Hannah part 20

389 38 5
                                    

💥 *Hannah* 💥
*Romantic love story*
        2️⃣0️⃣

*Maryam Abdullahi(oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

Da sauri ta juyo ta kallesa a tsorace ganin mk ne yasa ta d'aure fuska ta fizge hannunta tana 6ata rai, Kujerar ya janyo ya zauna ya zuba mata lumsassun idanunsa da suka kankance,
  Kawai sai ta rufe fuska ta fashe da kuka harda shehssheka ,mk jin kukan yake yana ta6a masa zuciya tuni idanunsa sukai jajur murya kamar zai kuka yace "beauty nine bakison gani Koh?"
Ta dakatar da kukan da take a hankali tace "Toni wayace kazo gidanmu kawai kasa aunty sai fad'a takemin " ta Kuma rushewa da sabon kuka, mk jin kukan yake yana ta6a masa zuciya a hankali yace "sorry beauty abbane ya kirani akan batun auranmu" da sauri ta bud'e manyan idanunta tace "me aure?"
"Sure beauty aure nakeso Kuma ke kad'ai na zaba zuwan da nai abbane ya kirani ko baki sonane beauty" ya karashe cikin wata mayaudariyar murya ,kamar zatai kuka tace "ni wlhy banason aure yanzu karatu nakeso nayi kawai Yar karama dani ban gama karatuba ace za,amin aure" mk ya saki wani murmushi yace "beauty wayace bazaki karasa karatun kiba? Na Miki alkawari kamar yadda Kika fara Zaki gama karatunki lfy nima inaso naga matana da ilimi me zurfi" tunda ya fara magana sai yanzu ta saki murmushi ta zauna akan Kujerar a hankali tace "da gaske kake sir?" Gyad'a Mata kai yay yana jifanta da wani kallo yace "sure beauty yanzu kin amince Zaki aureni" boye fuskarta tai ta ringa murmushi kasa kasa ita kanta in tace batason mk tayi karya batasan lokacin da sansa yay Mata mugun kamu ba ,kasa magana tai ta ringa wasa da zoben hannunta ,leko da kansa yay daidai fuskarta Yana Mata wani kallo,da sauri ta juya a shagwa6e tace "sirrr" saida yaji tsikar jikinsa ta mike saboda yadda taja sunan a kasalance yace "yes ma'am" turo baki tai tace "zan shiga gida aunty tana jirana" langwa6ar da kai yay yace "kin gaji danine beauty?  ok ki gaishemin da auntyn bye" bata Kuma cewa komai ba ta wuce ya bita da kallo har Saida yaga ta shige apartment d'insu sannan ya sauke ajiyar zuciya ya wuce ,still suka Kuma had'uwa a parking space da haydar yana zaune akan motarsa ta gefen ido haydar ya kalleshi kafin ya Mika Masa hannu a takaice sukai musabaha kowa ya janye hannunsa cike da basarwa,
Mota ya shiga yay reverse ya fice daga gidan yanakan hanya hanny ta kirashi a speaker yasa wayar ya d'aga batare da yay magana ,"baby Ina guesthouse d'inka fa Ina jiranka" hanny tace cikin wani salo daya Kara kashe masa jiki dama tunda ya rike hannun hanna ya nemi nutsuwarsa ya rasa a kasalance yace "ina hanya" yana fad'a ya kashe wayar ya kara gudun motar,
  Da sallama ya shiga bedroom d'in mami tana zaune kan dadduma tana karanta azkar zama yay akan gadonta harta kammala ta juyo tana kallansa tace "haydar "
Dagowa yay ya zuba Mata ido yace"mamii akwai abinci?"
"Eh yana dinning na jera maka" mamii tace tana linke dadduman datai sallah da ita, "ok thank u mamii" har yakai kofa mamii tace "ka had'u da wani saurayi a waje?" Tsayawa yay ya juyo yace "eh mun had'u" mamii tace "to saurayin hanna ne dafatan dai Kun gaisa" Mami tace tana tsurawa fuskarsa ido taga reaction d'in da zai nuna sai dai ko kusa bataga komai ba sai ma cewa yay "ok Mami" da kallo mamii ta bisa cikin takaici harya fice,
A dinning ya zauna ya zuba abinci kad'an yasa cokali sai dai ya kasa kai loma d'aya bakinsa Sai juya abincin yake daga karshe ma rufe abincin yay da wani plate ya fice daga gidan baki d'aya yawo ya ringa yi yana zagaye gari daga karshe wani park ya tsaya ya fito yana tafiya a nutse wasu kujeru daba kowa ya zauna ya d'ora kafarsa akan table d'in dake wajen ,ma,aikacin wajen ne ya karaso yace "yalla6ai a me za,a kawo ma?". "drink da snack" yace a takaice,ba,a jimaba aka kawo Masa ya biya kudin, zama yay yana danna waya unexpected yaji ance "hiii man" basai  ya d'ago ba dan tuni ya gane muryar wace ,
  Tamke fuska yay ya d'auki tissue yanacin samosa tamkar baiji taba, Kujerar da ke wajen taja ta zauna had'e da sallama sai sannan ya bud'e baki da kyar kamar ammasa dole ya amsa ,
Murmushi siyama ta saki ta d'auki samosan da ya ajiye takai bakinta inda ya gutsura tace "ajikina naji alamar kana wajannan ina zaune naji Ina Sha,awar zuwa nan ashe zanyi gamo da sanyin idaniyata"  shidai baice komai ba sai wayarsa da yake dannawa siyama ta kar6e wayar ta marairaice fuska tace "man ka d'ago ka kalleni mana ko zanji dadi" mukullin motarsa ya dauka dake kan table d'in ya mike kallo d'aya yay Mata ya d'auke kai yace "bani wayata" make kafad'a tai tace "ah ah saika tsaya mun gama magan,,," tun kafin ta karasa ya wuce ta bisa da sauri harta karasa inda yay parking ya bud'e motarsa yana Shirin tadawa ta fad'a motar ta ajiye wayar akan cinyarsa tana murmushi tace "bukatata ta biya tunda har nai gamo dakai nakumaji muryarka mai sani nutsuwa na tabbatar yau zan karasa wunina cikin farin ciki da annushuwa ,"  fita tai daga motar ta zuro da kanta ta glass tace "Ina sonka man,bazan ta6a daina sonkaba bazan taba rabuwa da Kai ba" tana gama fad'a  ta wuce
Fizgo gyalanta yay a fusace dama kiris yake jira yace "ke wace irin mayyace siyama na biyo miki ta lallami bakiji ba ko,zan fara nuna miki asalin waye ni tunda bakyajin magana ina d'aga miki kafane a matsayinki na mace me rauni bakya ganewa ko" ya karashe Yana aeka Mata wani mugun kallon daya tsoratata,mayafin nata ta janye ta juya tana kokarin maida hawayen idonta ya bita da kallo kafin ya fice daga wajen da gudu yana sakin tsaki da karfi,
  Washe gari a fusace yaje office fuskarsa ba alamun fara,a a tattare da ita,tun daga yadda yake tafiya zaka gane akwai fushi a tattare dashi ,leemat data riga tai kwantan bauna a office d'in ta dinga leken zuwansa tana hangosa ta daka tsallen murna tana juyi shu,umar humrar data kashe kudi sosai ta siya ta shafata da yawa a jikinta yana turo office d'in ta saki wata Kara ta daka tsalle ta dane haydar ta cikwikwiye jikinsa tsam tana "wayyo Allah na a taimakamin " cikin tafasar zuciya ya finciketa daga jikinsa yay wurgi da ita kanta Saida ya daki jikin bango ta fasa kara cikin tsananin azaba mikewa tai cikin tsananin azaba da rad'adi ya Kuma kifeta da wani mari ,tuni jinta da ganinta suka d'auke na wucin gadi ta kasa kuka sai ajiyar zuciya da take,
  Bai sake kallan inda take ba ya ajiye briefcase d'in sa yana huci tsawa ya daka Mata a fusace yace "ke wace irin dakikiyace da zaki had'a kazamin jikinki da nawa?" Jikintane ya fara wani karkarwa cikin rawar baki tace "wlhy sir toilet d'inka nake wankema naga wani abu me kamada miciji shine na taho da gudu bansan ka taho" ta k'arashe tare da fashewa da kukan azaba data kasa, shiru yay bai sake cewa komai ba jin kukan nata yana damunsa yace "out" da sauri ta fice har tana tuntu6e kamar zata kifa, toilet d'in ya shiga ya gama dube dubensa baiga komai ba daga karshe fita yay daga company baki daya sbd mayataccen turaren daya fara kashe masa jiki .

HannahWhere stories live. Discover now