SHAFI NA TALATIN DA BIYU

701 112 9
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

   *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA BIYU*

32.

  Tsoro me tsanani ne ya kama Hafsat yayinda Data yace yana kallonsu a firgice, wannan harbin daya shigo ta window yabi, ginin bullet proof ne, harsashi bata iya huda ginin da kuma k'ofar sedai window d'in shi d'inma dan yana a bud'e ne, maza ku kowa daga kwance ya rerafa zuwa b'arin da ba window ku rab'u da gini" Ba musu aka soma gungurawa se Hafsat data kafe da hannun Mood dabesan me ake ciki ba yana zube a sume, Data ne kinkimesa ya kwantar dashi gefe take ya zari bundiga ya lab'e jikin window ya soma musayar harsashi dasu, inda yayi nasarar harbe bakwai daga cikinsu, uku tsuka gudu, har wannan lokacin Mood be farfad'o ba, Hafsat se kuka takeyi nak'in k'arawa tana jinjigar yayan nata dake tsananin bata tausayi, tare da ganin cewar tabbas ayau rayiwar ta ta k'are, sabida inba yanzu ba bata tab'ajin k'arar bundiga haka kamar saukar aradu ba se a film, ilahirin duniyar ta seda ta gigita, ganin komai ya lafa ya baiwa Data damar kiran waya police suka cika gidansa, sannan akayi k'ok'arin farfad'o da Mood, bayan ya farka aka kaishi d'aki yaso sosai barin gidan amma ina, Data kyakyawan tsaro ya tilasta aka baiwa gidan sannan ya fita farautar 'yan iska.

     Jay zirga zirga yake a tsakiyar d'aki tamkar me yunk'urin nak'uda ilahirin jikinsa kuwa rawa yakeyi na yanda aka kama yaransa bakwai, dan an tabbatar masa dukkansu ba harbin mutuwa aka musu ba, maharbin k'wararre ne, idanda ze samu dama daga asibitin ze sanya a hallakar dasu gaba d'aya sabida gudun karsu tona masa asirin sa, tayaya abubuwa zasuke tab'arb'are masa kamar daga sama? Komai ya nemi muhalli ya darb'e wuri d'aya se jagulewa al'amura suke wannan wace irin rayuwa ce ta rashin 'yanci, tayaya Mood ze rayu da kwnan tonon asirin sa? Menene matsalar wannan tafiyar wai, wayarsa ya zaro ya danna kiran wata lambar kafin yace

"K'afa ya zakamun haka? Na sanar dakai ilairin gidan ku kashe su, Mood da Hafsat gaba d'aya inso samune a biznesu a gidan, yaya labari zezomun mara dad'i akan sun kasa? Cikin murya irinta 'yan daba K'afa yace

"Kad'an d'agamun k'afa me gida, wannan aikin daka bamu na kasada ne gashi ko kud'in k'warai ma baka biyamu ba, tayaya zaka tursmu gidan Detective gaba d'aya harsashi baya b'ula ginin gidansa, yanzu mekenan ka mana? Asaran Harsashi kokuma hasaran yaran aiki? Nazan d'agama k'afaba, duk yaro d'aya daya shek'a lahira akan wannan mission d'in sena huda cikinka da alburushi alk'ur'an" Cikin d'aga murya  yace

"Kai har ka isa in fad'a ka fad'a, ni zakayi musayar yawu dani kaiga d'an jagaliya ko, daga kai harsu babu wanda ya isa wlh, sena girgiza tarihin kafuwar k'ungiyar ta addancin ku" Dariya irinta 'yan daba k'afa yayi kafin yace

"Kai bud'a danla gafara, ni zaka gayawa rashin suma aka?! Nafika jin tsinin balaga wlh tatas zan kwaye maka aiki, kasan fa sirrikanka a tafin hannuna suke ko? Kawai ka kiyayi kwayewar bayanka a hannuna, banza dako zuri'arsa be ragawa ba d'an ragga kawai! Yana kaiwa nan ya kastse kiran tare da cewa

"Ni Ranka ya dad'e zewa wowta kirawomun wannan Detective d'in sanar masa cewar K'afa ne zanzo muyi magana akwai aikin bud'a k'afa zan bada kai ne" Da mamaki yaransa me suna karan d'ori ya kallesa

"Oga anya haka zamuyi kuwa? Sosa sumar kansa yayi

"Gaba d'aya tun mutuwar d'an haza da kuma jikan malam na tsorata da harkar nan karan d'ori, kawai gwanda mu d'aga k'afa zamufi samun sassauci" Girgiza kai yayi shima cikin gamsuwa "Se Oga, hakan ma yayi sosai muyi hakan bara a masa waya kawai"

******************
   Baya baya Barra tayi zuwa d'ayan d'akin tana sauke numfarfashi masu nauyin d'auka, gaba d'aya aduk halayyar Jay wannan b'anagaren ne bata yarda dashi ba, duk iyakar bayanan da Hafsa take mata duk tayi bincike tabbas hakane amma kisa, mijinta? Koda baya son nata kamar aka fad'a mata auren manufa yayi da ita bata kawo ze iya kisa ba, bare rayuwa ba d'aya ba, bazata iya bari wani yaji wannan maganar ba, zata rufe asirin Jay har k'abarinta bayan ta tallafi Family d'inta, wata zuciyar ce take raya mata taje tayi masa maganar kanta tsaye, amma tana tsoron abinda ze biyo baya a duniyar ta idan har Jay yasan cewar tabbas tasan bad'inin zahirinsa! Kamar daga sama ta ganshi akanta, hakan ne ya tsanantawa k'irjinta dokawa, mik'ewa tayi duk yanda taso adane bayanan sirrin dake zuciyar ta hakan seyaci tura dan kuwa firgici sosai ya nuna a fuskar ta, wanda baze tab'a b'oyuwa ba awurin mutum irin Jay da kamar shine ya raineta, gaba d'aya halayyarta babu wacce be sani ba. Takunsa ya k'arawa tsayi zuwa daf da ita yanda xuciyarta ke lugude kana jiyo sautin bugun numfashinta dukda k'arar na'urar sanyaya d'aki dake d'akin, tafukan k'afarsa duka ya d'aura akan k'afarta kamar yanda sukeyi a duk sanda zasuyi wata mu'amalar aure dake riskarsu daga tsaye, jikinta ne ya tsananta rawa gumi take har akan fuskar ta, d'age k'afafunsa yayi ya tura a k'ark'ashin nata ganin batada shirin yin hakan kamar yanda ta saba, sosai ya d'ageta sama ya kai hannayensa ya rik'o fuskarta sannan ya soma goga tsinin hancinsu wuri d'aya lokaci d'aya yana mata lilo tubda ya d'ageta da k'afafuwan sa, cikin wata murya dabata tab'a sanin Jay yana ita ba me razanarwa tare da nuna rashin imani k'arara yace

TSINTAR AYAWhere stories live. Discover now