SHAFI NA GOMA SHA BIYAR

942 106 7
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

*NA:BILLY GALADANCHI*

-Babu wata k'awa datake tona miki asiri face kin tonawa kanki asiri, ku dena ganin laifin k'awaye dan abu ya had'aku dasu kuma sun muku tonon silili, kece kika gaya musu kikace kuje ku fad'a.Ba zancen dena yin k'awa kuyi k'awayen ku na alkhairi amma ku adanawa cikinku abinda be shafeku dasuba, koyin tsegumin wani, idan kika sirrinta sirrinki babu wata wacce ta isa ta yayata sirrinki.-

*SHAFI NA GOMA SHA BIYAR*

     Cikin wazgewa ya sauke hannun sa, jotter sa ya zaro a hanzarce ya rubuta

"Your wasting my time" Haska mata jotter yayi amma be kalleta ba, waige ta shiga amma tana mamakin mesashi gwale ido hadda rufe baki, babu kowa awurin se ita dashi kawai se kuwa mutumin dake gaban table nashi yana displying mata phones dasuke dasu, kallon rubutun tayi sannan setayi wata siririyar dariya tace a sarari

"Zargina ya tabbata kenan" Amma bashi take kallo ba koda tayi maganar, d'auke kai tayi ta ksrb'i farin wayar kawai suka bar shop d'in bayan ya biya kud'in, seda ya saya mata sim cards har biyu da layinsa akayi gwaji sannan suka d'auki hanyar gida, lokaci zuwa lokaci a mota suna satar kallon juna wanda khairiyya ma ta kula dukkansu basa cikin nutsuwar zuciya kaman yanda suka fito agida, amon sautin muryar Mood yana ratsa dodon kunnen Hafsat, tabbas magana yayi wannan shine karo na biyu dataji maganar sa sedai kuma wancen karon waya kawai ta hango yanayi amma ta tabbatar magana yake, yanzu kuma murya rad'am lafiya lau mezaisa yayi hakan to? akan wane dalili ze takure rayuwar sa alhali yana magana? to kuma ance mahaifiyar sama kurma ce kodai ita d'inma tana magana akwai abinda yasa sukewa mutane kwantan b'auna? zuciyarta tana azalzalarta akan sanin waye Hammood menene ainahin gaskiyar labarin sa shida mahaifiyar sa, daga wacce masarautar suka fito ance kakansa ma na wurin uwa sarkin wata masarautar ne shin menene dalilin dayasa Uncle Jay yana k'anin Ummin hammood amma yake zama a masarautar da yayarsa ke aure a maimakon tasa masarautar, batada wata alak'a da kowacce masarauta seta k'auye, a k'auyensu mahaifinta mahaifinsa shine me garin k'auyen nasu amma banda hakan batasan komai akan sarauta ba, abu d'aya ta sani akwai mak'iyan Hammood a masarautar daga lokacin da akace ze aureta mutane sama da goma sunce ta kashe sa zasu bata dukiya, kodai itama kurmar zata zama ne sabida ta samu amsar tambayoyinta? Har suka isa gidan batasan sun k'arasa ba, seda Driver ya mata magana so kusan uku sannan tafita tabi bayansu tana godiya wa Hammood.

     Kai tsaye Toilet ya fad'a ya sakarwa kansa shaya, ya akayi yayi sub'utar baki haka? ze iya cewa a shekaru biyun dayayi a Nigeria koda kuskure be tab'a yiwa wani magana ba seso d'aya shi d'inma a wayane, wayar kuma ta zama dole ne sabida daga U.S d'in aka kirasa, lumshe idansa yayi ruwan me zafi yana sauka ajikinsa, dukda dad'in ruwan dayakeji hakan be hanawa xuciyar sa cunkushewa ba, idan har zargin sa akan Hafsat hakane na turota akayi ta dagula lissafin sa tabbas yau ta samu makamin dashi kad'ai ya ishi mak'iyansa kawar dashi dan kuwa sun saki jikine akan bazasu tab'a bari kurma ya mulke suba, daga lokacin dako yau akace sunsan yanxu ya samu lafiya yana ji yana kuma magana tokuwa sesun yi duk yanda zansuyi sun kashe ruwan daya cika masa baki ya furzar sannan ya fito yabzura bathrobe d'insa ya zauna a bakin gado, wayarsa ya janyo ya k'urawa number ta daya gwada kira d'azu, shin magana ze mata ko me, kokuma ya bata kwana biyu ya gani koda zatayi wata alamar dake nuni da cewar taji kai tamaji, reaction d'inta kawai ya isa ya nunar masa cewar tabbas taji yayi magana, ajiye wayar yayi agefe ya shafi sunar kansa datasha gyara tamkar ta larabawa anyi style da sumar ata gaban kansa, Khairii ce ta shigo ta zauna a kusa dashi

"Menene yake damunka you look really tensed, tunda kuka fito shagon wayar nan naga mood naka ya sauya, kaddai wani izgilin waccen wawiyar tayi maka" Murmushi yayi ya janyita gaba d'aya ya ringum'e a k'irjin sa, sumba ya manna mata a goshi yanajin sonta yana ratsa shi, be tab'a zata qrayuwa zeso wata mace kamar yanda yakeson khairiyya ba amma me wannan yarinyar ta gama da ilahirin gabb'an jikin sa da zuciyar sa, bece komai ba a haka suka fad'a sabuwar duniya, ga alama khairiyya tanada yawan sha'awa sedai kuma tabbas  raguwa ce, batason sakin jikinta ayi sha'ani daga zaran tabiya buk'atarta a wurin wasanni seta soma yangace masa ala dole ita ta gaji.

TSINTAR AYAOnde histórias criam vida. Descubra agora