Hannah part 23

362 39 0
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣3️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Suna tsaye a room din da Sameer yake sunyi jugum jugum dasu ,mom d'insa tana rike da hannunsa lokaci zuwa lokaci tana share hawaye,
  Farouk da dawowarsa kenan daga airport kai tsaye dama asibitin ya dosa yana zaune sai haydar shima da yake kusa dashi ,
  Big daddy d small dad sai Abba da papa suna zaune kowa da abinda yake sakawa ,a hankali hannun Sameer suka shiga motsawa mom da ke rike da hannun ta saki salati tana dariya da hawaye tace "Alhaji hannunsa yana motsawa" da sauri aka shiga rige rigen kiran likita ,shigowarsa ce tasa duk mutanan d'akin ficewa ,kimanin minti 10 ya d'auka kafin ya fito yace "to Alhamdulillah ya farka lfy Kuma babu wata matsala sai buguwar da yay idan mukaga yanayin jikin nasa zamu iya sallamarsa anjima" musabaha sukai cikin farin ciki suka kutsa kai d'akin idanunsa a lumshe suke sbd ciwon kan da yake damunsa,
Sama sama yakejin maganganun su Mom suna masa magana shiru yay can ya bud'e idanunsa da sukai jajur cikin wata irin murya yace
  "Daddy da gaske an bayar da Hanna ga wani?" Kallon kallo aka shigayi da yan d'akin yayinda farouk yaji kansa na juyawa girgiza Kai ya shigayi yanabin yan d'akin da kallo mamii ce tai karfin halin yin magana tace "Sameer wace magana kakeyi kaida kake halin rashin lfy," runtse ido ya sakeshi da karfi ya budeso ya sake cewa "mamii ku fadamin gsky da gaske ansa ranar hanna?"  Shiru mamii tai sai mom dinsace tace "Wai son me yake damunkane ,kaga ka kwantar da hankalinka bakaga bakada lfy bane" sudai su Abba gaba d'aya kasa cewa komai sukai sbd Al,ajabi durowa yay daga kan gadon cikin kunar rai yace "kenan da gaske ne mom?" Gyad'a kai tai ta kasa cewa komai,
  Wani irin mikewa farouk yay jikinsa banda karkarwa ba abunda yake cikin rawar baki yace "wai daddy wai wace hannar ake magana? Badai hannataba" yay maganar cikin wani irin murya gaba d'aya d'akin shiru ya d'auka gaba d'aya idanun farouk sun rufe daidai lokacin hanna da fannah suka shigo gabanta ya tsaya ya rike hannunta cikin wani irin tashin hankali yace "hanna wace magana nakeji kina nufin kinba wani zuciyarki ban sani ba" kallansa take da mugun mamaki ta kasa cewa komai cikin wata irin tsawar da bata taba saninsa da itaba yace "kimin magana hanna wani kikabawa zuciyarki?" Ya karasa yana girgiza ta kuka ta fara a hankali ,Sameer da ba Wanda ya kula da tasowarsa ya bangaje farouk yace "hanna ki fad'awa su daddy su janye wannan maganar wlhy ni nake sonki ,kece zabina ke nake kauna tsahon lokaci Ina dakon soyayyarki a Raina hanna ki cewa su daddy nice zabinki" turesa farouk yay ya sake kamo hannunta da suke rawa yace "shin kinsan tsahon lokacin da na d'auka Ina sonki kuwa Hanna?kinsan iya adadin lokutan da nake kwashewa kullum ina tunaninki? Nayi dakon soyayyarki tun baki San soba na soki tun baki Zama mace ba na soki sona gsky hanna kin tuna maganar da nace zan fad'a Miki Inna dawo? Sonki nake Ina kaunarki sbd ke na guji duk wata mace ina sonki Hanna" ya karasa yana girgizata da karfi, huci kurum Sameer yake cikin zafin kishi da tafasar zuciya Yana niyyar magana small dad ya daka musu tsawa cikin 6acin rai yace "wane irin shashanci kukewa mutane a asibiti ,bakuda hankaline ,me kuka mayar damune?" Shiru sukai sai huci da kowanne da yake,dama haydar kansa na kass tunda suka fara bai d'agoba sai dai ransa a mugun bace yake idanunsa sunyi jajur dasu sbd bacin rai har wani huci yake fesarwa  daga karshema tashi yay ya fice yabar asibitin gaba d'aya,
Big daddy ne yay magana cikin bacin rai yace "usman jeka karbo sallama mu wuce gida doctor ya ringa zuwa dubashi gida" yana fad'a ya fice yana gyara babban rigarsa,
  Suna zaune a parlour su 4 big daddy small dad sai Abba da papa bayan dawowarsu daga asibiti,ko wanne da abinda yake sakawa a ransa, big daddy ne yay gyaran murya a nutse yace "yanzu meye mafitane akan wannan lamari? Tambayar da zan muku shin Sameer ko farouk wani ya taba furtawa yana son hannatu?" Papa ne ya girgiza Kai yace "bamu taba wannan maganar dashi ba" small dad yace "ni inaga yarannan zurfin ciki sukai wajen furtawa sai da aka bayar da yarinya zasuzo su daga Mata hankali ,a shawarce dukansu su hakura da ita tunda a cikinsu in akace za,a bawa wani rigimace sabuwa sannan ya zamuyi da yaron daya kawo sadaki?" Shiru dukansu sukai Abba dama kwata kwata baice komai ba tunda aka fara magana big daddy yace "lallai kayi magana anan ,dukansu zasu hakura badan munso ba kuskure dai sun ringa sunyi da suka boye tun farko, za,a barwa Wanda ya kawo sadaki, farouk na hadashi da basma shi Kuma Sameer na hadashi da fannah ina ganin hakan zai rage musu radadin da sukeji,haydar dama zan masa magana ya fito da wacce yakeso duk a aurar dasu a huta koya kuka gani " sai sannan Abba yace "wannan hadin yay sosai alhaji Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi" small dad yace "duk abinda ka yanke yayi Ina goyon baya dari bisa dari"
  Mikewa mom tai bayan ta gama sauraron papa tace "Amma alhaji ayi haka tunda ya rasa waccan a bari mana ya gama hucewa saiya zabi wacce yakeso koma inane" wani kallo yay mata a takaice yace "mun rigada mun gama yanke hukunci sanar dake nai sbd kinada hakki a matsayinki na mahaifiyarsa" yana gama fad'a ya mike ya wuce parlourn sa ta bisa da kallo kamar idanunta zasu fad'o tagumi ta buga tana kallan Sameer daya fito daga bedroom d'insa duk ya fad'a cikin kwana 2 zama yay cikin sanyin murya yace "mom  dan Allah karkisa damuwa a ranki akan wannan lamari na riga na hakura Kuma na karbi za6in da su papa sukaimin watakil biyayyar da zan musu ta sanadin haka Allah ya daukewa zuciyata son hanna ki tayani da addu,a mom zuciyata zafi takemin gani nake kamar bazankai  wani dogon lokaciba" goge kwallar data zubo masa yay ya mike a hankali ya fice da kallo ta bisa ta kasa cewa komai sai hawayen da take ,
   Koda abba ya fad'awa aunty fatan alkhairi tai haka basma ma ta amince tasan intace batason farouk tayi karya sbd yakai namijin da duk wacce ta ganshi saita kyasa, fannah kuwa tunda mum dinta ta sanar da ita take kuka,kuka na farin ciki dajin dadi bata ta6a tunanin zamowa matar Sameer ba duk da kullum cikin addu,a take ,
Ta wani bangaren tana bala,in tausayin yayanta dan gaba d'aya yanzu farouk ya Kuma zama silent dashi kwata kwata baya zaman gida yanzu yay wata rama da kana kallansa kasan ba jin dadin rayuwar yake ba,
  Haydar ne zaune a gaban big daddy ya sunkuyar da kansa kass yana sauraron daddy a hankali yace "tukunna dai daddy " daddy yace "to matarce baka samu ba ko Yaya?" Shiru yay can yace "kayi hkr daddy a farayin nasu inyaso kafinnan na samu wacce nakeso" shiru daddy yay yana kalkansa kusan second 5 yace "to shikkenan tashi ka tafi Allah ya kawo ta gari" mikewa yay yayiwa daddy sallama ya fice a hankali.

HannahWhere stories live. Discover now