SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR

1K 129 13
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*INA 'YAN KASUWA WANDA SUKA SHAHAR SUKE KUMA SON SU K'ARA SHAHARA TA FANNIN KASUWANCIN SU? TOKU GARZAYO NESA TAZO KUSA,DOMIN MUN SHIRYA TSAF DOMIN TALLATA MUKU HAJAJOJINKU AKAN FARASHI ME SAUK'I TA HANYOYI SADA ZUMUNTA NA YANAR GIZO DABAN DABAN AKAN FARASHI ME SAUK'I, NEMI WANNAN LAMBAR DON K'ARIN BAYANI..07084161619.

*Miss Hindu wannan shafin nakine, nani dad'in yanda kike nuna tsananin k'aunar ki agareni, Allah yabar zumunci*

*SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR*

25.
   Lokacin da likitoci sukazo d'akin da Hammood yake se suka tarar baya nan, abin ya matuk'ar d'aure musu kansu, gaba d'aya sun rasa tunanin ina zeje, har toilet sun duba baya nan, likitan cikin tashin hankali yace

"To ina zeje? Shida yakeda rauni? Yaushe ma allurar baccin ta sake sa? Karmu b'ata lokaci anan mu duba sauran patient d'in, Dr. Anwar kai seka duba mana patient relatives d'in kaji inda yaje" Juyawa yayi sukuma sauran likitocin suka juya d'akin me martaba nanma bayanan, hankali atashe suka juya d'akin Muhseen nanma bayanan, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana! Dr. Gaba d'aya jikinsa rawa ya d'auka ya rasa inama ze saka kansa, tomeke shirin faruwa? Idandai ba wani abu sukaji ba tayaya zasu bar asibiti acikin sirri kuma ba tare da kowa ya gansu ba? Kai tsaye office d'insa ya nufa ya d'auki waya ya kira Baba usman bayan sun gaisa yace

"Yallab'ai akwai matsala fa? Cikin tashin hankali Baba Usman yace "Matsala fa, Wacce iri kenan?"

"Gabaki d'aya munje muyi aikin allurar nan kamar yanda muka alk'awaranta dakai amma semuka tarar duk patient basa d'akunan su, kuma patient relatives sunce basusan yaushe suka fita ba, abun akwai matuk'ar d'aure kai" Cikin tashin hankali da d'aure kai  yace

"Wannan wace irin magana ce? Sekace wasu cinnaku ka gayamun duk baka gansu ba wannan maganar ai zancen wofi ne" Zufa Dr. Ya share sannan yace

"Maganar gaskia kazo da kanka ka tuntub'i relatives naku da kuka bari dakuma wannan fadawan da dogarawan, danni gaskia zan iya mayar ma da kud'ad'enka akan in shiga wata fitinar" Cikin masifa yace

"Deal.ya rigada ya k'ullu likita, zanzo inji inda suka tafi dai amma maganar mayar da kud'i batama taso ba, shin ku bakuda CCTV a d'akunan kwananku ne da waje? Cikin k'aguwa likitan yace

"Bamudasu, a main gate ne kawai akwai" Tsaki k'arami yaja kafin yace

"K'aramin asibiti kukeda kenan ba babba ba, bansan mesa me martaba yake zuwa asibitin kuba, koda yake dak'ik'in gaske ne shima" katse kiran likitan yayi kafin yace shi kad'ai

"Wannan mutumin inaga lauye aniyar sa zanyi, ban tab'a kisaba dama, inaga Allah ne ya taimakeni danya tseratar da rayuwarta daga fad'awa halaka, sabida aniyarsa ce zansa tabisa, wanda dik ze iya sanadin jininsa har haka tokuwa tabbas a dubawa rashin imanin sa"

*****************
   A station gaba d'aya hafsat be kawo wuta seda ta shafe kusan awa biyu a cell tana nazari kafin azo interogeting d'inta!!! Mutumin gaba d'aya wani irin mutum ne me tsananin cikar kamala da haiba, kana ganin sa zaka tabbatar wa kanka cewar wannan a k'ware a harkar sa, beyi mata kama da police officer me kaki ba sedai ko d'an sandan ciki ne, cikin dak'ik'a dabefi biyar ba ta gama karantar yanayin sa, katse tunanin ta yayi da cewar

"Sunana Sifeta Sufyan amma anfi sanina da Data, nazone in miki wasu 'yan tak'aitaccin tambayoyi akan wannan al'amarin daya faru, duba da yanayin shekarunki na tabbatar sakaki akayi" Murmushi kad'an tayi sannan tace

"Bazan baka amsa ko d'aya ba a yanzu malam Data, duba da yanayin shekarunka da wayewar ka na tabbatar kaiba jahili bane ba, dagani kuma koban tambaya ba na tabbatar cewar kai d'in nan kasan aikinka fiyeda tunanin me tunani, dan haka anan taimako d'aya zan maka sabida bazanso kasha wahala ba, ba wani taimako bane me wahala, da Farko.zan baka lambar wani wanda xe taimakeka ka samu amsar tambayoyin ka acikin sauk'i, kokuma zan baka dama ka gayyatoshi ayi komai agabana, na biyun sa kuma zan baka wani assighnment idan kaje kayi shima ze taimake ka" Langwab'ar da kansa yayi yana mamakin yarinyar kafin yace

TSINTAR AYAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz