SHAFI NA SHIDA

1K 99 8
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

*JOIN OUR TELEGRAM PAGE TROU THE LINK BELOW.*
*https://t.me/joinchat/FgfKMiS_mYc-DIjC*

*WATTPAD @68billygaladanchi*

*My Sunita this whole page is for you, nagode da tsaftatacciyar k'auna Allah yabar so ya nunamun aurenki.*

*SHAFI NA SHIDA*

"A parlon k'asa ya taddata a zaune da cup a hannunta da alama wani abun takesha, tsayawa yayi yana kallonta ita kuwa idanta yana kan tv zahiri amma a bad'inin ta wani abun ne daban a ranta, rayuwarsa  tana raya masa cewar yaje ya shak'o wuyanta seta dena numfashi, kamar ance ta waigo segata tana kallon sa, da fara'arta ta mik'e tazo daf dashi tace

"So nake inje inyi wanka aruwan sama, amma ba'a ruwan sama ya zanyi?" Wani irin kallon tsana ya wurga mata sannan ya janye jikinsa daga nata ya nufi sama, bin bayanshi tayi ta rik'e masa riga ta baya

"Dan Allah yaushe za'ayi ruwa, nace dakai so nake inyi shillalo na aciki" Hannunsa yakai ya bige mata hannu cikin fusata ya d'are matattakalar da gudu yanzu kam, shagwab'e fuska tayi wane zatayi kuka, shikuwa seda ya d'are sannan ya tsaya ya waigo yana kallon ta cikin wani yanayi mara misaltuwa tana abin yara tace

"Niko Niko banama sonka, idan kaga ina wasana karkazo kace ka sanni ma,nama gaya maka" Ta koma kan kujera ta zauna ta sadda kanta acikin cinyoyinta tanata k'unak'uni!!!

  Ameena ce ta kalli barira suka shek'e da dariya k'asa k'asa, Barira tace "Sabon salo gemu a kafad'a yarinyar nan fa da sabon samfuri ta dawo daga asibitin nan, batasan d'an kurma bane ba, zataci ubanta" Amina na dariya tace

"Bakisan iskancin datamunba d'azu ai, kawai basega yarinyar nan ta zauna duk ta b'ata wuri da soyayyen k'wai ba, kamar 'yar shekaru biyu fa, aikuwa na fakaicin ido na mammari shegiya, abinda yaban haushi ma shine yanda ta koma tana kuka tamkar wata k'aramar yarinya" Tsaki Barira taja

"Tsiya d'inkin ludayi, ni kuwa d'azu rok'ana tayi in kunna mata TV cikeda ladabi, nace a ina suka samo wannan wawiyar, wai a haka prince mood zata aura, Allah da farko naso sosai tabar gidan nan, naso idan Fada abinda suka soma yad'awa ya yad'u" Tab'e baki Amina tayi

"Dama ta koma gidan princess Barra niba k'aramin dad'i najiba, ko uban me tazoyi mana yau oho" Dariya Barira tayi me sauti

"Ameena sekinyi kyau da zama princess, kafatanin hadimai da bayin gidan nanke babbar suce a iya iya hege,idan yau ace ki zama sarauniya niko zanta miki bauta kodan indinga kallon yanda zakike yarfa mutane" Kan Amina ne ya kumbura tana wata tafiya tace

"Da kuwa tafiyana ma canjashi zanyi zuwa irin na Prince D'an galadima" suka kuma kwashewa da dariya  har suna tafawa...

        Wayarsa ya zaro a aljihunsa yana mamakin zuwanta gidan, wane irin behaviour ne haka yarinyar nan kanta d'aya kuwa, da sauri ya rubuta wa anty Barra message

"What is she doing here?"  Anty Barra tana zaune kusa da Mami suna magana da yaren kurame wayarta tayi k'ara alamar shigowar sak'o, a hankali ta d'aga wayar ta duba, murmushi tayi, gaba d'aya mur'add'en hali irin na kurma yana bata mamaki, tana tunanin amsar dazata bashi kawai wani text ya kuma shigowa

"She's acting wired! please take her away" Kallon Mami tayi damuwa bayyane a fuskarta, cikin tsananin damuwa ta soma mata magana

"Mamina wannan itace alfarmar dazakimun, ku baiwa yaran nan time, a k'alla 6 month or a year Mami, abin ze masa yawa wlh" Mami cikin fad'a ta soma magana da yarensu tana demonstration da hannu

"Da yasan ba auren yakeso ba meya kaishi lalata yarinyar mutane, Barra kinsan masarautar nan da idanduna dubu kunnaye dubu ko ina kabi kunne ne da ido caa a kanka, harse yaushe Hammood ze dena janyomun magana ina zaman zamana, tun yana k'aramin sa komai aka bud'i baki Mood baya koyi da galadima sam,  shi haka yaga anayi, shine d'an cikin gidan shine d'an gidan amma d'an rik'o yafika iya sarrafa masarautar ka, ni mulkin be damen ba, amma k'imana ya dameni, babu wani me martaba dazanje incewa wai a janye maganar auren nan amma  ke zaki iya zuwa da kanki" Dafe kai Barra tayi

TSINTAR AYAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt