SHAFI NA ASHIRIN DA HUD'U

792 111 10
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA HUD'U*
24.
Lokacin da Hammood ya fita gaba d'aya se hankalin Hafsat yak'i kwanciya, wanda suka mata abinda suka mata bazasu tab'a barin taba, wama ya sani ko dama dakun jiran suke ya tashi a wurin su far mata, da sauri ta nemi abayar ta ta zura ta d'auki jakar ta, k'arewa d'akin kallo tayi kawai taje ta murza key ta rufeshi ata ciki sannan seta fita ta window lokacin banda tari da attishawa babu abinda take, ta jima sosai a wani wuri cikin asibitin seda haske asuba ya soma washewa sannan ta fito titi, batasha wahalar samun abun hawa ba kai tsaye gidan momy ta wuce, Baba me gadi jin kmocking ba k'aramin mamaki ya bashi ba, amma a haka ya taso yazo ya bud'e mata  ya kafeta da ido duk ta fita a hayyacin ta

"Hafsou kece da asubar fari, lafiya kuwa? Kafin ta bashi amsa ata bayanta kawai aka rotsa mata wani abu akai dayasa kai tsaye ta fad'o ajikin baba me gadi a sume, da sauri ya ajiyeta a k'asa yabi bayan wanda sukazo, sandar da dama da ita yazo bud'e gate d'in ya saita ya wurgawa wanda ya daketa, sannan cikin azama ya zaro wuk'a saga kunkurunsa ya kuma saitawa ya wurgawa d'ayan a kafad'a segasu zube gaba d'aya a kwance da gudunsa ya k'arasa yaje ya janyosu yazo ya d'auresu acikin gidan sannan ya kira momy

"Baba lafiya dai? Kallon ta yayi

"Wasune suka biyo bayan Hafsou bansan daga ina suke ba da wannan sanyin asubar ba, nayi nasarar saita d'aya da wuk'ar lak'ani, na kuma jefe d'aya da sandar lak'ani" cikin tashin hankalintace

"Inji ita Hafsat ba abinda ya same ta" Da hannu ya nunata a kwance

"Gatacen ya mata sanda akai, amma kizo ki kamata sena mata turare tas zata mik'e" Jiki na rawa momy ta fito tazo ita da masu aikin ta suka kama Hafsat sannan sukayi ciki da ita Baba yazo da garwasu a tray ya bad'ad'e kanta da hayaki take ta soma shak'uwa segashi ta dawo a mutum sak, dukda kanta yana mata ciwo, momy har kuwa seda tayi, idan masifar dake wannan masarautar takai haka akan Hafsat yaya khairiyya take? Inama zata saurareta? Inama zata tarbi uzurinta su tallafi maraicin juna, Bilal ya sakko tun zuwansa Nigeria amma ita sam se k'ara d'aukar zafi take da ita, Hafsat se zazzare ido take tace

"Momy bazan zauna a gidan nan ba, dole zan koma masarauta idan bacen ba babu inda nakeda tsaro, ta raina ake momy kar masifar dana janyowa kaina ta shafeki" Baba me gadi ne yace

"Anan gidan dai, banda k'arfin ikon Allah babu wanda ya isa yazo yace xe tab'aki, wancen yaron ma na zare wuk'ar jikinsa na shafa masa maganin tsayar da jini, seyayi bayani tiryan tiryan waye ya aikoshi dan bazan masa lamuni ba" Jinjina kai momy tayi, dukda haka zanwa Daddyn muhseen magana ya turo mana motar mopol biyu wannan shine kad'ai ze taimakeka Baba, idan kanada maganin k'arfe dana Bindiga Baba mifa? Gwanda dai a samu tsaron semu k'ara da naka, muyita addu'a kuma" Rik'e hannun momy Hafsat tayi

"Momy ki sanya mopol d'in su kaini masarauta, inason sanin halin da hammood yake ciki gaskia"

"Bara in kirawo khairiyya muji kenan" Tana janyo wayarta ta kira khairiya sega kiran Bilal (Yaron momy dakeson Hafsa dasuka had'u a US nake magana,yayan Khairiyya)

"Bilal ya akayi? Gyaran muryarshi yayi sannan yace

"Khairiyya ta kira waya tana kuka yanzu, wai mijinta da abokinsa da me martaba duk an harbesu" kallon Hafsat tayi kafin tace

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, harbi kuma a ina?

"Sun dawo masallaci ne kaman tace da asuba, ya kamata ki shirya zanzo muje yanzu" Da sauri tace

"Mu had'u agidan Bilal ba lokaci" Ajiye wayoyin sukayi sannan momy tana kallim Hafsat tace

"Ku tashi yazama dole muje masarautar ku yanzu" Batace komai ba sebin bayan momy datayi duk suka fita suka bar Baba me gadi da wannan mutanen tare da 'yan aikin gidan.

TSINTAR AYATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon