SHAFI NA GOMA SHA TARA

1.7K 153 19
                                    

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA TARA*

     Zaman fada ake cikin tsananin jin zafin juna, kowanne da abinda yake sak'awa aransa game da d'an uwansa, tsananin takaicin juna akeji a wannan zaman, gyaran murya Me martaba yayi sannan yace

,"Hammood ya bada sak'o a gaya mana ta hanyar kawun sa yana neman alfarmar a k'ara d'aura auren sa da waccen  yarinyar da abu ya had'asu a baud'e" Zabura magatakarda yayi sannan cikin girmamawa yace

"Ranka ya dad'e ayi haka? Kallon sa me martaba yayi sannan ya d'auke dubansa daga gareshi yace yana kallon Jay

"Menene kake tunanin ya dace akan wannan maganar, naso sosai hankalin sa ya soma kwanciya akan matarsa ta farko, banason rigima"  Zubewa yayi yana me bada girmamawa kafin yace

"Idan mukayi duba da yanayinsa na farko akan maganar auren zamu iya yiwa Allah godiya hakan yana nuni ne kai tsaye da cewar hankalin sa ya kwanta da iyalansa har yake sha'awar k'ari, dan haka ina ganin gwanda acika masa burinsa kawai" Magajin garine ya zube kafin yace

"Allah yaja daran sarki, banaji hakan tunani ne me kyau, idan har akayi hakan ita gimbiya khairiyya nasarautarta bazuji dad'iba sam, duba da cewar dududu auren nanfa ko wata shida be rufa ba"  Sarkin baka cikin girmamawa yace

"Mahaifin gimbiya khairiyya yasan da maganar ita wannan yarinyar ai, ai gata ya masa dacen farko kuma yanzu akan gimbiyar ai bazamu fasa cikawa yarima me jiran gado burinsa ba Allah yabaka nasara"  haka kowa da abinda yake fad'a akan maganar daga k'arshe Sarki yace zeyi tunani akai............
  
******************
       Yau Hafsat sun tashi a aschool kai tsaye Bus stop sukaje itada k'awayenta, tunda taketa wannan ciwon tadena yawo ma sam, tana nan zaune suna jiran isowar Bus se ganin Hammood tayi a gabansu, mik'ewa tayi ganin ya jingina da mota ta matsa kusa dashi, seda suka kalli juna na some seconds sannan tace

"Yaa Mood Barka da rana" kallon sa take yanda yake wani yamutsa fuska kuma ga mamakin ta seya motsa bakinsa amma ba magana yayi ba, hannu ya nuna mata ta shiga mota seda ta gama karantar yanayin sa sannan ta juya dayiwa cylia da chidi sallama ta bud'e gidan baya ta shiga, shi d'inma baya ya zauna ya janyo New's paper ya soma dubawa abinda yake shirinyi rayuwarsa banda harbawa babu abinda take amma duk yanda yaso yaji maganar Uncle Jay yau ji yake baze iya ba, shi d'inma namiji ne, ya mallaki hankalin kansa, yanada matuk'ar muhimmanci ya yak'i mak'iyansa, yanzune lokacin daya dace ya zauna acikin mak'iyansa ya dena tsoron su ya nuna musu iyakar su....A b'angaren Hafsat kuwa Allah ya halicceta da saurin karantar halayen mutane, indai har ta nutsu mutum ya nutsu tokuwa sedai idan bashi take kallo ba, amma muddin idanta yana kan mutum to kai tsaye zata iya karantar zuciyar sa akowane yanayi suke atare musamman idan akace idansu yana sark'e dana juna, a irin hakan ta karance Bilal tunkafin  ya bayyana manufar sa akanta, a irin haka ta karance halin da Bilal da momy suke ciki tun kafin ta fara jiyo sautuka muryoyin su suna shek'e ayarsu, a irin haka take janye jikinta daga duk wani me sak'a gadar zare iri biyu a rayuwar ta, Hafsa yarinyace da magana be wani dameta ba, amma tanada wayau fiye da tunanin duk wani me tunani, wayonta yakaita gacin nasara ta k'waci kanta a hannun Bilal! Wani mayaudarin murmushi ta sakarwa kanta tunawa da yanayin idan, labarin da zuciyar sa ke bata daban akanta amma idansa yana yawan k'aryata nazarin sa, zuciyar sa tak'i tsayawa akan cutar dashi zatayi idan nashi ma basu gama yadda da hakan ba, abinda ta lura dashi a yanayin sa na yanzu akwai abinda yake shirin aikatawa sedai ya gagara nutsuwa ya aikata koma menene, kawar da kanta tayi daga dubansa zuwa ga hanya taga gaba d'aya ba hanyar gida suka d'auka ba, wani siririyar dariya tayi me had'e da Hmm tana son wannan baiwar da Allah yayi mata, tana tsananin jin dad'i idan tayi karatun faifan fuska da zaren zuci ta canka daidai kanta har wani fad'i yake, d'agowa yayi ya kalleta idansu ya sark'e dana juna ko wannensu ya gagara d'auke idansa ana d'an uwansa har lokacin murmushi ne k'unshe a fuskar ta yayinda yake k'ara had'e tasa fuskar sa a zuciyar sa yanaji tamkar yarinyar nan ta gama raina masa wayau dariyar me take, k'ara fahimtar abinda yake tunani aransa ya tilasta mata k'arayin wata dariyar babu shiri wacce a wannan lokacin kasa hak'ura yayi ya damk'o k'aramun d'an k'walin data rufe kanta dashi me zubin hankici ya had'o tare da sumar kanta, idansa anata amma ga mamakin sa go gezau batayi ba, bata motsa ba, bata kuma nuna alamar taji zafin rik'on ba, d'auke nashi idan yayi anata sannan ya cillar da ita gefe yana jan gajeran tsakin daya fallasa tabbas harshensa yana motsawa ya kwantar da kansa akan jikin sit motar yarasa mesa hankalin sa yake yawan d'aukewa zuciyar sa bata masa sassauci akan kai hannun sa jikin Hafsa, besan wane irin k'i yake mata ba haka, koda yake shi halittarsa ce k'in duk wani mak'iyin sa indai har ya fahimci kai mak'iyin sane tokuwa tabbas shima daga ranar ya dena sonka har abada, driver daya gaji da shawagi dasu seyace

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 17, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TSINTAR AYAWhere stories live. Discover now