SHAFI NA HUD'U

1K 107 6
                                    

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

   *BILLY GALADANCHI*

       *SHAFI NA HUD'U*

kai tsaye d'akin da aka tanada dominta ya shiga yana me banke k'ofar da iyakacin k'arfin sa, idanuwansu suka tsark'e dana juna atake jikinta ya soma b'ari tana zaune asaman gado ta takure wuri d'aya se rarraba ido takeyi! Yafi mintuna goma a tsaye yana kallonta bece komai ba, seda dan kanshi ya gama tunanin dayake sannan ya juya da zummar barin d'akin abinda yajiyo je daga waje ya dakatar dashi ad'an lobin dake tsakanin waje dacikin d'akin

"Bari bari bari prince mood anji haushi, ai yanzu ance ko sarki yaji komai, jakadiya ta tabbatar wa sarki wannan yarinyar 'yar hannu ce cikine sukaje su zubar yazo da gaddama, ance tutsiye yarinyar akayi ta fad'i gaskia akan dama saurayintane dasukaje azubar da cikin daya mata shine fa aka samu matsala seya d'akkota ya kawo ta nan besan asirinsa ze tonu ba" Dariya d'ayar tayi

"Daba sunce aure zasu masa da itaba? to yanzu naji ance sarki yace a koreta tunda abun hakane, yazata hakk'inta yaci daze d'aura aurensu yanzu kuwa korace"  Tafawa sukayi

"Bakiji yanda na tsani yarinyar ba wlh, da akace ze aureta nace su kurma an iya zab'e wannan yarinyar kyau kamar aljana shegiya se gashi,yanzu danaji labarin za'a koreta se wani sanyi ya mamayeni, dankuwa ni wlh inasan sa haka" Duka d'ayar ta d'aka mata a cinya

"Banza yafi k'arfin ma'aikata da bayi ki kama kanki" Be jira sun k'ara wata maganar ba ya fito daga d'akin,yauma kamar kullum beko kallesu ba ya shiga d'akinsa jikinsa a matuk'ar mace wai meke faruwa ne? menene gaskiyar maganar mutanen nan su kuma manyan munafukai ba? yaya yakejin maganar tana juyawa up side down?..... Mik'ewa yayi yanzun ma da sassarfa ya sakko k'asa ya nufi motar sa, beko nemi Muhseen ba dankuwa yaga motarsa a sukwane ya nufi gidan *UNCLE JAY*.......

    Tunda Anty Barra taji tsayuwar motar da gudun tasan D'an kurma ne agidan yau kamar yanda take kiranshi, dan hakanda azama ta juya daga parlor zuwa ciki

"Uncle Jay bazan iya da rigimar Kurma ba, naji tsayuwar motarsa nakumaji gudunsa dan Allah ka tashi kaje" D'ago kai yayi ya kalleta yana murmushi

"Dama nasan zezo ban tsammanin zezo yanzu bane ba" Murmushin ta mayar masa "amma lafiya dai?"

"Ba lau ba dai, Mood ne bashida wayau ko kad'an, duk abinda zeyi seya saka rashin wayau se uban zurfin ciki da miskilancin tsiya" Tana kallon sa harya kai aya, nisawa tayi tace

"Ka saurareshi yanzu, tunda yazo mayi maganar daga baya" Mik'ewa yayi

"Noo wife agabanki zamuyi maganar muje kawai, its good kina wurin with those ur boosting idea's i belive abubuwan zasuje mana da sauk'i" Ba musu suka fita atare hannayensu sak'ale ana juna, a parlor suka sameshi harya shigo yana zaune akan sopa ya sunkuyar da kanshi hannayensa duka cure acikin sumar kansa. Gaisawa sukayi dashi da yarensa sannan  ya mik'awa Uncle Jay duk abubuwan da suka faru a rubuce a takarda har gulman dayaji ma'aikatan dayace a kora sunayi, ga alama be isa yace ayi ba ayi a yanzu! Tare da Barra Jay ya zauna suka karance takardar tatas kallon sa yayi sannan yace

"Naje gidan da safe gun Maminka tamun bayanin farko akan yanda ka shigo da ita, dakuma ya da maganar ta k'ara juyewa akan na ciki, sedai sarki be yarda da maganar jakadiya ba akamar yanda kaji ana tsegumi, hasalima ya kashe wannan maganar, abu d'ayane ya dai ya kafe akan seka auri yarinyar ranar juma'a" Da sauri ya d'ago ya kallesa,cikin yare irin nasu kurame da tsananin b'acin rai ya soma magana da hannayensa wannan karon har kansa da wuya mosti yake yana yi tamkar ze tashi sama. Seda ya lafa sannan Uncle Jay ya kalli Barra

"Barra me kike hasashe, da gaske kema abinda muke zargi akan had'in bakine da yarinyar haka kema kike zargi" D'an shiru tayi na wani lokaci kafin ta nisa tace

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora