SHAFI NA ASHIRIN DA D'AYA

1.2K 130 22
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*ASSLAMU ALAIKUM,KAMAR YANDA NA FAD'A DAGA FARKO DAI HAKANE, BA KULLUM ZANKEYIN POSTING BA, IDAN NAYI YAU BAXANYI GOBE BA, DUK RANAR DAKUKAGA NAYI YAU NAYI GOBE TO NASAMU CHANCE KENAN INA FATAN ZAKUMUN UZURI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA D'AYA*

21.

Wata hanya ya d'auke tare da d'auke hankalin masubin bayansu, hannu ya sanya ya rufe mata baki bayan sun shiga lungun ga duhun dare bazata iya gane waye ba suka k'urawa juna ido acikin duhun dukkaninsu suna iya jiyo yanda sautin bugawar zuciyoyin junansu ke bugawa da k'arfi, zuwa wani lokaci dabaze wuce minti uku ba ya sake ta sannan ya fita daga lungun yana fitar da sautin hakin k'arya daga huhunsa yana tambayar wasu

"Kunyi nasarar ganinsu kuwa? Ni ban same suba" D'ayan yana kallon sa yace

"Bibiyar su a yanzu baze amfanemu da komai ba, shugaba ya suma dan haka mu koma kawai kafin k'ubgiyar kwantacciyar maciji ta ganmu ta gane sirrinmu" Haka suka juya zuwa d'akin taron na sirri zuciyoyin su babu dad'i suna mejin rad'ad'in abinda suka fad'a agaban wad'an nan. Dafe zuciyarta tayi dake k'ok'arin faso k'irjinta ta fito ta soma sauke numfarfashi sama sama tsananin tsoron data shiga, jikinta ba k'aramin rawa ya hauyi ba seda ta denajin takun sawun tafiyarsu da mintuna biyu zuwa biyar sannan ta zare mask ta cire bak'ar rigar dake jikinta, ta zubesu anan sannan ta fito daga cikin wurin tana waiwaye...... gab dazata shiga part d'in Bahar aka rik'o hannunta a zabure ta k'walla k'ara da sauri ya rufe mata baki da hannun sa cikin  rad'a a kunnenta yace

"Daga ina kike cikin wannan daren" gano cewar Hammood ne ba k'aramin kwantar mata da hankali yayi ba, tace cikin sauke numfashi

"Alhamdulillah" sannan tayi lamo ta lafe ajikin sa, shikuwa hakan datayi ba k'aramin tasiri yayi ajikin saba, sungumarta gaba d'aya yayi nan d'inma lafewa tayi a k'irjin sa tana sauke gajerun numfashi a wahale, ji takeyi tamkar wani macecin rayuwarta yazo, kai tsaye cikin gidan yashiga dogarawa masu tsaron k'ofar basuce dasu komai ba, har d'akin dayake mallakin ta ya shigar da itabya ajiye ta akan gado, hannu yakai ya janyo mata hular dake kanta ta rufe sumar data lek'o ata gaban kanta, yana nazarin yanayin ta yace

"Daga ina kike yanzu? Kawar da kanta tayi daga dubansa sannan tace

"Kai daga ina kake yanzu? Murmushi yayi kafin yace

"Kinada ban mamaki Hafsat, kina ganin kamar ke kinfi kowa wayau ne kome? Tsammani kike kamar kin samu power dazaki iya kayar dani, ki sani nan masarauta tace kuma  duk wani wanda yake k'ulla sharri ko alkhairi akaina inada masaniya akansa, lokaci kawai na baiwa kowa daze yabawa aya zak'inta a hannuna, wlh bakina dana rufe na tsawon shekaru sena fansheshi akan mak'iyna cikin k'asa ga wata watanni shida, idan kikaje ki gayawa manyan ki su shirya, kuma sunyi sake d'an zaki ya girma, a shirye nazo kuma tabbas sena kayar dasu nine da nasara, suna tak'amar suna iya wargazani, nikuma ina tak'amar zan iya wargaza dukkan shirin su, sena zame musu k'arfen k'afa fiye da yanda Takawa me martaba sarkin masarautar hankaka ya wargaza azzaluman masarautar sa. Duba littafin TAFARU TA KARE dan samun yanda ta kaya a wannan masarautar. Sena tabbatar na rugurguza anniyarsu kuma wallahi, summa tallahi billahi ni Hammood nayi alk'awarin koda raina ze zama fansa sena wargaza sirrin mak'iyana sannu a hankali" Mik'ewa tayi zaune sannan tace tana kallonsa ido cikin ido

"Na tab'a gaya maka cewar ur a coward ko? To yauma zan kuma nanata maka ur nothing but a cowar and just that, ni kake zuwa kana yiwa barazana nida banda k'addara bankosan da wanzuwar kaba, kazo kana fad'a da mace macen ma 'yar shekaru sha bakwai kai kuwa ka takewa talatin baya, kaje kayi fad'a da maza mana bani ba, yes am an informer yanda kake tunani haka ne, ina bibiyar rayuwar kane kuma sakani akayi bazan sauraraba kuma senaga bayan wannan coward life da kake living, do your worst and lastly ni kadena yimun barazana dan duk abinda nake ba fasawa zanyi ba, i promised wanda suka sakani sena tabbatar naga k'arshen wannan rayuwar da kake, So idan barazana zakayi kaje ka nemi magautanka maza bani ba" Bakinta ya matse seda idanta yayi ja amma batako yi k'ok'arin k'watar kanta ba, shi kanshi idanshi yayi ja jajir jijiyoyin gefen kansa duk sun fito rad'o rad'o fatar fuskarsa tayi jajir sabida tsananin fusata yace

TSINTAR AYAOnde histórias criam vida. Descubra agora