SHAFI NA GOMA SHA HUD'U

1.2K 117 9
                                    

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

*NA:BILLY GALADANCHI*

*Hajiya Maryam (Sakatariya) Nagode da irin k'ok'arin dakike mun, Allah ya k'ara d'aukaka da laifin basira, littafin Ido da tsakuwa yana tafiya yanda ya kamata, masoya Billy Galadanchi ku bibiyi litattafan Haj maryam akwai tarin fad'akarwa acikin su.*

*SHAFI NA GOMA SHA HUD'U.

      Tana shirin shiga parlor ya rik'o ta, da sauri ya ajiyeta agabansa, tsatsareta da idansa yayi ita d'inma shi take kallo lokaci d'aya idanta ya kawo ruwan sanin cewar Bahar bata nan,muryan ta yana rawa tace

"Allah Yaa Mood sune suka tsokaneni, wannan yaran ne yake tab'ani, d'an iskane yanata rik'emun hannu na, nace ya dena ya kama ya rirrik'eni shine ni kuma sena.... sekuma ta k'asa k'arasa durta kalmar marin data masa, hannunta daya matse tak'e k'ok'arin ta wace cikin kuka tace "Yaa Mood please am sorry bazan k'araba daga yau kaji" Har lokacin hannun yake dad'a matsewa amma be sak'eta ba idanshi kuma yana kanta yama rasa mezeyi mata, wace irin mara kunyace yarin yar nan wai? yazata kalli babba girman Bilal ta antaya masa mari dan kawai ya rik'e hannun ta, she's so mean wlh, hannunta dake hannunsa yajata har gaban Bilar ya direta a durk'ushe yana had'e rai da hannu yayi mata alamar

"Apologize" D'auke kanta tayi dan bataji zata iya bada hak'urin, itafa dama hafsat she's very stubborn , ko a school zaka sameta ajerin masu zafin school abu kad'an ya k'ular da ita kuma acikin mutanen datake hurd'a dasu zakaga ba k'auyawa tanason waye wa, wasu sabida yawan rashin shiga harkar mutane datake suke cewa da ita she's very arrogant, juyo da fuskarta tayi suka kalli juna ya nuna mata Bilal ya kuma mata alamar

"Appologize" Nan ma bata dena kallon sa ba kuma batayi abinda yace d'in ba, zuciyar sa gaya masa take ya wanke ta da mari amma bayaso yake dukan mace ba halin sa bane ba, amma me yarinyar nan take nufi dashine haka wai? cikin fad'a sosai yanzu kam ya kuma mata alamar ta bada hak'uri amma bud'ar bakin ta se cewa tayi

"Shine ya dace ya bani hak'uri and thats what am waiting for, i did nothing wrong then why should i be the one to appogize, how can he just grab my hand d'an iskan inane shi daze kaman hannu na" Mamaki sosai ya k'aru a fuskar Mood what is this girl wai? ya tambayi kansa a sarari kuma masifa yaso ya fara da hannayensa Bilal yayi saurin cewa

"K'anwata am sorry, i really am, kinsan na rayu anan shenaru sunkai goma sha biyar, am used to, anan ba komai bane sam na manta da hakan shisa akeso kake zama tushiyar ka kodan gudun manta irin wannan abubuwan, amma God know's i mean nothing" Murmushi ta masa

"What ever" Tana shirin mik'ewa Mood ya saka k'afarsa ta durk'ushe awurin da hannu ya kuma mata alamar "Apologize now" Tab'e baki tayi

"Wainikam baka ganewa ne? shi yama fika hankali ya gane me nake nufi dan kaga ya bada hak'uri" Damk'o kanta khairii tayi

"Me kike tunanin kice?  cewar Prince dak'ik'i ne kome? ke kanki d'aya kuwa? Yauma kamar ranar haka ta durk'ushe tajuya fskantar khairi hannun ta ya langwashe ta k'walla k'ara kuma dole ta sake mata sumar da har hular kanta ya fita ta barbaje, hannu bibbiyu ta saka ta tureta taje cen Hammood ya rik'e ita kuwa ta kwasa a guje sumar kanta daya baje kamar wata haihuwar indiya tana gudu sumar kan nata tana shawagi sabida gyaran datasha an kashe kud'i wurin gyaran ta sosai, dan kuwa Bahar ba baya ba akwai tsafta, Hammod tsaye yayi ya rik'e k'ugu yana kallon ta shi kuwa Bilal yana dariya yana tafa hannu yace

"That funny thing, she's very honest inason mutum me irin halinta, so staright forward, gaskia tafimu gaskia" Kallon takaici Hammood ya masa yama rasa mezeyi, kawai barin wurin yayi. Kallon 'yar uwarsa yayi yace

"Khairii be very carefull with that girl, nasan ki da fad'a da tsanar me kyau, that poor thing u see there ko, zatayi wuyar sha'ani a murd'e take kaman namiji karki rik'a cewa zaki shiga sha'anin ta kinji ko? Murmushin yak'e tayi sannan tace

TSINTAR AYADove le storie prendono vita. Scoprilo ora