SHAFI NA GOMA SHA SHIDA

829 153 19
                                    

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

     *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA SHIDA*

        Kawai tsayawa yayi yana kallonta sanda take haki alamar tasha gudu, yanayin idanta dariya ma yaso bashi, ya kula hafsat rigimammiya ce tak'in k'arawa, tanada neman tsokana ainun, batada tsoro sam sannan bata b'oye b'oye, idan dai akan gaskiyar ta take tokoda kasheta za'ayi zata tsayawa kanta, zuwa yanzu ya soma gane cewar bazata dena sakashi gudu ba, shikuwa gudun dama tammar jiransa yake, duk sanda yaga ta ruga idan ba binta yayiba  ba dad'i yakeji ba, hannunta ya sake, itama seta tsaya tana kallon sa, turo baki tayi gaba

"Idan kaci zalina Allah yana kallon ka" D'an zabura yayi tamkar ze kuma rik'ota ta arce da gudun fanfalak'i batako waigo saba, daidai titi Bus d'insu ya tsaya, da sauri ta shige tana lek'ensa, shi d'inma tsaye yayi har seda Bus d'in nasu ya b'acewa ganin sa, yana juyawa ya koma ciki da murmushi d'auke a fuskar sa kawai yayi karo da Khairii, d'anja baya yayi ya akayi besan da zuwan taba, ko k'amshin turarenta ma beji ba, koda yake gaba d'aya daddad'an k'amshin arab oud na hafsat ya gama mamaye ilahirin wurin, had'e fuska tayi

"Abinda kace zakazoyi kenan, nifa na soma zargin kamar soyayya kuke da yarinyar nan, bini bini ka bita da gudu sekace kuna wasan tsere, nasan cewar gudu halittar kace a cikin jinin jikinka yake amma why always Hafsat? idan kudu kakeso kayi tare da wani banida nauyi ai as u can c, kawai ka shirya mu ringa wasan b'uya, am very good at hide and sk game, after that kuma kana zuwa wurin Hafsa u just grab her hand bazaka iya marinta bane meye na tab'ata tun farko?" Sororo ya tsaya yana kallon ta amma harta k'araci surutan ta bece da ita ci kanki ba, rab'awa kawai yayi ta gefenta ya wuce, bin bayansa tayi har suka isa cikin gidan bakinta be mutu ba masifa kawai take, shi hankalin sama baya jikin sa, gaba d'aya tunanin sa ya ebesa ya kaishi wata duniyar....A b'angaren Hafsat kuwa tunani take anya Man d'in nan kansa d'aya kuwa ? yaya ze rik'a wani kwasowa a guje duk sanda ta tserewa muguntar sa? yanayin gudu sekace d'an shekaru sha biyu, wata zuciyar tace da ita kekuma me 17yrs kina tik'ar uban gudu ace dake me? lokacin da suka tsaya station nasu Cylia suka d'aukesu bata hak'uraba seda ta baiwa  cylia labarin Yaa Mood sarakan tsere, nan suka dinga dariya abinsu, duk abin nan har yau Hafsat bata tab'a gayawa k'awayen ta labarin wani abu daya shafi gidan suba, ita dai kullum Bahar ce abakinta granny d'inta sekuwa Yaa Mood wanda koda yaushe cikin bada labarin tserensa akeyi.

**************
    Gabaki d'aya anrasa gane kan meke damun Barra, Gadai ciki ajikinta amma gaba d'aya banda zubar jini babu abinda takeyi, Bahar ta shiga rud'ani dan kuwa har an dawo mata da Barratu a b'angaren ta, yau abun yafi k'arfin nako yaushe dan kuwa tun cikin dare jini yake b'ulb'ula daga jikinta, hankalin Bahar da Jay ya matuk'ar tashi hakan ya tilasta musu d'aukar ta su kaita asibiti, abin mamaki shine likitoci basa ganin komai, duk wani dake jikinta yana nan lafiya lau musamman cikin dake jikinta, ba laifi tana shan addu'a iri iri awurin bakuna masu yawa sosai, dan kuwa mahaifiyarta a tsaye take k'ik'am tana mata addu'a. Zulaiha da yayarta ce suka kawowa Barra ziyarar dubiya a asibiti wanda sosai suka jajanta yanayin ciwon Barra, barinsu d'akin keda wuya suka had'a hannu suka tafa, Anty Safara'u ta kalli k'anwarta tace

"Ba se idan mun yarda zata haihun ba, tayaya munzo mu k'wace gida mu kuma sake baki wata jaka tazo ta shiga gabanmu, dacen tasan zata haihun tajira seda kikazo kika kasa" Murmushi Zulaiha tayi

"Tokuma ai anty safara kinji boka yace ze kashe d'an cikin nata ni kuma ze bani ciki" Dariya suka bushe dashi Safara tace

"Ki bari Boka yana kashe mini canjina da yawa, shegiya tayita sumy sumy da ita kamar ta Allah, nina tabbatar tana shiga bokaye ace duk kayan matan dakike sha itace miji kewa cin tuwon mayunwaci, ke kuma sedai ya lasa ya mik'e" Cikin k'unan rai adaidai lokacin dasuka shiga mota suka zauna Zulaiha tace

TSINTAR AYAWhere stories live. Discover now