SHAFI NA GOMA SHA UKU

1.3K 107 6
                                    

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

  *NA: BILLY GALADANCHI*

*SUMOOD TACE TANA GAYAR DA DUK 'YAN MATAN HAMMOOD, KU SANI ITACE UWARGIDA*

    *SHAFI NA GOMA SHA UKU*

Hada ido sukayi atake khairiyya ta wurgawa hafsat harara tana wani yamutsa fuska, hafsat mamakin duniya ne ya kamata aranta tace sabon salo gemu a kafad'a lokaci d'aya wani gajeran murmushi ya sub'uce mata wanda akan idan khairiyya, abun yayi matuk'ar baiwa khairiyya haushi uban me takewa dariya tana 'yar aiki? ita dai hafsat saukar da kanta kawai tayi asaman kafad'ar bahar tana turo baki irin na shagwab'abb'u, cikin kulawa Bahar ta kalleta tana murmushi

"Yarin yar nan idan mumaje k'asar nan naje na dawo za'asha fama, kefa sam bakya girma ko? k'ara turo bali ta sak'alo hannunta ya zago cikin na bahar sannan tace

"Ammu, bacci nakeji fa" Tab'e baki Bahar tayi

"Halin ja'irancin ya motsa kuma, se kace kina jinjira kina zuba wannan shagwab'ar dan kinajin bacci" Nan da nan idanta ya kawo ruwa

"Ammu nifa baccin gaske nakeji zo zan kwanta so nake nayi pilo da cinyarki" D'auke kai Bahar tayi, k'wallan idanta ya gangaro

"Ammu dan Allah fa" Sauke ajiyar zuciya Bahar tayi sannan tace

"Tozo ki k'arasani, ubanki yana biyana kud'in jinyar k'afana idan kika b'allani da sakarcin ki" Tana murmushi tana share hawayen ta

"Dududu how many kg nake waighying haba Ammu"

"Naji zo ki kwanta d'in" Ran Khairiyya ya b'aci gata ita za'a nunawa gata ita dakeda Annah, in yanzu takeson ganin Anna kuma ta k'irata a waya tace tanaso su had'u acen tanaga se hirgin Annah ya riga nasu U.S, d'an gajeran tsaki taja wanda Hammood ma ya jita sannan ta kawar da dubanta daga garesu a ranta tana zagin dukkan su, ita ko wannan tsohuwar bataga dalilin dazesa a had'o ta da itaba a rayuwarta gaba d'aya ta tsani takura, dagani seta dinga shiga hancin ta, sam ita bazata lamunci shiga hanci ba dan babu wanda take zaman sa.

********************
    Zaman shirun ne ya ishi Jay ya kalli Barra cikin kulawa da tausayawa yace

"Barratu" Ita kanta duk sanda taji Jay ya kira sunanta gaba d'aya kai tsaye haka ta tabbatar koma menene magana ce dake neman nutsuwar ta, cikin tausayin kansu ta kallesa, amma batayi magana ba

"Kiyi Hak'uri Barra, banaso ko kad'an na ganki a irin wannan yanayin, gabaki d'aya hankalina seyake tashi gani nake tamkar nine sanadi, Barratu da sam ba haka kike ba, kowa yasanki da walwala amma acikin shekaru biyun nan kinfi ko yaushe sauyawa, Barrana tamkar akan aurena da zulaiha ne kika shiga wannnan rayuwar"  Hawayen idanta ta share sannan tace

"Jay ba haka bane wlh, kawai tausayin mu nakeji, ka k'ara aure ma amma ace ko zulaiha shiru har yanxu ko b'atan wata bata tab'a yiba ya zanji nikuwa" Murmushi yayi sannan yace

"Barratu mufa shekaru goma kawai mukayi bamu haihuba, wayasan inda rabonmu yake? kika sani ko lokacine beyi ba? inaga wannan ai shiga hurumin Allah mukeyi kawai hak'uri zamuyi da kuma addu'a" Aman dataketa yi tun safe ne ya kuma taso mata da sauri ta mik'e tana dafe bakinta tayi hanyar toilet, this fast few day's yana ganin sauyi sosai a wurin Barra, meke damunta batason sanar dashi? ya rasa gane kanta kwata kwata, da sauri ya bita toilet d'in ya taimaka mata ta kuskure bakinta sannan suka dawo bed room d'in, kallon tsukakken waist d'inta yayi acikin rigar dake jikinta wacce tabi lafiyar jikinta gaba d'aya, Barra jiki ta k'ara haka ya ayyana a ransa tana tsaye tana shan ruwa ajikin bedside, zuwa yayi ya d'aura hannun sa akan waist d'inta

"Barratu meke damunki wai? Kallon sa tayi idanta yana lumshewa

"Bacci nake yawan yifa, nafi 3month ina fama da cutar baccin nnan aika sani ko? to yanzu ko kitchen nake a zaune ma bacci nake, daga tsaye gyangyad'i nake" Murmushi yayi

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora