SHAFI NA TALATIN

806 115 22
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

      *BILLY GALADANCHI*

        *SHAFI NA TALATIN*

*HAFSATY AN RIGIMA GA SHAFIN DARE NAN NA SAUKAR MIKI DASHI,NADAI CIKI ALK'AWARI KO?😂

30.

Maganar data fad'a ne ya k'wank'wasa kansa akan labarin daya gabaci wannan, hannayenta ya rik'o ita kanta seda ya bata tausayi jikinsa yana b'ari kansa yana sara masa yace.

"Hafsa please tell me more, banaso ya kasance tunanina ya tabbata gaskia ne, its being long danaga Baba Surbajo, nakanje gaidata Bahar tana turani wurin ta sosai, apart from Uncle Jay Baba Surbajo kad'ai tasan ina magana, that woman suffered alot, tana fama da matsaloli lafiyar ta k'alau but she still have to act like she's mentally ill, when ever i visit her, tanamun nasiha wa'azi and tana yawan gayamun cewan she's doing everything for me, Hafsa kin tab'a ganinta, muna kama sosai ko? Sadda kai k'asa hafsa tayi hawaye yana zuba daga idanta sabida tsananin tausayin hammood dataji ya kama, muryanta yana rawa tace

"Nikanje gayar da ita sosai Hammood she help me with alot of information, she's ur mother she loves u so much yaa Mood,  she endue everything alot of pain just so you live, am sorry to say amma gaskia Uncle Jay da Mami bazasuga annabi ba" Had'e jikinsa da nata yayi yana wani kuka me sauti tare murza bayanta da hannayensa da k'arfi, sosai ya matseta dankuwa taji zafin matsar gunjin kukansa ya sanya ta sake wani kuka meban tausayi ita kanta se yanzu abubuwa suke dawo mata sosai, lallai an cutar da Mood, acikin k'ank'anin lokaci Allah ya taimaketa tasan komai dole ta kwantar wa Mood da hankali, wannan shine time datake jira tayi calming nasa, cikin murya k'asa k'asa tace kusa da kunnenshi

"Ka saurareni , ka kwantar da hankalinka muyi mahana Yaa Mood, ka d'auka duk abinda zakaji jinsa shine mafi alkhairi agareka kaji" Data ne ya mik'e ya janyo hannun sa shima ya soma ban baki "kayi hak'uri Hammood, dama haka rayuwar nan take ups and down ne sukayi yawa acikinta, dik abubuwan dazakaji tamkar a film kawai akeyinsu wlh anan ma anayi a duniyar zahiri sukan faru, balantana rayuwar sarauta mutane da Mulki da kuma Kud'i suna iyayin komai a kansa, akwai labarin wani gidan sarautar dana sani d'a ya kashe mahaifin dayake gargarar mutuwa yana fama da ciwo shekaru kusan biyar be mutu ba kuma be bashi sarautar ba kawai yaran nan ya kashe uban yace ya gaji da jiran sa tunda shi mulki yake so, ashe naka bame sauk'i bane ba? Ehm Hammood" kwantar da kanshi yayi ajikin Data tamkar wani k'aramin yaro yashiga sauke gaurayen ajiyan zuciya, seda Hafsa ta hadiyi zuciya sannan taci gaba

"Lokacin dana ziyarci Baba Surbajo kallo d'aya na mata k'irjina ya doka sabida tsananin kamannin datake da Mood,lokaci d'aya na harbo bakin zaren, sabida ita kuyangar dataje da maganar awurin barra batada cikakken ililmi akan meya faru a wannan daren da lokacin haihuwar, bayan na zauna kusa da ita na gaisheta bata amsani ba haka kuma bata nunamun hankalin ta sosai yake ajikinta ba, seda nai gyaran zama nace ina kallon ta

"Baba ina wuni, ya lafiyar jikinki? Bata amsani ba har lokacin wannan ya sanya kawai na zauna na kama kanta nayi addu'a tare da mata fatan samun lafiya sannan a tak'aice nace da ita

