SHAFI NA BIYAR

1.1K 110 4
                                    

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

  *BILLY GALADANCHI*

Join my telegram page through the link below.
https://t.me/joinchat/FgfKMiS_mYc-DIjC.

*SAK'ON GAISUWA ZUWA GAREKI K'AWATA HAR ALJANNAH HAFSATUL ELHAM, INA MIKI FATAN ALKHAIRI ADUK INDA KIKE, ALLAH YA NESANTAKI DA AMINAI MASU FUSKA BIYU YAKUMA KAREKI DAGA SHARRIN DUKKAN WANI ABUN K'I....IYA WUYA K'AWAR ALKHAIRI.*

  *SHAFI NA BIYAR*

Rik'o hannunsa Barra tayi yana kuka tamkar k'aramin yaro, bata damu da zaman likitan agun ba ta runguneshi gaba d'aya, daidai saitin kunnensa take rad'a masa

"Calm down mana heroin, ban sanka haka ba, karka yanke kowane hukunci acikin fushi, nutsuwa zakayi mu baiwa Mood duk kannin kulawar daya dace a yanzu, nasanka nasan halinka fiye da yanda kai kasan kanka Jay, a yanzu na tabbatar zuciyarka tana raya maka kayi wani abu mara kyau, please let it be,just let the situation be for now kaji" Sauke nannauyan ajiyan zuciya yayi sannan cikin rauni yace

"He's my only son Barra, how can this happened? duk iyakar k'ok'arina seda yarinyar nan ta tayar masa da ciwon nan, idan ya mutu yazanyi?" D'agoshi tayi tamkar wani k'aramin yaro suka fuskanci juna

"Bana so ka d'auki alhakin abinda ya faru ka d'aura akan yarinyar nan, har yau nidakai ba wanda yasan ainahin menene gaskiyar abin nan so dole semunyi taka tsantsan da shiga hurumin Allah dakuma hakk'in wani" Shiru sukayi dukkansu, likitan ya k'ara kwantar masa da hankalin sa akan komai ze daidaita sannan suka juya zuwa wurin likitan dake duba Yar shara.

      "Bata samu wani injury a ko inaba se  wannan na kanta, wanda shima ba wani matsala bane dukda matsalar nekam, zata iya warkewa yanzu, gobe kokuma anjima, zata iya bazata warkewa ba har abada, abune dayake tafiya da lokaci shi d'inma ba komai bane, memory d'inta yana nan daram sedai matsalar dazata fuskanta shine wani lokacin kawai zata rik'a muku al'amari tamkar wata k'aramar yarinya, yanzu yanzu setana lafiya yanzu yanzu kuma seta soma muku da childish behaviour,anan abinda zan iya cewa biyu ne, da farko dai zamu tura asibitin dasuke kula da masu matsalar kai sabida su d'aurata akan magungunan daya dace, na biyu kuma sekunyi hak'uri, kunce shekarunta 17 to akwai haushi ace babba abun yara wannan shine hak'urin dazakuyi da ita for the time bn, dan azahirin gaskia bazamuce se yaushe zata warke ba, k'unan k'afarta kuma munada wani likita daya k'ware a wannan fannin ya duba k'afar kuma harya soma saka mata  wani cream yanzu haka wurin ya soma bushewa so within a week komai zai daidaita inshaa Allah" Tun sanda ya soma magana shi Uncle Jay yake kallo harya kai aya, abun akwai bam tsoro, dama akwai irin wannan ciwon ne shikuma? Nisawa yayi sannan yace

"Dama akwai irin wannan cutar kanne likita? Gyaran zaman file dake kusa dashi yayi sannan yace

"Sosai kuwa, amma gaskia da wahala kaga ansamu d'in, dan acikin shekaru biyar befi kaga irin case din so biyu ba koma k'asa ga hakan, ita kanta nayi mamakin abubuwan nata yanda suka juye akan k'aramar buguwa irin wannan, ina tsammanin dama akwai irin ciwon ajikinta batun yauba, samuwar sanadi se abun yayi k'amari" Jinjina kai yayi cikeda gamsuwa da bayanin sa sannan ya masa godiya sosai kafin suka juya b'angaren Mood. Basu samu daman shiga ba sabida ba'a shiga wurin sa, anan suka masa addu'a suka juya gida.

********************

    Yanayin zaman da tayi awurin kad'ai zaka kalla ka tabbatar cewar tacika kamilalliya, dukda yake shiga ce ajikinta irinta wayewa sosai amma hakan be isa ya hanaka fahimtar zallar kamilancin taba, handout ne da biro a hannun ta tana karatun handout d'in yayinda take k'ananun rubutu a wani small jotter haka, gabaki d'ayan hankalinta yana kan karatun datake, zuwa yayi ya zauna kusa da ita,lokaci d'aya dadd'an k'amshin turaren sa ya daki hancin ta, d'agowa tayi a hankali ta k'are masa kallo cikin d'ak'ik'a k'asa da talatin, dukda bataga fuskarsa gaba d'aya ba sabida ba gefen datake yake kallo ba amma kallon farko ta ayyana aranta wannan kyakyawa ne, bayan saurin kawar da kan datayi daga dubansa hadda yakice tunanin daya ziyarceta mara tushe akansa. Yafi mintuna talatin agun yana wayarsa batare daya nuna yakosan da wanzuwarta agunba, hakan ne ya masifar k'ularda ita, bayan kammala wayarsa ta farko sekuma ya gincira sannan ya kuma dialing wata number, ana d'agawa kuwa ya soma magana cikin d'aga murya yana fara'a, wannan abun ba k'aramin k'ular da Khairiyya  yayi ba, cikin zafi tace

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora