Hannah part 34

499 54 12
                                    

💥 *Hannah*💥
*Romantic love story*
        3️⃣4️⃣

*Maryam Abdullahi (Oumramadan)*


Washe gari da asuba ita ta fara tashi a hankali ta bud'e idonta ,jinta a jikin mutum yasa ta sake bud'e ido da mugun mamaki gaba d'aya tai kane kane a jikinsa ji take kamar ta fashe da kuka gashi ba damar motsi sbd kunya,
  Rufe ido ta sakeyi a hankali ta dinga kokarin zame jikinta saidai kwata kwata bashida alamar sakinta dan har wani sake makalemata yake ,turo baki tai cike da takaici ta d'auke kanta,
  A hankali ya shiga ware idanunsa slowly yanabin fuskar hanna data fara masa wlcm da kallo bakinsa yakai kan goshinta ya sumbata can k'asa yace "good morning baby" lamo tai a jikinta ta kasa motsi tanaji ya mike a hankali ya fice daga d'akin ta bisa da harara ta mike ta shige toilet,
  Wanka ta farayi sannan ta fito sata doguwar riga tana niyyar tayar da sallah ya shigo jikinsa sanye da jallabiya fara tass fuskarsa da alamar lemar ruwan alwala,batai maganaba kamar yadda shima bai mata ba dadduma ya shimfid'a ya jasu sallar dan masallacin unguwar sun idar, suna idarwa dakyar tai azkar dan wani irin bacci takeji k'asa k'asa tace "ina kwana yaya"
  "Lfy Lau "
Yace mata ba yabo ba fallasa ta gefen ido ta kalleshi ta ta6e baki a ranta tana cewa mutum kamar me aljanu yanzu ka ganshi yana abun kirki anjima ya wani d'aure fuska,ta sake ta6e baki ta mike a hankali taji yace "gulmata kike?" Ta zaro ido tace"ni?" Girgiza kai yay yace "aa ni" turo baki tai tace "nidai banyi maganaba" baice komai ba saida ta juya ta murguda baki ta haye kan gadon ta rufe kanta da duvet bata jimaba bacci ya d'auketa,
  Shima bai jimaba ya mike ya koma bedroom d'insa ya koma bacci,
  Karfe 8 hanna ta tashi kai tsaye dama toilet ta fad'a wanka tai ta fito d'aure da towel akan stoll ta zauna ta goge jikinta da wani towel d'in ta shafa manta sannan tazo ta mulke jikinta da humra me mugun kamshi ta kuma dakko body spray ta fesa lokaci d'aya d'akin ya dumame da wani irin kamshi me dad'i powder ta shafa ta taje girarta tasa jambaki light brown tasa eyeliner parking d'in gashinta ta gyara ta mike ta bud'e wardrobe ta za6o wani bakin material da akai masa ado da baby clour dinkin riga da sket 8 pieces tasa ta koma gaban mirror ta nad'a daurin dankwalinta sosai tai wani irin kyau ,
  Gadon ta karkad'e ta sake gyarashi duk daba wani datti yay ba ta fesheshi da air freshener me kamshi,
  Plate ta d'akko pich clour tasa ta fito parlour tsaye tai tana karewa parlourn kallo ba karamin burgeta yay ba azuciyarta ta dingayiwa iyayenta addu,ar gamawa da duniya lfy,
  Karkad'e parlourn ta shigayi shima ta fesheshi da air freshener tana juyowa taga haydar ya rik'e kugu yana sanye cikin wata shadda ruwan Zuma sai maiko take yayi kyau sosai ,
  Yadda  rik'e kugun ne ya bata dariya bataiba sai d'an murmushi tai ta ajiye freshener d'in,takowa yay a hankali ya zauna kan Kujera yana kallanta ta k'asan ido turo baki tai ta d'auke kai tana hararar kujerar gefenta ta zauna , mikewa yay ya sauka downstairs ta bisa da kallo direct k'ofa ya nufa sama sama yakejin bugu yana bud'e yaga driver d'auke da basket a hannunsa da flasks madaidaita guda biyu , kar6a yay bayan sun gaisa yakai dining ya ajiye ya wuce upstairs bai mata mgn ba sai hannunta daya kama ya mikar da ita tsaye yasata a d'ayan barin jikinsa a haka suka sauka kasa itadai ganin abin take kamar a mafarki ta kuma rasa dalilin dayasa take kasa musa masa ko yar tsiwar data sabayi masa,
  Kan dining d'in ya ajiyeta ya ya juya wata k'ofa taga ya shiga bai jimaba ya fito hannunsa rik'e da cups da plate da cokali tana zaune kamar status sai binsa take da ido ya ajiye cups d'in ya fito da kayan da yake cikin basket d'in hannunta takai kan nasa da yake shirin bud'e abincin gani tai kamar bai kamataba cikin sanyin murya tace "ka bari zan zuba"  hannun nata ya kurawa ido dayasha Jan lalle yayi mugun kyau sunkuyawa yay ya sumbaci hannun cikin shauk'i da kyan da yay masa,
  Da sauri ta janye hannun sakamakon yadda jikinta ya sauya ta dingajin wasu abubuwa na mata yawo  tsigar jikinta tana tashi ,daga jiya zuwa yau lamarin haydar mamaki yake bata gani take kamar bashi bane ta kasa d'agowa ta kallesa sai wasa take da yatsun hannunta , murmushi kad'an ya saki ya bud'e warmers d'in d'aya chicken paper soup ne me had'e da kayan lambu dayan kuma soyayyar doya da kwai ce sai runwa tea da kunun danyar gyad'a a flask d'in,
  Doyar ya zuba ya zuba chicken soup d'in a gefe ya zuba kunun da yasha Madara da kwakwa sai kamshi yake tea din kad'an ya zuba ya koma kitchen d'in ya wanko hannunsa ya fito ya koma kan dining d'in ya zauna kusa da ita,cup d'in tea ya mika mata ta kar6a a hankali suke sha da yake kad'an ya zuba nan da nan suka shanye kusan minti 3 da shanshu ya Kuma mika mata cup d'in kunan ta kar6a doyar ya dakko had'e da had'in kayan lambun ya sa cokali 2 itadai sai rarraba ido take   yunwar da takeji yasa ta dake ta faraci a hankali,
  Kusan tare suka gama ya tayata kwashe plate d'in a sink ta ajiye ta fara wankewa ya shigo taimaka mata yay ya tayata wanke wanken ,
  "Ina tsiwar ta tafine?"
Taji ya fad'i mata a bazata juyawa tai taji ta kusa cin karo da mutum ta turo baki tace "ni fa Yaya banaso" kugunta ya rik'o ya fizgota jikinsa yana kallan idanunta yace "me yake damunkine, banason ganinki a haka ba d'an surutun nan naki kin wani d'inke fuska kamar dai wata boss" kici kicin kwace jikinta take cike da shagwa6a tace "nidai ka sakeni" ya kuma matseta da kyau har Saida ta sakar masa kukan shagwa6a tana turo baki tace "da zafiii fah yaya"
  Ya lumshe ido  yanayinsa yana  sauyawa, wani irin yanayi mai dad'i yana yawo  dashi bakin data turo ya manna nasa akai wani irin sumba ya ringa yi mata me tafiya da ruhi da gangar jiki,jikinsane ya fara tsuma  yanajin wani irin yanayi me wuyar fassara yana shigarsa jin bakinta yake kamar sweet sbd dad'insa numfashi yake saki a hankali 4the first time da ya ta6a kissing d'in wata mace a rayuwarsa ,hanna kuwa tuni ido ya raina fata banda zare ido ba abinda take tuni hawaye ya 6alle mata harda shehssheka,
  Kwata kwata baiji kukan da takeba dan sosai ya fara sakin layi mutsu mutsun da take da karfine ya dawo dashi daga duniyar daya tafi a hankali ya zare bakinsa daga kan nata yana binta da wani kallo k'asa k'asa ,kuka ta fashe da shi me karfi kunya nauyi da haushi yasa ta sulale zata fice ya sake rikota cikin shakakkiyar muryarsa data dishe yace "lesson d'in dazan fara koya miki yanzu,ki ringa haddacewa dan wataran zan tambayeki assignment kuma a aikace nakeso kamar yadda nake kikaga nayi miki"  ta fizge jikinta da karfi ta fice saida taje bakin k'ofa ta juyo ta galla masa harara tace "nidai ba ruwana saina fad'awa mami abinda kakemin na rantse " ta sake fashewa da kukan shagwa6a tace "yanzu fa jibi lips d'ina sai zafi sukemin sabon salon muguntar daka sake kenan nidai gsky banasoo" ta d'an murguda baki ta wuce da sauri , k'aramin murmushi ya saki ya bita da kallo harta fice yana shafa kansa shi kad'ai yasan irin farin cikin da yake ciki fuskarsa sai fidda annuri take duk daba a sake take ba amma tana fitar da wani irin yanayi me nuna mutum yana cikin happy ,
    hanny ce ta fito cikin wasu fitunannun English wear kanta ko dankwali babu yunwa takeji rabonta da abinci tun jiya da daddare dama ko leke bataga idanun mk ba bata wani damuba dan tasan zata fuskanci fiye da haka ma a parlour ta tarar dashi yana zaune yayi zurfi a tunanin hanna tun daga sama ta kalleshi ta shek'e da wata irin dariya cike da rainin hankali tace "ango kasha kamshi ,wane irin angone wannan dabaisan darajar  amaryar saba" tai wani murmushi tace "  kanan kana kunci wacce kake domin ita tuni ta riga ta amarce da sabon angonta sunacan suna kashe juna da kauna ya riga ya kar6e abinda ka kwallafa rai akansa ,dadai zaka rufawa kanka asiri muji dad'in rayuwarmu kamar da inaga zaifi" wani mugun kallo ya ringa binta dashi idanunsa sunyi wani irin ja wani azababban kishi ya tokare masa a wuya kwata kwata hanny bataga tasowarsaba sai saukar maruka taji a jere ,ihu ta fasa a rikice ta juya ya damkota har wani huci yace ya shiga kilarta kamar ya samu jaka,
  Banda ihu ba abunda Hanny take ganin zai illatata yasa ta wawuri wani frame dake kan center table d'in parlourn ta kwada masa a mara,
  Da sauri ya cikata ta mike da gudu tai hanyar bedroom d'inta da fasasshshen bakinta daya kumbara tace "Allah ya isa mugu  Kuma wlhy bar ganin ka samu galaba a kaina sbd ka shammacenine amma mu zuba mu gani dan halak ka fasa abunda kake kulafuci dai bazaka ta6a samun saba har abad,," taku biyu tai ta shige bedroom din sukwane tasa mukulli ganin yayo kanta da karfi,
  Huci ya tsaya yanayi yana yamutsa gashin kansa cikin wani zazzafan kishin hanna center table d'in parlourn yay ball dashi da k'arfi take ya fashe ya zauna a fusace yanacin mugayen alwashi akan hanny da hanna dan yaci alwashin bazai ta6a bari wani ya sameta cikin sauki da kwanciyar hankali ba.

*Kwana biyu ba lallai a ringa samun post kullum ba sbd Ina zuwa asibiti amma in da lokaci zaku ringa ganina kullum insha Allah a tayani da addu,ar samun lfy ngd*

HannahWhere stories live. Discover now