SHAFI NA ASHIRIN DA TARA

818 122 19
                                    

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA ASHIRIN DA TARA*

Data ne ya k'waceta yana kallon sa cikin tsananin takaici.

"Mekenan kakeyi Hammood? Kanka d'aya kuwa? So kake ka kashe 'yar mutane, tsuntsaye ne a kanka ko k'wari? Yana hushi yace

"Bakajin metake cewa? Bakajin metake gayamun? Ummi na take alak'antawa da muggan kalamai, uwa fa, kasan meye uwa kuwa? Runtse idanta tayi kafin ta bud'esu fess a kansa

"Banaji kanada iko ko hurumin dazaka k'ara kai hannunka jikina immaka banza, idan izgilanci ya kuma turaka kamun wannan shirmen wlh rashin kunya me balaga zan maka, tsammani kake kafi zuciya kome? K'ura mata ido kawai yayi batare da magana ba a fusace tace tana kallon Data

"Uncle idan wannan baze sauraremu ba zamubar nan yaje yanemi maganin matsalar sa da kansa, nifa banida lokacin dazan b'ata anan" Rik'o hannun sa Data yayi sannan yace

"Hammood karka k'ara cewa komai, bari muji abinda sukazo dashi" zama yayi yana sharce gumin fuskar sa, hafsa tana kalla masa harara cikin nutsuwa tace.

"Sanda rayuwa tayi tsanani a gareni a duk fad'in gidan sarautar masarautar daulatul dinar ban samu majingina me kyau ba se awurin dattijuwar alkhairi wato Bahar Sarauni. Banyi wani zama me tsayi da ita ba ma fahimci rigimarta babba ce sedai komai nata akan tsananin gaskiyarta take yinsa, nasha farkawa acikin talatainin dare se in tarar da ita tana kuka wasu lokutan nikan tarar tana d'aga hannayenta asama tana addu'a tana kukan dana rasa dalilin sa, gashi a d'aki d'aya muke kwana sabida yanayin ciwona, sedai na fahimci  tsantsar damuwar datake ciki. Wasu lokutan nikanyi alwala inbi bayanta muyi sallah intana addu'a ina binta da Ameen, wasu lokutan tana nuna bataso haka nake nacewa hardai wata rana nayi nasarar zama da ita donjin matsalar ta.......

"Bahar wai nace dan Allah menene yake damunki  kike yawaita kuka, kinga wata rana dana raka uwar rik'ona asibiti abinda likita ya fad'a agabana shine, shekarunta yana ja, tadena sanya damuwa a ranta kar hawan jini ya kamata, kinga ke kinmafi Momyna tsufa zanma iya cewa kin haifeta ko wanda yafita meyasa kike tunani? Meyasa kikeso ki janyowa kanki wani ciwon" kallon Hafsat bahar tayi sannan cikin tsananin damuwa tace

"Da shekaru na tsufa kusan saba'in da d'oriya zan iya cewa inada cikakken darasin dana haddace akan rayuwa dakuma abinda rayuwar ta k'unsa musamman sha'anin daya dangaji abinda ake kira D'an adam da halayyarsa, na zauna da mutane iri iri, na rayu acikin dubbun dubatar motane wanda gaba d'aya sukayi sanadiyar shigata wannan halin, acikin duniyar dana rayu, k'alilan ne suka bani farin ciki, k'alilan ne suke sona, duk ranar da akace  yau Allah yayi maka d'aukaka ta mulki, sarauta, kud'i koyaya suke to rabi da kwatan hak'oran dake haske agabanka inka lek'a k'asansu duhu ne, shekara da shekaru ina tsintar aya, shekaru masu yawan gaske na rayu kaina a duk'e ina faman cinye tsakuwa daga cikin aya amma tamkar k'ara watsamun ita akeyi, Hafsa ina cikin damuwa, rok'on Allah nakeyi koda wane lokaci ya nunamun ranar da zuri'ata zata zauna lafiya a masarautar nan kozan samu kwamciyar kabari cikin kwanciyar hankali bayan raina" Cikin tausayawa Hafsa take kallon Bahar kafin cikin tsananin nuna so tace

"Bahar ni wannan hausar taki sam bana ganewa, gaba d'aya kin batar dani dan Allah ki bani labari akan matsalar ki" Murmushi irin na manya Bahar tayi sannan tace

