SHAFI NA ARBA'IN DA ƊAYA

685 76 9
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOƘ

    *BILLY GALADANCHI*

        41.

Gaba ɗaya a wannan daren Hafsa kasa bacci ta yi, haka nan ko madarar  shanun dake bata kuzari bata nema ba, tuwon Dawar ma batako bi ta kansa ba, daga ɓangaren Bahar aka kawo mata kuwa. Wayewar gari seta tashi da azababben ciwon kai, da ƙyar ta yi sallan asubahi anan ta kwanta wani nannauyan bacci ya kwashe ta.

   Gaba ɗaya daga kammala cin abinsa baƙi yaƴi a part ɗinsa, bashi ya samu zama ba se bayan isha, ya gincira a saman sopa ɗinsa take agun bacci me nauyi yayi awon gaba dashi, bashi ya farka ba se 7 na ssfe, a gaggauce yayi sallah sannan yayi wanka da jallabiya ya buɗa a guje dama gudu ba wani wahala yake masa ba, kai tsaye part ɗin Hafsa ya nufa. Zazzafan kishi dabatama san tana dashi ba ya haddasa mata zazzafan zazzaɓi, shigar sa ɗakin da sallamar sa be tsaya komai ba inda take kwance akan carpet ya nufs ya ɗago kafaɗun ta sabida tun daga ƙofa kana jiyo sautin numfashin ta sannan se rawar ɗari takeyi, jin jikinta da zafi sosai ya sanya da hanzari ya rabata da hijab ya shiga jere mata sannu, amma se baccin wahala take da yunwar masifa data addabe ta, kan gado ya kaita sannan da sauri ya fita wurin hadiman ɓan gare, kitchen ya nufa dan acen yake tsammaninn ganin su. Yana isa suka zube suna kwasar gaisuwa, be amsa su ba yace,

"Tun Yaushe ne Hafsa batada lafiya kuma me tace yana damun ta? Kallon juna sukayi sannan da ƙyar ɗayar tace, "Sanda kuka shigo a tare jiya shine ƙarshen ganinmu da ita, tuwon ma da aka saka mata bata fito taci bs har yau, dabinon ma mun ɓare ƙwallayen amma bats fito ba" Cakuɗa fuskar sa yayi tamau cikin masifa yace

"Ita Sarauniya Hafsa, itace kuke jiran ta setazo tace ga abinda takeso? Rabon daku ganta tun jiya wuraren la'asar and baku neme ta ba, gayamun ma kuke cewar bats nemi tuwo ba kuma ku kun kammala amma baku kai mata ba. Yaushe gidan sarauta ya zama haka? Hafsa saraki ce fa! Jikinsu ne ya ɗauki rawa yayinda shi gaba jikinsa yafi nasu rawa tsabar ɓacin rai "ku fita daga part ɗin nan kuje waje ku jirani, badai da yunwa kuka barmun itaba ba wata kulawa, ƙarshen wata a biyaku sannan a ciyar daku ga wurin kwana me kyau. Haƙuri zasu bashi ya daka musu tsawa sannan ya buɗa fridge ba komai se fresh milk da yghurt. Su ɗauka ya nufi ɗakin, kanta ya ɗago ya tace ta, gaba ɗaya yunwa ce asalin ciwon ta seko kishi, batayi musun shan yoghurt ɗinba tuleliyar roɓa ɗata ta shanye tatas sannan ta lafe a jikin sa. Sai dai me wani amai ne ya taso mata dik yanda taso ta hanawa aman nan zuwa seda yaci ƙarfin ta, gaba ɗaya seda ta wanke jikin sa da nata da aman yoghurt ɗin da yanda ya shiga haka ya fito kawai zafine ya ƙara a maimakon sanyi, a galabaice taje ragwaf, cike da tausayi yace

"Damsel meke damun ki? Menene damuwarki baki gaya mun ba, mesa bakya cin abinci? Nashiga uku ni Hammood" Wani aman ne ya taso mata tasoma yunƙuri ba ƙaƙƙautawa amma ba komai acikin ta, toilet ya kaita atare ya musu wanka sannan ya dawo da ita, doguwar riga kawai ya zura mata shima ya duba kayansa a ɓangaren ya samo shirt ya saka ds jeans. Kwanciya tayi har lokacin yunƙurin amai take amma ba komai acikin ta, gaba ɗaya ruɗu ya shiga ya zauna ya rasa me zai yi se sannu yake jere mata. Da ƙyar ta buɗi baki tace,
"ka kaini wurin momy na ko Bahar, mutuwa zanyi" Hankalin sane ya kuma tashi ya tallafeta gaba ɗaya,

"Damsel muje asibiti kawai, mesa kike wannan maganar wai? Bata bashi amsa ba, se numfarfashi take sama sama tamkar zata sheƙa lahira. Beko tsaya saka hijab ko ɗankwali ajikinta ba, haka ya kwasheta da gudun da har lokacin yana nan ajikin sa, se ɓangaren Bahar. Fadawa da kuyangi se kallon sa suke, Bahar se ganin su tayi tamkar anjeho su akanta ya zube Hafsa akan kujera,
"Bahar ki taimake ni, Hafsa cewa take zata mutu tana yunƙurin amai ba komai acikin ta, ance bataci komai ba tun jiya kuma bata fito ba se yanzu danaje na tarar batada lapia" kallon takaici Bahar tayi masa kafin tace "Ban gane ba? A gidan uban wa ka kwana kai ka barta ita kaɗai? Sanda bakanan anan take kwana, inacen ina murna kana kulawa da ita dik dare wahale take kwana ashe kai kana cen wurin waccen tsuntsuwar ka bar yarinya acikin sababin ciwo! Miƙewa yaƴi tsaye,

TSINTAR AYAKde žijí příběhy. Začni objevovat