SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

1K 119 10
                                    

    *TSINTAR AYA*  FREE BOOK

         *BILLY GALADANCHI*

     *SHAFI NA ASHIRIN DA UKU*

23.
Tunda wad'annan mutanen suka fara shigowa se gaba d'aya hammood yabar reception sabida shima bawai ya fito haka kawai bane, tsaf acikin motar sa seda ya sauya kaya zuwa wata matacciyar yadi da hula kayan daud'ar jikinsu kad'ai ta ishe su, gaba d'aya yayi dressing irin na me garin k'auye da wani karkataccen madubi bayau ya saba basaja irin haka ba, dan kuwa gaba d'aya motar dayake kanta ba wacce aka sanshi da ita bace, wata iriyar starlet ce me sanya ciwon jiki, gaba d'aya rawanin dake kansa ya wani cukurkud'e wuri d'aya gashi a karkace, wannan shirin ba k'aramin b'atar da kamanin sa yayi ba fiyeda yanda ya kawar da kamanin Hafsat, shi kanshi shirin barin wurin yake dan haka kusan atare suka shiga abun hawa, ita tahau napep shikuwa ya shiga wannan kwarab'abbiyar starlet danake da tak'inin ta girmewa shekarun haihuwar sa, kallon matar yake data shiga keke napep d'in, tun d'azu me napep d'in yake wurin bayan ammasa bayanin wani abu an nuna masa waya, kuma wanda yabi bayan matar yashiga napep d'in bawai tare suke da matar ba, sannan kuma yaga yana wata magana dame napep d'in kafin fitowar ta, kenan parking d'in natane dama ita ake jira? Dama motarsa a kunne take hakan yasa yayi azamar zuwa domin yayi overtaking nasu amma me seyaga matar ciki wuyanta  ya tafi baya tamkar matacciya har mayafinta ya zame baya, seda wata mota ta tashi bugun nashi sannan ya saisaita kansa, me napep kuwa zuwa yayi da azama ya wuceshi sunata sauri tamkar zasu tashi sama wannan ne ya k'arawa abun k'aimi a zuciyar sa yace lallai seyaga inda suka dosa!

      Sanda yabi ta d'ayan layin daya ajiye motarsa yayi parking wannan motar sannan yashiga tsakanin gutter's ya tsallaka ya b'ulla ta wannan layin dayayi parking acikin motarsa ta alfarma ya sauya kayan jikin sa nanma, seda yayi branching guest house nashi yashiga ya ajiye wannan motar sannan yafita da wata motar ta k'ofar baya ya nufi masarautar sa a sukwane tamkar zakin daya shekara beci namaba! Kai tsaye part d'in khairiyya ya nufa acen ya tarar ta dawo, kallon ta yayi sosai sannan ya haska mata wayar sa, sesa ta karanta abinda yake nuna mata sannan ta kawar dakai tare da cewa

"Anguwa naje" Cikin fusata ya kuma rubuta

"Yaushe kika isa kije unguwa batare da izinina ba? Kuma unguwar wurin wa? Wa kika sani a garin? Tana gama karantawa ta kallesa

"Ajiyeni kayi ne? Kokuma kaine raina yake hannunka kaga Hammood dan Allah ka shafawa lafiya ta lafiya, abinda ya isheni ya isheni" Fusata yanzu kam yayi ya matso kusa da ita a harzuk'e ita kanta tayi mamakin yanayin sa, tunda suke yaune rana ta farko data hango masifa haka a idansa, matseta yayi har jikin bango amma bece mata ci kanki ba kawai ya tsatsareta da manya manyan idanuwan sane dasuka sauya launi, runtse idanta tayi cike da tsoro, she really need a shoulder to cry on, mesa yake mata fad'a, gaba d'aya mahaifiyarta ta janyo mata mummunan tabon daze illata rayuwarta, menene amfanin wannan mugun aikin data aikata, akan me Bilal zeje wannan matakin a tonawa mahaifiyarta a siri, zuwa wannan lokacin gaba d'aya kukan datakeso tayi tun d'azu bezoba se yanzu ya wanke fuskarta dukda idanta a rufe yake, duk yanda taso ta had'iye kukan nata seda yazo da iyakacin k'arfin sa, kukan ta saka sosai wanda ya sanya yayi kasake kawai yana kallon ta cikin mamaki, maganar sace ta b'ata mata rai kome? Metakeyi tare dasu Baba Usman?  Me suka ce mata? Is she alright? Janyota yayi zuwa jikinsa ya soma patting bayanta a hankali ziciyar sa tana harbawa ya tabbatar akwai wani abun dasuke shiryawa tare da khairiyya kuma yanzu ne suke so suyi trapping nata tun ita batasan asalin halayyar suba, meke shirin tasowa kuma, be hanata kukanba seda tayi me isarta sannan ya kwantar da ita kawa yabar d'akin dan kuwa hankalin sa yanakan waccen yarinyar dayabi bayan 'yan keke napep yaga sun kaita unguwar Shiyar fada cikin tsohon guest house d'in me martaba dayake k'ark'ashin kulawar  Baba Usman a yanxu, mecece alak'ar dake tsakanin Baba Usman da khairiyya, mesa kuma ya sanya aka d'auke matar mutane zuwa shiyar fada danya tabbatar cewar shine ya sanya aka d'auketa, to Amma ina hafsa taje? Metajeyi a wannan gidan? Kai tsaye part d'in Bahar ya nufa dan yasan a k'a'ida yau akace zata tare agidan ta, koda yaje ya binciki bahar batanan, driver dasuka fita atare ya tambaya ita inda ya tabbatar masa da cewar ga unguwan daya kaita kuma tace k'arfe shida ya koma ya d'auketa, yaje ance tafita tin yamma bata dawo ba, yajira har bayan magrib bata dawo ba wannan ya sanya ya taho a tunanin sa ta koma gida!  Kai tsaye gidan Hammood ya nufa inda yaje ya tarar da Baba me gadi dan tuni ya dawowa aikin sa agidan, seda ya waiga baya yaga ba kowa sannan yace

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora