SHAFI NA TARA

1.2K 101 4
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*


JOIN OUR TELEGRAME PAGE TROU THE LINK BELOW.
https://t.me/joinchat/WVNVv7LzJdo-DIjC

*ASSALAMU ALAIKUM, INASO NAYI AMFANI DA WANNAN DAMAR WURIN MEMAN YAFIYAR DUK WANDA WANI ABU YA TAB'A HAD'ANI DASHI A MEDIA, DA WANDA MUKA FADA, WANDA NA ZAGESU A BAYANSU, WANDA NAYI GULMANSU IDAN MA NAYI, WANDA AKACE NAYI GULMANSU KODA BANYIBA,WANDA KE GANIN NA HAD'ASHI FAD'A DA WANI, WANDA KE GANIN RASHIN ADALCHINA, KAI DAMA WANDA KODA SUNANSA NA AMBATA A BAYANSA,DAN ALLAH YA YAFEMUN, ANATA MUTUWA BANNASO IN MUTU DA HAKK'IN KOWA AKAINA, NIMA NA YAFEWA KOWA DA ABINDA KAMUN INA SANE DA WANDA BAN SANIBA DUK NA YAFE, ALLAH YA SANYAYA ZUCIYAR DUK WANDA NA ZALINTA YAJI YA YAFEMIN HAR ZUCIYAR SA AMEEN. SAK'O BILLY GALADANCHI.*

     *SHAFI NA TARA*

Be gama zama a parlon ba ta Barra ta shigo, a hautsine kallon sa tayi

"Meya sameta? K'ureta yayi da ido amma bece mata komai ba, kallon mahaifiyarta tayi

"Ammu Bahar, meya sameta haka? Yatsine fuska tayi

"Daga sama aka jehoki ne? Cikin damuwa tace

"Ammu dan Allah meya faru, koda yamun sak'o ina kan hanyar zuwa nan d'in dama"

"Yarinya sekace mahaukaciya Barratu, iya hege kala kala, abinci anbata ta dagula wuri, se sakalci wai dan an mata fad'a taketa kuka daga k'arshe segata tana fad'awa ajikin Hammude nace wannan wai salon son a la'anceka ne kaga laifin mutane" Nisawa Barra tayi

"To Ammu seme kuma ya faru?" Tab'e baki tayi

"Suma tayi hakanan kawai, shine sarakan tausayi ya rud'e dukya fita hayyacinsa, amma na kula tana numfashu ta dawo hayyacinta kamar baccine ya kwashe ta" Jinjina kai tayi

"Abinda Jay yace nazo na miki bayani kenan akan yarinyar nan Ammu, batada lafiya akanta, anan aka rasa meya fad'ota daga bene ta buga kai, shine ta samu cutar irin ta tab'uwar wani b'ari acikin kanta da wasu lokutan kawai seta sauyin abubuwa irin na yara, amma zaki iya wuni da ita koma kwana biyu abun be tashi mata ba, sabida haka dan Allah Ammu kiyita hak'uri da 222,idan ana hantarar ta inji likita setayita samun attack irin na suman nan, kuma idan har yaci gaba wata rana idan ta suman bazata sake farfadowa ba se mutuwa"  Wara ido Bahar tayi

"Yau naji labarin Assha, anan gidan haka ya faru? Nan dai barra ta kwashe komai ta gaya mata har rashin lafiyar Hammude da aketa b'oyeta, anan Bahar ta fahimci tabbas gadar zare ake shiryawa Hammuden ta, sedai ita sam bata zargin yarinyar, duk yanda akayi wasu ne suke bibiyar ta ya ceceta, tinda har aka ganta da wuta me alamar k'arfe da zane ajiki, wama ya sani ko 'yan yankan kaine sukaso su hallaka ta ? Cikin nutsuwa ta kalli Hammood tace

"Hammude nasan kana jina, dalilin dayasa nayi kiranka anan dama shine in gaya maka, tafiya dai dazakayi America k'afata k'afarka, kana cika son sanya damuwa aranka kuma ni dama nagaji da zaman fadar nan, kasan halina batun yauba tun zamanin da banason takurar da akewa matam sarki, inaso inje ind'an sha iska inke d'ebe maka kewa, to amma wannan maganar da Barratu tazomun da ita akan maganar baiwar Allah cen ta sanya na sake shawara, ni dakai dakuma yarinyar nan atare zamuje America, dole semun nema mata lafiya acen d'in, lakurarta a hannunmu ya sameta dan haka ka shirya tafi banda bayi harmu biyun, akwai wasu bayi guda biyu dasuke b'angaren ka mata ina yabawa da kokarin su Barira da Amina dasu za'aje, Hammude banasanjin kamun gaddama munsan halin juna ai" Jinjina kansa yayi sannan da hannu yayi mata alamar aiba matsala, yazone ya gaya mata zeje wurin waccen yarinyar daze aura me martaba yace yaje gobe, to yau zebar garin sabida nisa inyaso ya isa gidan nasu gobe" Rabin rayuwar Hammude yayita ne awurin Bahar, lokacin kawunsa Jay shima hannun Bahar yake duk yanda yake magana ta fi k'owa k'warewa a wannan fannin,batace komai ba se jinjina kanta yaci gaba

TSINTAR AYAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt