SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS

828 117 21
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*Sak'on gaisuwa zuwa gareku mutanen Daraja kuma nagartattu, Lallai na aminta ita darajar gaskia ta Allah ce, Allah ya saka muku da alkhairi masu alk'alamin daraja, Nu'aiym yana matuk'ar godiya da addu'o'inku da kulawarku da kuma jajircewa, bazamu manta dakuba Sister Batul Mamman, Ant Mejidda musa, antyna Zuwaira maman ja'afar, Ayusher muh'd, Maman khady da sauran wanda ban ambata ba, Allah ya karrama darajar ku ya d'aukaka darajar alk'alumanku, ya saka da alkhairi.*

*Sak'on gaisuwa na musamman zuwaga d'aukacin mutanen duniyar kafar sadarwa ta whatsapp, ubangiji yanda kuka hana wayata sakat da kira domin jin labarin lafiyar Nu'aiym ya hanaku bak'in ciki duniyar sa da lahirar sa,Allah ya saka da alkhairi yabar zumunci, tabbas kun  nunamun halacci kun tabbatar mun da cewar ina zagaye ne cikin nagartattun mutane, Allah ya biyaku da aljanna mad'aukakiya.*

*Anty Ramla @ mai dambu, inji Nu'aiym yace a gaisheki da k'ok'ari.*

*SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS*

    28.

Yanayin shigar sa irinta mutanen Niger, yanayin sa gaba d'aya tamkar wani bak'in buzu, gaba d'aya kayan tarkacen sanduna ne ajikin sa, d'auke da kaya tare da matar sa d'aya wacce itama kallo d'aya zaka mata ka tabbatar cewar wannan wata yankice daga cikin bak'ak'en buzayen Niger,adaidai k'ofar gidan ya zauna saman wani banci inda matar sama ta zauna, Detective ne yazo yana fara'a ya tarbesa da cewar ya hanya, dama shi yake jira yau me gadinsa zebar gari yayi tafiya inda me gadin ya fito da kayansa shi kuwa har yana musu sallama iya securities kawai ya bari dama basa zama seda me gadi dayake buzu! Kai tsaye ciki Data ya shiga dashi har zuwa cikin parlor, daga waje kuwa yana d'aga murya akan cewa Maharazu me gadin sazeyi tafiya

"Kayi rana a wannan tafiyar, nizan nuna masa komai karka damu ka tafi abunka kawai,maharazu me gadi se godiya yake kafin yabar wurin.

  Gaba d'aya Hafsa bata cikin walwala amma hakan be hanata shek'ewa da dariya ba ganin Ayatullahi a yanayin sa, zama tayi kusa da Laura sannan tace

"Gaba d'aya Ayatullah duk yanda nake tunanin hikimar ka ka wuce nan, ko a ina ka samo wannan attire d'in acikin sa'a d'aya? Murmushi yayi

"Ranki ya dad'e ai irin wannan ai ajiye suke,dama kawai muke jira" Murmushi Detective yayi danya gane Ayatullahi mutumin amana kenan, yana aiki dashi sosai bedai furta bane ba

"Kana k'ok'ari sannunka da fama, akwai babban abinda yake gabana ayanzu bayan wannan, yanzu taimakon dazaka mana shine ka bamu dukkanin bayanan damuke buk'ata, menene labarin yallab'ai Jay bayan da suka kamani" Zaman sa ya gare sannan ya d'akko burgamen sa ya janyo Laptop yayi jone jonen sa kana ya zaro wani gajeran memo ya kalleta yace

"Zamu fara da b'angaren dakika bani aiki a kansa kafin faruwar komai sabisa kisan irin bayanin da zakiyi, magana ce akan Bilal, tunda wannan abun ya faru ban rage komai ba na dangane da bibiyar sa harna samo wasu daga cikin muhimman abubuwan danake buk'ata game dashi, da farko dai gobe zeje gidan Momynki acikin dare shida wasu 'yan fashi, ya sanar dasu mahaifin sa yanada garkuwa amma wacce mahaifin sa yasanya aka masa tafi ta mahaifin k'arfi, dan haka ze masa rauni tunda yafishi k'arfi abinda yace zasuyi acen shine. "Da farko yace idan sun shiga gidan Momy zasu tutsiye ta acikin matasan 'yan fashin nan dazasu ziyarci gidan ko wannen su seyayi amfani da ita susu bakwai ne, yace shima zeyi shine ma farko" Da sauri ta kallesa jikinta ya soma b'ari

"Meke kan Bilal ne wai, bashida hankali ne kokuma d'an iska ne? Tayaya zeyi wannan tunanin, to shikam akan Momyna k'addara irin wannan ta fara afkuwa ne dabaze k'yale taba? Yana cikin nutsuwar kansa kuwa?" Kanta ta dafe jin yanda jijiyoyin kan nata ke harbawa da sauri ta zauna amma bata k'ara cewa komai ba se dafe kan datayi shi kuwa yaci gaba

"Bayan wannan sunce zasu kwashe duka gwala gwalan dake gidan, duk wani ko takardun gidaje kona filaye data mallaka zasu kwashe shi su gudu dashi sannan yace saga k'arshe zasu kashe ta, ze dab'a wuk'a a k'ahon zuciyar ta so yake tayi mutuwa mafi k'ask'anci itace ta b'ata masa rayuwar sa, dan haka bayan ya kashe ta, ze binneta acikin gidanta ya gudu yanda musulmi bazasu sallace taba, a cewar sa gawarta bata musulma bace ba! D'aga masa hannu tayi alamar ya isa, sannan tace

"Barni in gama da wannan matsalar tukunna, wannan ma ya isheni, na saurara da kyau naji duk abinda nakeso naji akan maganar, yanzu bani wayar ka ta sirri" kallon ta yayi sannan yace

"Suna bibiyar dukkan wayoyin datake amsawa, a shirye suke tsaf domin cimma burinsu, naso in tsayar da abun, amma yin hakan babbar illa ce, zasu iya fahimtar ta fahimci wani abu su sauya akalar shirin su" Dafa kai kad'an tayi kafin ta d'ago su had'a ido sannan tace

"Kace gobene ko? Murmushi yayi "Gobene fa, haka naji sunce" Jinjina kai tayi

"Rabu dasu suje goben mu gani" kallon ta Data yayi yana mamakin ta

"Wawtar zaki k'ara yi mana kenan" Mirmushi yanzu kam tayi

"Kawai Bilal ne yake bani tausayi wlh, gaba d'aya bashida hankali baya neman yin sa, ya takura akan an zalince sa ba'a ragowa shi Allah ya raga masa? Gaba d'aya maganin sa zanyi wlh" Hannu Mood yasa ya rik'o hannun ta

"Kinsan condition na rashin lafiyarki, kinsan gabaki d'aya kanki baya jurar abubuwan nan mesa kike son d'aurawa kanki abinda bashi kenan ba? Hannunta daya rik'e dayanayin  dayayi rik'on ta tsaya kallo wani abu ya tokare mata mak'oshibta data rasa ko meye abu d'aya ta sani ya kusa ya sanyata amai sabida yanda takejin tsananin d'aci a mak'ogwaranta

"Koma mezai sameni kanada asara ne malam? Ina tuntun tuni kakeso kaga na shek'a lahira, wane gadon asibiti ne baka kaini ba da hannun ka, malam dan Allah dont try to act smart with me, i know very well how u hate dislike me so save those acts, watarana ze maka amfani" A hankali ya janye hannun sa akan nata, sannan ya kalli Ayatullahi yace

"Idan ba damuwa karta san saura  matsalolin sabida batada lapia ba'a sonta da yawan damuwa" kallon Ayatullahi tayi

"Ayaa kamun bayani rabu dashi kawai kaji" Saukar da kansa k'asa yayi kafin yace

"Shi Bilal d'in ainasaka an sacemun shi a yanzu haka yana hannuna a damk'e, bayaga haka matasan da Baba me gadin gidan momy ya damk'e suma duk suna hannuna kuma wuya tasanya sunyi bayani, abinda yake matuk'ar d'auren kai anan fa shine gaba d'aya yaran nan sunce Uncle ajay ne ya turosu su kashe Hafsat, Bilal banida lokacin sabisa abinda nakeso namar shine k'arshen tutiyar sa" kallon sosai Mood yayiwa Ayatullahi

"Mesa kuke neman zautar dani ne wai? Tayaya zakuke alak'anta mafari da tushen matsalolina ga mahaifi babban uba kuma uban riko Jay, kanku d'aya kuwa" Murmushi yayi agefen bakin sa kafin yace

"Wannan itace wowtarka ta farko yallab'ai, bazan tsaya mu b'atawa juna lokaci ba  amma tabbas, da Jay da kuma Mamin ka sune suke neman ranka rai da rai, inada cikakkun hujjoji akan hakan" Kallon tuhuma duka d'akin sukayi masa kafin Mood cikin fusata yace

"Hafsat wannan wane irin wasane? Dama ba taimakona kikayi ba k'ara jefani a rud'ani kike? Kuskurena na farko shine sakin jikina dake, yarda dake shine wowta na ta farin, tayaya mahaifiyata anya Hafsat kanki d'aya kuwa" Duk'ar da kanta tayi a k'asa cikin sanyin jiki sannan tace

"Yaya zanyi dakai idan baka aminta dani ba Mood? Bazan maka tilas ba babu uwar komai a tsakanina dakai a wannan lokacin kakkab'ewa zanyi in barka ka rub'e,bari kaji tundaga kan ummi har Jay bame k'aunar ka, bansamiba koka tab'a sanin Zulaiha matar sa matsalar kace,ban saniba koka tab'a bincikar asalin zulaiha, koda yake bazaka aminta ba harseka tabbatar da cewar shida kanshi shine yake hanawa Barra d'aukar ciki idan kuma ta samu ya zubar, kai bari kaji a tsakanin wannan lokacin dabadan tsoron harsashin bundiga ba dana tashi gaba d'aya masarautar ku na baka sarautar dake mallakin ka na kashe kowa ciki har Ummin ka!! D'an kwalin dake kanta ya cinzge idan nan ya kad'a yayi jajir ya damk'i sumar kanta tare da mik'ar da ita a tsaye cikin tsananin fusata yace

"A yau senasan wanda ya turoki arayuwata kuke yawo da  hankalina kona kasheki yanzu anan" Hannunsa ta rik'e yayin da su Data sukayi kansa suna aikin ya sake ta!!

*Wannan sak'one ba oage ba,sak'on gaisuwa zuwaga masoyana nanda anjima kad'an page ze sauka inshaa Allah, dukda na rigada na masa lak'ani da shafi na ashirin sa takwas,sekun jini, yanzu ba charge ne a wayar.*

Mom Nu'aiym.

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora