SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

877 111 10
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

   *NA:BILLY GALADANCHI*

*Masu tambaya akan yanayin ciwon hafsat, tabbas ana samu, anyi a unguwar su antyna, nasan yarinyar kuma har yanzu datayi aure ta haihu befi idan abun ya tashi mata ba tayi wasan k'asa, idan fatan kun gamsu.*

*SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI*
17.
Seda suka zauna sannan suka kalli juna, gano yanayin cewar Hafsat bata cikin hayyacinta ya sanya Amina tace

"Kinji abinda naji kuwa? Kinga abinda na gani Barira? Kamar fa Prince Mood nagani tsage tsage yana magana da waccen nurse d'in ko" Ita kanda Barara mamaki bawai ya barta bane ba ta kalleta cikin jimami tace

"Amma ke Amina banace ki rabu da shiga shirgin Idan fad'a ba? Banace ki rabu da d'aukar muhimman maganganu kina gaya musu ba, ke yanzu 'yar wannan gulmar damuke a tsakanin mu bata ishemu ba sekin d'auki magana kinkai wa idan fada, kuma kina sane da cewar k'yas kawai suke jira kisa ma zasu iya yi" Turo baki gaba tayi

"Haba Barira ke sam bakya tab'a dubawa ci gabanmu koda wane lokaci ci bayanmu kawai kike kallo, a bauta zamu mutu? Iyaye da kakanninmu haka suka k'are suka auri bayi suka tabbata a bayin su, yanzu mu banbancinmu dasu d'aya shine munsamu mund'anyi makarantar bokon nan, a duk cikin fad'in fada gayamun idan ba idan fada ba wayake ta tamu? Magana idan kikaga sun mana toko tabbas aiki zasu sakamu, da gaske tona masa asiri zanyi kowa ya huta" Rik'o hannunta Barira tayi

"Kada kiyi haka Amina, nifa ina ganin ma kamar bawai magana yake mata ba, koke kinji sautin muryar sa, akan wane dalili ze dawwama da harshe me motsi yana dak'ushe tasirin sa, wane d'an adam ze tabbata kurma har'a wurin matar sa alhali yana magana, nida ina tunanin kawai motsi yake da bakinsa tunda kinga har hannun sama yana motsi, ta yiyu matar batajin yaren kurmanci, kinga dole yayi yanda zata fahimta" Shiru Amina tayi tana kallon yanayin Barira tare da tunanin kumafa hakane? Barira ganin Amina ta d'auki maganar datake gaya mata yasanya tace

"Idan fada ko jininsu basu ragawa ba bare mu, ya dace mu tabbatar dakoma meye kafin mu sanar dasu, bayaga haka yanada kyau sosai mu iya kame bakunan mu mu dena shiga sha'ani irin wannan daya shafi rayuwa da mutuwa, kiyi komai amma ki kiyayi d'aukan hakk'i wannan shine iyakar abinda zan iya gaya miki, idan kunne yaji gangar jiki ya tsira" Nisawa tayi

"Toni dana rigada nakira Baba babba yanzu inya kirawoni mezan gaya masa" shiru Barira tayi kafin tace

"Kice dashi kina tsammanin ciki ajikin amaryar prince" Jinjina kanta tayi alamun gamsuwa "Dama kuma kinsan suna tsammanin baze nemi mace ba"

****************
  Barra dai jiki yak'i dad'i, daga asibiti an kuma dawowa da ita gida, wannan karon da kanta take addu'ar neman mafita daga wurin Allah, tasani wannan wata ayace, watak'il sabida yanda take neman haihuwa ne ido a rufe Allah ya jarabe ta a yanzu kam gwanda mata lafiyar ta akan wannan bak'ar wahalar ga zullumin ganin kamar zata mutu. Sun dawo asibiti da kwana biyu lolacin cikinta yacika wata biyar ta haihu, haihuwar d'an tayi ba'ako gama halittar saba amma kana kallon jinjirin zaka gano cewar mace ce, shida kanshi yasha wahala ainun, kuma anan se jini yak'i d'aukewa baya dai b'ulala kaman da amma tas yak'i ya d'auke se wasa yake mata da hankali, hankalin uwarta ya tashi tashiga damuwa me tsanani akan rayuwar da Barra  take ciki, anan aka duk'ufa wurin karb'o mata magunguna da addu'o'i irin gargajiya tunda asibiti yaki yi.

    Tunda aka sallamo Hafsat asibiti abubuwan datake sunfi k'arfin tunani, gabaki d'aya be wuce ta zauna tayita gwab'e abinci a wuri ba kokuma, tayita surutai irin na yara, ko irin tabi'un yara, kuka ba komai bane akan tanason abu idan ba'ayi mata ba, ga Mood se b'oye b'oye yakewa Bahar bayaso tasan halin da ake ciki, kusan sati hudu kenan yana fama da Hafsat ga tsananin tausayin datake bashi, bahar naso tayi waya da Hafsat amma wayar hafsat d'inma tana hannunsa ya kashe ko school ta dena zuwa sabida yanayin ta. Yauma kamar ko yaushe yana zaune yana aiki a laptop dake gabansa, wani kamfani suka bashi aikin zanen tiles yake so ya kammala yaje yanzu takai musu yanada presentation ba, zama tazo tayi kusa dashi shiru kamar me nazarin wani abu,se cen kuma ta sanya rigarta abakinta tana tsotsawa, kallonta yayi rigar ma gaba d'aya be dace ta sanya shiba, ya gayawa Barira kuma take kula da ita tadena barinta tana sanya gajerun kaya tunda ba hankali bane akanta, yanzu ta yane rigar zuwa bakinta duk ga pant d'inta nan afili, kawar da kanshi yayi sannan ya mik'e daga wurin zuwa d'akin sa batare daya d'auki komai na aikin saba,ganin ya tashi a wurin ya sanya ta saka hannunta tayita dandanna lambobi gaba d'aya seda tayi erasing aikin dayasha wahalar yi wuni d'aya, koda ya dawo da sauri wurinta yazo ya karb'i laptop d'insa yana duba, a zuciyar sa ya soma ambaton Allah sannan ya juyo ya wanka mata mari, so yake ya taushi zuciyar sa akan karya ci gaba da dukanta amma seda ya shureta, da gudu ta nufi d'akin ta tanata zuba kuka me k'ara sekace ta goye, haka yabar gidan ransa a b'ace a dole ya lalubo zanen farko daya gama yace be masa ba ya nuna musu, ga mamakin sa se murna suke suka karb'a hadda k'arin kud'in aiki, yayi godiya sosai sannan ya wuce presentation shima na zane nez sedai wannan bedding company ne ke neman zanen sa yaje ya nuna musu tasa k'warewa danshi be tab'a zanen gado wa kampanin ba, bashi ya dawo gida ba se after 9, inda ya tarar da hafsat still tana kuka. Kuyangin ya tara shiba sabawa yayi da magana dasu ba, yarasa dalilin dayasa tunda hafsa tashigo rayuwar sa yake yawan son yayi magana, yanzu da wanne bakin ze tambayesu dalilin kukan hafsat gashi khairiyya tayi bacci, wayarsa ya zaro ya rubuta

TSINTAR AYAOnde histórias criam vida. Descubra agora