a waya zama hajiya binta tai tace "siyama"
Tana daga kwance tace "na,am mom"
"Ki tashi ki shirya Anwar yana parlourn baki yana jiranki" turo baki tai tace"Dan Allah mom ki manta da wani zancan Anwar dinnan kwata kwata baimin ba tayaya zan iya son wani bayan zuciyata haydar take so"
Huci hajiya binta ta sauke cikin bacin rai tace "wlhy siyama ki shiga hankalinki dani a gidannan,ki fita idona in rufe ke wace irin wawiyace kina girma maimakon kiyi hankali sai tsabar rashin sanin ciwon kai, kin fara kaini bango haka zanta zuba Miki ido shekara 25 kin makalewa Wanda bai damu dake ba ,in zai soki da tuni ya soki tun yaushe kuke tare dashi shekara nawa kina bibiyarsa yaki kulaki ,ke bazaki nutsu kiwa kanki fad'a ba , to wlhy kin fara kaini bango yakamata ace kin saduda kin rumgumi masu sonki da gaskiya"
Bata rai siyama tai tace"haba mom ki daina fad'ar haka mana, wayace miki bai sona lokacin,,,," katseta hajiya binta tai cikin tsawa tace "Dan ubanki tashi ki shirya kije ki sameshi kafin ranki yay mummunan baci anan,Kuma in Kika sake na dawo dakinnan nida kene wlhy " Mikewa tai ta fice a fusace, 6ata fuska siyama tai tanabinta da kallo harta fice ,
  Mikewa tai tasa hijab ta sa plate shoes ta fice a parlour ta tadda hajiya binta har lokacin ranta a bace yake wani mugun kallo hajiya tabi siyama dashi cikin tsawa tace "wannan shine Shirin da nace kiyi sbd kin rainani" juyawa tai rai a cunkushe ta koma bedroom doguwar ta sake ta yafa mayafinta ta fito tana had'e rai,kwafa hajiya binta tai tana hararta ,
Maimakon ta wuce parlourn baki saita zagaye ta wuce lambun gidan inda wasu kujeru suke tai tazamanta anan,
Kusan minti 30 Anwar yay yana jiran siyama kafin ya mike a kasalance ya fice daga parlourn batare da yayiwa hajiya binta sallama ba,
  Kafin ya karasa ya hango siyama kamar ya wuce sai Kuma ya doshi inda take , kamshin da tajine yasa ta d'ago da kanta ta saukesu akan Anwar da ya tsaya ya zuba Mata ido yana kallanta tuni ta sake d'aure fuska ta had'e rai a nutse ya karaso inda take yace "nasan kinajin haushina a zuciyarki ko? Kinajin haushin ina bibiyarki naki daina kulaki ko? Kinamin kallon mara zuciya daya nace miki,kinajin haushin yadda naki rabuwa da ke ko? Kinamin kallan mutumin da yay Miki Karan tsaye a rayuwarki ko?" Numfashi ya sauke a hankali kana yace "irinsa Wanda kikeso yakeji a ransa siyama,duk irin abinda kikeji a kaina haka shima yakeji a kanki , meyasa zaki ringa wulakanta Wanda yake tsananin sonki at least ki mutuntani siyama kusan duk sanda Zanzo wajenki bakimin kallon arziki ko kiki fitowa meye laifina dan zuciyata ta kasance tana sonka?" Jikin siyama duk yayi wani mugun sanyi ta kasa kallan anwar tana gani ya juya ya wuce sannan ta d'ago tabi bayansa da kallo wasu zafafan hawaye suka zubo Mata.

*Assalamualaikum dear fans Ina ganin yawan korafinku akan a Kara yawan typing, wlhy bazan iya typing me yawa kullum ba sbd inada iyali ga aikin gida amma in kunason typing me yawa to za,a daina post kullum a koma yi duk bayan kwana 1 ko 2 kokartawa nake Ina muku typing dinnan ba jin dadin jikina nake sosai ba sbd na farane Kuma banason na Kuma ajiyewa amma ina jiran ra,ayoyinku a cigaba dayi haka kullum ko Kuma a komayi duk bayan kwana 1 or 2* 08107942566

Zaku jini shiru yarona ba lfy tun 3 nake a hopst ana kara masa ruwa typing dinma dan nayine tun safe shiyasa

HannahWhere stories live. Discover now