"Ba labari na zan baki ba, zan baki labarin gaba d'aya abinda ya shafi wannan masarautar da tarihin rayuwa ta a tak'aice" Gyaran zama Hafsat tayi

"To Bahar tawa ina jinki"

"Asalina ni cikakkiyar bahaushiya ce wacce tarihin jinin rawani yake zagaye dani a k'ark'ashin masarautar Bauran dawa dake mulki b'angaren yankin Baura a wajejen saharar bahaushe dake yankin nan, gaba d'aya ni tuwo ce me lillib'e da miya datasha manshanu wanda aka dafa aka soya da zallan albasa tare da watsa kanwa acikinsa don kashe tsaminsa, domin kuwa iyaye da kakannina a sarauta muka tashi, tun kafin mulki ya zama wata tsiya ahalina suke mulki a k'asar hausa, a yanda tarihi yazo  kakan kakanmu yana daga cikin wanda suka taya shehu yad'a addinin islama a sanda yazo mana dashi.
   Mahaifina yanada 'ya'ya maza guda hud'u seni mace jal da Allah ya bashi wanda kuma duk a cikin matayen sa mahfiyata kad'ai ce da wannan jerin se kuwa kuyanga d'aya data haifi mace itama aka 'yanta ta ta zama me fad'a aji dalilin haihuwar ta, na taso abar so awurin mahaifina ya sanya mun suna Salama tu sabida shine suna awurin uwar haihuwar sa, ya nunan gata sabida nice sanyin idaniyar sa a wannan lokacin, yayinda sarakuna suke tsananin son ganin sun samu magaji se Allah ya jarabi mahaifina da son samun magajiya acewar sa mata rahama ne. Seda nayi shekaru hud'u a duniyar mu sannan aka haifi k'anwata Maryama, a lokacin senayi tsaikon samun mijin aure sabida mahaifina yace baze barni in auri kowane b'eran dawa mara gata ba, haka wata rana bazan manta ba yak'i  ya b'arke atsakanin masarautar mu da yankin arewan daular wannan masarautar danake ciki alokacin inada shekaru sha uku a duniya, haka akazo se akayi rashin sa'a yankinmu sunata fad'uwa ana kashe mana sojojin yak'inmu, dan haka se mahaifina ya nemi sulhu a maimakon ci gaba da zubda jini, a zaman sulhu ne Allah ya kad'oni shaidawa me martaba mahaifiyata tana kakarin mutuwa dan muna tsammanin guba taci, duk yanda akaso a ceto ranta inaa magauta sunyi nasara akanta sun bata guba taci dama tare da sarki takeci takesha, to wannan sha'anin yak'in ya sanya dole takeci ita kad'ai se sukayi amfani da wannan damar suka kashemun uwata abar sona, anan ne d'an sarkin Daular nan na wancen lokacin yace shisam aduniya bega matar aure ba saini, dan haka ana ihun mutuwar uwata suka nemi a aura masa ni kosu tashi yankin mu, mahaifina yana cikin bak'in cikin rashin mata mafi soyuwa agareshi segashi kuma anaso a rabashi da 'yarsa dayafiso ta K'arfin tuwo kuma a irin lokacin dayake cikin d'acin rai! Badan yaso ba ya zab'i zaman lafiyar yankinsa akan soyayyar 'yarsa da farin cikin sa dana 'yarsa wato ni Salamatu. Zuwan da akayi dani wannan Daular sena fahimci a yankina mun gaji mulkine amma tsagwaran mulki ga inda akeyin sa nan. Gaba d'aya komai se ammaka sannan duk inda ka juya hararace, ina zuwa sirikata tashi masifa akan lallai se an aurawa Marwan 'yar k'anwarta dake masarautar Jijiga kamar yanda tun farko aka tsara, dan haka inaji ina gani akamun kishiya da wuri, Marwan yana matuk'ar sona tun bana sakin jikina dashi harnima nazo na cire d'ard'ar muke matuk'ar son junan mu, b'angaren Jaruma kuwa kamar takasheni dan kishi, ban damu ba sirikata bata sona amma se Allah be mata tsawon rai ba dan haka na samu sassaucin azaba nakeji dana Jaruma kawai har Marwan yazo ya karb'i sarautar garin nan wannan itace tushiyar komai!!!

TSINTAR AYADove le storie prendono vita. Scoprilo ora