"Baba nizan koma, sabuwar 'yarkice Bahar tace inzo in gaisheki, me martaba ne yake matsayi  uban rik'ona a yanzu ta sanarmun rashin lafiyar ki tace kema uwatace ina miki fatan alkhairi" Da wannan naga ta bini da ido, kallon datamun ya dasa wani abu a raina harnabar wurin bata dena kallo naba, a k'wayar idanta na hango tsantsar k'auna, tabbacin cewar tana tsananin jin duk abinda nake cewa, a hakan na kasa bacci a wannan daren ban yadda batada lafiya akai ba, inada yak'inin garas take,mesa take pretending? Kasawar hak'urina ya sanya najewa Bahar da maganar lallai Baba surbajo lafiyar ta k'alau kokuma dai ta warke, da farko bata yardaba akan cewar cutace datak'i samun waraka fin shekaru talatin aduniya amma dana k'ara komawa namata addu'a sanda zan tafi seta rik'e hannu ta k'ara mayarwa akanta alamun tana buk'atar addu'an fiye da yanda nake mata, dan haka sena k'ara k'aimi na d'auki tsawon sati d'aya ina zuwa ahaka harna soma samun damar tana mun magana, lokaci zuwa lokaci sedai na kula cewar a sirrance takemun magana dan haka wata rana senaja bahar mukaje wurinta acikin talatainin dare, wanda na jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya a wannan daren, na farko A ranar nafara yin arba da mutan k'ungiyar aci duhu, aranar kuma mukayi nasara Baba Surbajo ta bamu cikakken labari akan lokacin haihuwar ka, tace damu.....

"Bayan na samu ciki sena dinga b'oyon cikina, badan komai ba sedan dalilai guda biyu na farko dai sabida an tabbatar mun da cewar Maryama itace ta sanya aka kashemun yarana guda biyu, nayiwa Me martaba maganar a wancen lokacin amma se gaba d'aya ya nunamun be aminta ba gulmar gidan sarauta ne! Na biyu kuma an tabbatar mun dacewar tace bazata k'ara barin ciki yayi k'wari ajikina ba ga wannan cikin nima bansan dashiba har seda ya soma motsi, nayi mamaki sosai danko girma bayayi, haka nida kuyanga ta ta wancen lokacin muka rufe maganar, ga mamakina rana d'aya ina lissafin ciki wata bakwai sega nak'uda gadan gadan, kuyangata taso sosai ta karb'i haihuwata da kanta amma se haihuwar tazo da gaddama yasa dole ta sanar a Fadar me martaba inda ala dole aka had'ani da Maryama wacce a lokacin itama tana gargarar haihuwa. Dukda azabar datake ciki hakan be hanata d'agowa ta kalleni ba tace cikin bak'in ciki

"Yanda kika b'oyemun wannan mugun cikin dake jikinki sena nuna miki iyakarki idan har na haifi Mace ke kuma kika haifi Namiji" Bance da ita komai ba kawai na kawar da kaina abinda nakeji a lokacin ya isheni, haka inaji ina gani aka sallami masu taimakona ya rage dagani se ita sekuwa Ungowar zomar dabata amsa umarnin kowa sena Sarauniya Maryama. Itace ta fara haihuwa kafin ni sedai Na mace ta haifa, akan idona ta kawar da kanta gefe sanda aka nuna mata yarinyar sannan tace

"Banason ganin ta tazone takanas danta wargazamun shirina, so take ta lalatamun duniya ta, tanason kafawa bayana mummunan tarihi, inzo in k'are da haihuwar mace! Akan me gwandamun mutuwar ta da rayuwar ta akan rayuwar ta" Ungowar zoman ce ta soma bada hak'uri tana ban baki, a lokacin nikuwa wata azababbiyar nak'uda ta tasomun wacce tasa nakusa fita hayyacina koma ince na fita hayyacina! Cikin ikon Allah sena haifo yarona Namiji santalele me tsananin kamanni da yayunsa marigaya, koda na dawo hayyacina abinda suka bani shine abinda yafi bani tsoro Maryama ce rik'e da yaron tana murmushin mugunta, ta kalleni kallo me kyau tace dani

"Surbajo ya rage naki ki zab'i d'aya daga cikin biyu abinda zan fad'a, kindaiga iyani dakene se Ungozoma a d'akin nan ko? To kodai ki amshi wannan yarinyar data rigada ta mutu a matsayin abinda kika haifa kokuma wlh tallahi summa tallahi billahi in kashe yaron nan har lahira yanzu yanzu in sauya akalar zancen, zance kin haifi mace kin kashe danna haifi Namiji, kuma kin had'a harshi muna k'ok'arin k'arb'arsa kika kashe shi zan sokawa kaina wuk'a a kafad'a duk ince kece kika sokamun, kinga dai gaba d'aya bayan kinyi asarar d'anki zakuma kiyi asarar mutincin ki k'arshe kema a kasheki a banza" Cikin bak'in tashin hankali na mik'e jiri yana d'ebana nace cikeda rauni

"Maryama wace irin mara imani ceke wai? Yanzu jinjirar nan kasheta kikayi? Hankali a tashe na karb'i yarinyar hannun unguwar zoma ina kuka ita kuwa seta baiwa unguwar zoma jinjirin hannunta tace

"Yauwa yanzu kinga 'yata tana hannunku, tsaf dani na shiga wanka in kimtsa kaina in fito na tarar kin shak'eta har lahira ta mutu kin kuma ce nice na kashe miki 'ya'ya shisa kika kashe tawa! Ya kikaga wannan wasan? Ina sharar k'wallah nace

"Keda Allah Maryama, Allah yafiki wlh, muguwar mace kawai" Wata dariyar shak'iyanci tayi ta amshi jinjirin nawa ta matse masa hanci a haukace nayo kanta nayi wurgi da gawar jinjirar ina k'ok'arin k'watar yarona  a hannun ta, kawai se gani nayi ta baiwa Ungozomar yaron da sauri ta k'wallah uwar k'ala take matan dake waje da kuyangi sukayo d'akin tana kuka ta kasa ciro jinjirar ashe a tafasashen kaskon ruwan zafi ta fad'a ban kulaba Allah ma ya sani, ganin sun shigo ta nuna yarinyar tana kuka tace

"Kunga Surbajo ta haukace, sabida haihuwar mace Surbajo ki d'auki d'anyar jinjira ki wurga a ruwan zafi dan zafin kishi a dole sekin haifi magajin sarki, ni sanda banida d'a banda jika kike hayayyafa haka kikaga nayi musu? Take wurin ya d'auki salati aka ciro yarinyar, wata tace zataje ta sanar, nidai gaskiyar datamun yawa ta sanya banje komai ba, kallon marar Maryama tayi

"Ku rufa mata asiri,abarshi akan bisa kuskure yarinyar ta su 'buce mata,ni ina tausayin ta na tabbatar tab'in hankaline ya sameta amma kubar nan wurin da jinjiri na, karta hallaka shi, ban yarda koda kallom sa tayiba, kishi ze iya sakata aikata komai dan haka da sauri kubar nan wurin dashi" Inaji ina gani suka gudumun da yarona ko nono ban bashi ba! Haka ina zaman zamana akazo da Likitan gargajiya ya dubani yace na samu tab'in hankali, maryama seta ziyarceni da sunan dubiya tace duk na kuskura nace da hanakali na seta hallakar da Jinjiri na dake hannunta har lahira, indai inason ya rayu tokuwa sena kawar dakai daga gareshi! Akan tilas na rayua haka dan inason yaron dako ganinsa ban tab'ayi ba ya rayu a duniyar nan.

Sanda Hafsa tazo nan abada labari sadda kabta tayi a k'asa ta dinga rusar uban kuka tamkar babu gobe! Hankalinta a tsananin tashe, Hammood ma kukan yake su Data kowa yayi shiru dan a yanda Hafsa tayi laushi ga alama sesun bata break na 1 hour!!!

Mom Nu'aiym.

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora