SHAFI NA GOMA

1.1K 97 7
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

*BILLY GALADANCHI*

~NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GAREKI MEENAT A 'YANDOMA, ALLAH BAYAR KAUNA YA SAKA DA ALKHAIRI~

   "SHAFI NA GOMA"

Mik'ewa tayi tabi bayanshi da kallo, bazata koma gidan Momy ba sabida Bilal baze tab'a barinta ba kuma sannan momy batada halaye na garin daya dace a zauna da ita, bakuma zata tab'a komawa wancen garin wanda yake tushe kuma mafarinta, idan har wanda ya kawo ubanka duniya ze cutar dakai a rayuwa waye baze cutar dakai ba? Wannan mutumin kuma gashi nan kansa a murd'e yak'i ya saurare ta, shikenan bazata matsa masa ba amma wlh zezo lokacin dayakeso yaji labarin wani abu daga bakin ta bazata furta koda kalmar ci kanka bane. Kannata yanaci gaba sara mata, tasoma fahimtar irin ciwon dake damun ta, yanzu yanzu zata suma kokuma tama rasa metayi sedai ta farka ta ganta a kwance kaman tayi bacci ta tashi, zuwa tayi ta kwanta akan doguwar kujerar dake parlor d'in amon sautin muryar D'an galadima yana ratsa dodon kunnenta

"Na fahimci matsalarki danginki basa sanki, na fahimci cikin shege akayi aka haifeki, nagama fahimtar bakida gata, to bari kini wannan masarautar dakike gani ta kowa ce, muna baiwa marayu irinki masauki, idan kinyi abinda nakeso in baki matsayin ko baiwa , idan kika kuskura kika bud'e bakinki kika baiwa wani labarin ainahin gaskiyar meya faru kokuma ke wacece tabbas sena azabtar dake, wlh maza hamsin zasu miki fyad'e kuma in wurgaki a teku ba abinda za'ayi mukeda mulkin, karnaji kin bud'i baki kinyi maganar asalinki ko danginki, yanda zakiji likita ya fad'a bakya iya tuna komai lallai komai nisan zaman dazakiyi agidan nan ki tabbata a haka, ranar daduk kika tonamun asiri wlh sena tona miki asiri kema" Lumshe idanta tae, after  all she decided to talk and this man is feeling himself, like seriously what is he feeling like? sarki kokuma d'an sarki, ita Allah yayi acikin bayinsa talakawa, amma ya d'aga darajarta tayi primary dukda a primary 4 tayi common entrance tashiga j.s.s. 1 kuma bayan tazo nan garin ta baro garinsu mamanta tana 'yar JSS 3 kuma data koma garinsu Babanta suka turota aikatau momy ta sakata school kuma tana shirin zana wa'ec ma wannan abun ya sameta, tanada ilimin addini daidai gwargwado tome yayi zafi shiba wutaba da har ze soma tunanin yafita ilimi kome? duk tayi irin nasa kuma ita sam ba jahila bace ba, bahar ta sanar da ita an karb'eta agidan a matsayin 'Ya awurin bahar hakan ya bata daman zama 'k'anwar sarki wanda a musulunce tasan an halasta adoption, mesa zatayiwa Allah addu'an neman d'auki ya kawo mata agaji kuma ta watsar, bazata yiwa Allah butulciba zataje wurin da aka shirya don gabatar da ita matsayin 'yar gida, zata karb'i sabuwar rayuwar datazo mata, shi kuwa Mood su zuba shida ita, bata masa komai bazata d'auki dizgi da wulak'anci ba, after all abinda yakeji dadi jinin sane kawai babu ajikin ta amma itama tanaji da irinsa yanzu!!

****************
     A lokacin da akaje bikin k'addamar da Hafsat matsayin adopted child agidan, se  kawai waziri ya zuga sarki akan shiya d'auki yarinyar mana matsayin 'yarda ya haifa kadafa ya manta banda Hammood bashida d'a bashida jika, bayaga haka 'ya mace ma rahama ce, yace daga baya seya nunawa bahar hikimar yin hakan gwanda ta zama kaka tunda koba komai aita tsufa..... Dukda Bahar tayi mamakin jin sauyawar maganar amma se hakan yayi mata dad'i koba komai ya nuna mata yafita son abinda take so, kowa se gulma yake tun a wurin, yarinyar da Mood yayiwa fyad'e tazama 'yar sarki, wasu suce ai ciki ne ya bayyana ajikinta ake b'oyewa, wasu suce ai an zubar da cikin kowa dai da abinda yake fad'a.... Mood sanda me martaba ya had'asu yana zancen sun zama d'aya banda gajerun tsaki mara sauti ba abinda yake zubawa, samun wuri da rainin hankali, wannan yarinyar tabbas yanzu ya k'ara yadda turota akayi, kuma dasanya hannun su galadima a faruwar komai, baya rab'a d'ayan biyu tabbas da sihiri suke aiki sun sihirce kakarsa da Mahaifinsa harma da mahaifiyarsa, kai kafatanin mutanen masarautar ma, banda haka bakusan asalin yarinyar ba sekuce kun mayar da ita 'ya 'yarma ta sarki wai taku, haba haba wannan maganar wlh da sake wai an baiwa me kaza k'afa.

TSINTAR AYAWhere stories live. Discover now