SHAFI NA D'AYA

3.5K 228 12
                                    

  *TSINTAR AYA*

*BILLY GALADANCHI*

*Bansaniba ko a wannan lokacin alk'alamin dana d'aga ze samu daidaito a tsakiyar zuciyar makaranta litattafaina tsofaffi da wanda zasu fara a yanzu! Abu d'aya na sani shine tabbas wannan salon daban yake, wannan salone me tsawon tafiya kana kuma salone da ban tab'a zuwar muku dashi ba. Ban shirya siyar muku dashiba, haka kuma bazan sayar d'inba, littafin kyautane babu tantama. Maganar dazan fad'a kai tsaye anan itace Akwai kalmomin dake jingine da nauyi acikin su, musamman awurin yaranmu, salone daze amfani kowa anawa ganin, amma ina roqon alfarma awurin yara su jingine wannan amfanin zuwa lokacin da karanta littafin ze amfane su.*

*Babu batsa aciki, sedai kamar yanda na fad'a kalmomi da abubuwa masu nauyin d'auka, banida hanyar sakaya kalaman masu jingine da nauyi abayansu, sedai inshaa Allahu zanyiwa kalaman kwaskwarima daidai da sakaye zuwaga zallar batsar.*

*Ban saniba ko zakuyi farin ciki da hakan, amma saukar kowane shafin zezone bayan na ajiye wanda ya gabacesa da kwana biyu, ina fatan hakan ze dawwamar da farin ciki a zukatanku masoyana.*

*A nawa b'angaren ra'ayi kuwa strictly matan aure zallah.*

*Tukuici zuwa gareki k'awata Ayusher muh'd, Alkhairin Allah ya kaimiki a duk inda kike, Allah ya d'auka kaki ya raya miki zuri'arki,yakuma albarkace su fiyeda iyawarki. Son so fisabilillah.*
           
*SHAFI NA D'AYA*

      Duk yawan mutanen dake bayansa suna k'ok'arin ganin sun take gabansa da bayansa hakan yaci tura, sabida yanayin sauri da Hamood keyi, saurin kuwa tamkar ze tashi sama haka yakeji, sabida lokaci zuwa lokaci yakan wurga kallonsa zuwaga agogon hannun sa yana me k'ara sarrafa k'afafunsa zuwa ga d'an sassarfa, tafiya dabata wuce ta mintuna uku ba ya sauya akalar k'afan nashi daga sassarfa zuwa d'an gudu lokaci d'aya yana tattare hannayen rigar sa zuwa sama. Mabiyan nasa ma gudun suka soma tamkar wasu zararraru haka suka dawo acikin fadar kowa se kallon su yake ido k'asa sabida sunsan halin Hamood yanzun nan zece kana kallon sa kai munafiki ne. A sukwane suka k'arasa cikin fadar, a tsaitsaye ya taradda d'aukacin dattawan fadar da kuma  masu babban muk'ami acikin fadar kamar su waziri,sarkin yak'i, Magatakarda da sauransu.Dukkansu sunyi layi gefe da gefe sunbar fili a tsakiyar su inda dagacen zaka hango me martaba a zaune saman wata kujerar mulki ta alfarma wacce aka k'era da zallan ruwan zinariya rubuce a saman ta an rubuta Daulatul Dinar! Be wani b'ata lokaci ba wurin k'arasawa kusa da me martaba lokaci d'aya ya sunkuya yana nuna alamar gaisuwa amma bakinsa be motsa ba babu kuma alamun ze motsa d'in! Kallon k'ur me martaba ke masa na wani lokaci yayinda wasu lafiyayyaun mintuna goma suka wuce amma har lokacin Hammood be gayar da Mahaifin nasa ba! gyaran murya murya Me martaba yayi inda sabo ya saba da halin Hamood d'in, wasu 'yan dak'ik'un seconds suka shud'e kafin yace.

"Hammood Menene dalilinka na kawo 'yan mata acikin fada? kana sani kuwa cewa hakan babban laifine da wannan masarautar bazata iya gafarta maka akanshi ba!Idan kana wajen masarautar kayi abinda kakeso mahaliccinka na kallon ka. Amma anan bazamu lamunta ba, sabida haka daga yau karna kumajin makamanciyar wannan halin a fadar nan" Shiru wurin ya d'auka na wuccin gadi, tsakanin mintuna da dak'ik'u an samu shud'ewar kusan minti talatin amma be motsa ba be d'ago kansa ba bakuma ze motsa d'inba kamar yanda koda ba gaskiya bane baze tab'a iya musawa ba. Shirun dayayi yawa ne ya sanya Me martaba cewa dashi

"You are dismiss" Be jira komai ba a sukwane ya mik'e tare da k'ara sauke kai k'asa alamun girmamawa sannan ya juya a hanzarce kamar yanda yazo yana shirin barin wurin kusa da galadima ya tsaya suka kalli juna, lokaci d'aya galadima ya d'auke kansa shikuwa seda ya gama k'are masa kallo sannan ya wuce cikin hanzari.

     zuwa wannan lokacin gudu yakeyi amma idansa duka biyu a rufe yake, yayinda mabiyansa ke biye dashi cikin tashin hankali. Timing dama yake sabida haka adaidai sanda ya iso inda yakeson tsayawa sekuwa ya tsaya d'in yana mayarda numfarfashi sama sama, Babban cikin mabiyansa ya kalla sannan ya d'aga hannu ya masa nuni da cewar ya bashi biro da paper. Atake jikin su duka ya mutu dan kuwa sunsan an tsokano musu yau, a hanzarce ya rubuta

TSINTAR AYAWhere stories live. Discover now