SHAFI NA TALATIN DA UKU

721 115 19
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA UKU*

33.

  Kallon Hammood Bahar tayi yanda yake sauke numfashi sannan tace "kwantar da hankalinka zakayi na musu waya kamar yanda kace, kuma suna kan hanyar zuwa nan, idan yazo base muji daga bakin saba, na fad'a masa Tahir ya mutu kamar yanda  kowa yaji a fada bari yazo muji da wacce zezo kuma gaba d'aya na kasa aminta Jay ze cutar damu, nasan zuciyar sa ta rashin imani tun yana k'arami amma wlh na d'auka cewar Jay ze dena wannan mugun halin, nayi tsammanin irin tarbiyar dana baiwa Jay ta sanya rayuwarsa da tunanin sa komawa irin na mutanen kirki, ban zata cewar shahararren mugu bane ba" Cikin raunin Murya yace

"Banshirya tarbar wannan ranar ba Bahar, ban shiryawa aminta da wannan cin zarafin ba Bahar, gaba d'aya duniyata ta shiga d'imauta, ace wai Jay ne da kansa zeyi hayar mutanen dazasu kasheni Sarki, su kasheni har dake me muka masa? Sumar kansa ta shafa cikin kulawa

"Ka rabu da mutum Hammude, ka dena biyewa salihar zuciyar ka tuni dama cen Jay la'ananne  ninasan halin sa, tsammani nayi ya sanja, sabida daidai gwargwadon tarbiya na baiwa Jay ita, na tsaya tsayin daka seda naga ya dena nuna yawan sonkan nan dayake, dacin zali, yaudarar mu yayi ashe, niya mayar tsohuwar kawai" Runtse Ido Hammude yayi kafin ya bud'esu ahankali akan Hafsa sannan yace

"Ke bazaki ci abincin bane, kizo kusa dani ki zauna" kawar da kanta tayi sannan ta turo baki

"Bazan ciba, gidan momy zan tafi da wancen yazo an kamashi, kaji dai abinda ake shirin musu" Kallonta khairiyya tayi"wace momyn? Ta tambaya a tak'aice

"Momyna mana, tana cikin wani yanayi" Cikin takaici khairiyya tace

"Ke tsintacciyar mage har wata mommy c3 dake, ki dena alak'anta uwata da kanki dab bakuda wani had'i na jini, yarinya kin shigo rayuwata kinbi kin tattare komai kin k'wacemun, mijina mahaifiyata, dangin mijina gaba d'aya farin cikina ya dawo naki wlh senaga bayanki" K'ank'ance ido tayi tana me zubesu akan khairiyya sannan tace

"Baiwar Allah matsalarki ta farko itace mijinki, tuni ya sakeni saki uku sabida haka matsalar farkon ta kau, ta biyun itace dangin mijinki wannan kuma mune danni k'anwar sace ke baki isa ki karkare wannan ba, se matsala ta uku shine Momy kije da kanki ki sanar mata ta dena kirana 'yarta idan kin isa" Bahar ce cikin mamaki ta kalleta

"Kanki d'aya kuwa? Magana kike akan Hammude ya miki saki uku, wannan ai rainin hankali ne, a gidan wane la'anannen akayi haka bana nan? Sosa kai tayi

"Nidai Bahar karkiga laifin Yaa Mood nice da kaina na nemi sakin" kallon takaici Bahar ta wurga mata kafin takai mata duka a kafad'a "Shirmen banzan shirmen wofi, yanzu kuma damu zakiyi irin wannan wasan" Sosa wurin da Bahar ta doke ta tayi "Allah ba k'arya nake ba, cewa nace ya sakeni kuma ya rubutamun sakin har uku gama takardar  nan a hannun Yaa Sufyan da anty Laurah" cikin sabon tashin hankali Bahar ta kalli Hammude  "kai da gaske wannan tab'ararriyar take ka nuna hali irin na rashin daraja ka saketa? Kallon Hafsa Hammood yayi baze iya da rigimar Hafsa ba, ba yanxu yazo ta tashi fitina akan maganar sakin  ba, gabaki d'aya soyayi se komai ya lafa, gajeran tsaki yaja sannan ya dafe kansa, Cikin hikima Data yace "Bahar yanzu fa gaba d'aya ba'ason abinda ze tab'a lafiyar Hammood ki dena masa maganar sakin nan har zuwa gaba" Kallon su take atare inda lokaci guda ta harbo akwai abinda ake b'oye mata tabbas! Bata nuna damuwar taba taja bakinta ta tsuke zuwa lokacin da Jay da Barra suka k'araso wurin, Jay tin shigiwar su masarautar bega wata alama dake nuni da cewar sarki ya mutu ba, musamman da yake kasheshi akayi, kallon Barra yayi a lokacin suna daf da shiga babbar fadar inda akace suje yace

"Banaji nan akace muzo Barra, labarin daya riskemu sedai idan be riski masarauta, idanda ya riski masarauta da tabbas bazamu samu hanyar wucewa ba batare da munsha bak'ar wahala ba, da farko na yarda da kalamanki har cikin zuciyata amma zuwa wannan lokacin na soma fahimtar d'inbin wowtar dana aikata, ubanme kika kawoni nan amun keda tsohuwar uwarki" D'agowa tayi batare datace masa komai ba a bazata ta sanya gefen hannunta ta dire masa mugun duka a jijiyar mukwana lafiyar dake gefen wuyansa wacce atake tayi sanadin suman sa ya zube agun, kallon tsana ta wurga masa sannan da sauri ta janyo waya ta kira Bahar take su Data suka zagayeta akayi sama da Jay zuwa inda aka tanada domin sa, ruwa me sanyi akayi amfani dashi wurin farfad'o dashi inda yana farkawa yayi arba da Maryama tanata zare ido, Hafsa ya gani tsugune kusa dashi tana wani murmushi, tana binsa da kallon shak'iyanci tace  "Welcome back Jay, duk nan kai muke jira" Wani mugun kallo ya zuba mata ita d'inma shi take kallo, a k'ufule yace "Haka mukayi dake? Butulu kawai" Dariya tayi sannan ta mik'e daga durk'ushen datake ta nemi wuri ta zauna tace  "kai gaula ne, kai banza ne, kai jaki ne, akuya ma tafika wlh, inbanda kake dak'ik'in jahili se kawai dan zaka bani miliyan biyu in cutar da jinina, an gaya maka kowa irin kane? Koda yake na manta tsintacciyar mage, dama cen kutse kayi basuda wata alak'a dakai kazo ka nuna kai nasu ne kabi jikinsu kana ha'intar su" Zabura yayi maza suka rik'eshi ita kuwa tayi dariya  "Wannan ranar senakeji tamkar ina kallon wani series film ina nishad'i abuna, yauga Boss durk'ushe agaban actor, gaba d'aya bakada tunani kayi shekaru kana aikata sharri amma gaba d'aya bakada tunanin kanka, yau idan Maryama ta d'auraka akan hanyar datake so, gobe seka shiga k'walwar Barra ka mata dabara ta b'ulle dakai hanyar dakakeso, jibi kuma seka lula acikin idan fada ka nemo satar amsa, gabaki d'aya kai d'innan mutum mutumine bakada kai saina jibgar kaya kawai sakarai mayaudari" Kallon yanayin Mood keyi harta kai aya yayinda Jay yace yana zabure zabure  "karku yarda da  maganar ta, muguwar yarinyace na yadda na cutar daku amma dasa hannun ta" Matsawa tayi ta zare takalmin k'afarta ta kwad'a mai a baki seda ya fashe, dawowa tayi ta zauna kowa yana binta da kallon mamaki

"Idan bace ba kada basira kace gazance ga magana, kai bakasan me ake cewa Tit for tat ba? So kake kace ka fallasa sirrikan da mukayi dakai duk sunji audio ai, ba maganar sirri d'aya damukayi dakai dabanyi recording ba, da 'yar zamani kake magana, barin maka fashin bak'i cinikayya mukayi tsakanin bayanai, ma'anai na sayar maka da bayanai nima kuma na saya bayanai a hannun ka, banbancin mu d'aya ni na sayar maka iya wanda nakeso ka sanine kai kuma ka bud'en cikinka, ni banida niyyan cutar dakai amma kai so kawai kake ka kasheni waika ga d'an tab'ara, idan yarinta ce nafika jin k'uruciya ingaya maka, gaba d'aya kai bakasna yanda zaka tafiyar da rayuwar kabama bare ta wani" Yawu zubar jinin daya taru a bakinsa ya fito sannan yace yana kallon ta

"Idan nabar nan wallahi sena kasheki" Dariya tayi "bakada hankali uban waye yace dakai zaka bar nan, naso ace ni namiji ce dana maka shegen duka sekaci kashinka a hannu shashasha me kamada biredin tamanin, kanshi kamar murfin masai da ido fiki fiki tamkar agolan nufawa" Yanzu kam Bahar seda tayi dariya, yayin da Hammude ya k'ure hafsat da ido ilahirin motsinta burgeshi yake, she is a genius irin wannan ta sabu aiki a turai b'angaren intelligence tayi 3yrs ta dawo Nigeria seta iya bud'e aiki, batada kunya batada tsoro inama ace ze iya wlh saya rungume ta, tabbas koda baya sonta tanada babban matsayi a rayuwar sa fiye da tunani. Sarki ya fito yaci mutuncin Jay dukda bashida lafiya raunin hannun sa yana damunsa, atake aka had'a shedu aka tattare duk wani munafuki dake fada, abinsa ze baku mamaki rabin mutanen masarautar suna cikin k'ungiyar aci duhu, shiyasa ko kashi kayi se wani yaji!

   Hafsa batayi k'asa a gwiba seda ta kawo mommy masarauta, har part d'inta, khairiyya bak'in ciki kamar ya kashe ta, seda ta nutsu zuwa yamma sannan ta fita tareda guads zuwa inda ayatullahi yakai Bilal!!!

   Kallon kallo ake a tsakanin su ga Bilal a d'aure yanashan wahala, matsawa tayi kusa dashi tana wani murmushi seda ta rik'e kunkurunta tamkar bazatayi komai ba sannan ta zare hannun ta d'aya ta kai masa lafiyayyen mari cikin izza tace "Bilal wannan marin marine na yagalgala jikina dakayi a baya" Ta k'ara ware hannu ta sake masa lafiyayyun maruka guda biyu sannan tace "Billal wannan marukan na wulak'anta rayuwar 'yar uwata khairiyya da kayi ne" Ta k'ara ware hannunta ta zabga masa mari seda jini ya gwafce ata hancin sa sannan tace "Bilal wannan marin daka gani duk zafin sa nakai kanka inda Allah be kaika bane,ubanme kake a masarauta? Shida kanshi courage d'inta ya d'imauta shi, tana zare ido tace Ayatullahi mutumin nan ya gama goge komai na iskancin daya ajiye an tabbatar? Ayatullahi data gama burgeshi yace "yagama Hajiya Hafsa, yarinya me halin girma"
"Yauwa duka dukiyar sa fa, da gidajen da komai?" "Suma duk an had'a komai yana nan" muemushi tayi

"Akan tunanin dayake na yiwa mahaifiyata fyad'e shida yan iskan gari ayi masa sabuwar kaciya lafiyayya!! Akan hannayensa daya turbud'a acikin matancin Khairiyya a datse masa 'yan yatsunsa manunai guda biyu amasa dressing, kashiyar ma amasa dressing, idan angama akaishi bakin gari a ajiye ya jinyaci kansa, idan kazo ka warke sekaci uwarka ba momy naba Bilal, sannan seka d'aukaka k'ara, koda na kaika ga hukuma bulus zakaci nikuwa nayi alk'awarin ganin bayan jin dad'in ka na har abada, mugu kawai, idan zaku ajiyeshi a bakin gari ku bashi dubu d'ari yaja jarin tireda" Ayatullah yana dariya yace"kaciyar ta asibiti ranki ya dad'e kota gida?" Dikda taji nauyin maganr seda tace "Ayatullahi wacce tafi zafi? Yana murmushi yace "wanzamai tasu tafi kaifi tunda basa kashe ciwo hajiya Hafsatu" Murmushi tayi tanason mulki itakam "Ayi masa me zafin a kashe zafin wurin da turate da gishiri haka ake mana a k'auye, akawai tabon dake zaune a tafin k'afata sabida Bilal nima a bakin gari aka yadani" Jinjina kanshi yayi "Lallai Bilal beci yafiya ba" Juyawa tayi shikuwa Bilal ya soma magiya "Dan Allah Hafsat kimun rai, wlh na tuba, ki k'wace duka dukiyar amma dan Allah banda mazakutata" Murmushi tayi sannan tace "Dama ace nasan amfaninta dana bar maka, Allah yasoni batada darajar dazan raga mata akan ta" Ihu yahau yi tayi gaba abinta, Ayatullahi kuwa se murmushi yake, dama ashe akwai inda rashin kunya yakeda rana, kalli yarinyar nan gaba d'aya ta iya hukunci.

Mom Nu'aiym.

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora