SHAFI NA TALATIN DA TARA

590 80 3
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA TALATIN DA TARA*

          39.
Daƙyar ya yi aikin rarrashi, sannan yau Hafsa ta tabbatar wa kanta wannan rayuwar itace zaɓin ta, meyafi daɗin ayi maka wanka, a san ya maka tufafi bayan an lafce ka da man shafawa.

  *SAFIYA*

Ƙarfe takwas na safiyar rananr agidan tayiwa Bahar, tazo ta tarar Hafsa tana bacci, Mood dake falo ta harara kafin tave tana taɓe baki "Kai ina Jikata kums ƴata" Girgiza kanshi yayi kafin yace "Ohh matata wai? Bacci take meye?  Dundu ta ɗaka masa a baya

"Ja'irin yaro ni zaka gayawa sanabe? Matarka ma kake gayamun, zakamun bayani ko kuwa, yau inaga ka ɓalla mata ƙafa ɗaya ko? Murmushi yaƴi sannan ya gyara zaman sa

"Dama wurinki zanje yanzu, maganar Hafsa. Jiya Momyn ta tamun waya akan maganar mahaifiyar ta, nasha mamaki sosai wannan ya sanya nake cewa zanje nayi ƙwaƙwaran bincike akan hakan, ban gama aminta ba" Kallon sa tayi cikin mamaki sannan tace tana kaiwa zaune

"Meta sanar mata ne? Gaba ɗaya ni bata sanar dani akan komai ba" Murmushi yaƴi sannan yace

"Idan aka motsa kice Jikar ki ƴarki, gashinan dai kinga nafiki matsayi a gunta" kallon takaici tayi masa kafin tace,

"kaga zaka gayan ne ko kuwa?

"Bahar kinsan meta sanar dani? Tsaki taja cikin masifa tace "Dole in sani mana tunda abun saukar wahayi ne" Dafa kanshi yayi yana dariya kafin yace

"Cewa tayi ƴar sarkin fulanin wuro ce taya haka zata kasan ? Magana take akan Masarautar Sarki Me Fura, Malam Arzika Djoro" Shiru Bahar tayi kafin tace "Tunani na bawai akan gaskiya ko ƙaryar abin bane ba, tsananin kamannin Hafsa da kuma Surbajo nake hasashe kamar karka ambaci Sarkim Fulanin Wuro" kallon ta yayi da mamaki "Surbajo kuma da Hafsah? Tayaya? Gyaran zaman ta tayi kafin tace

"Surbajo da kake gani mahaifin ta shine tsohon Sarkin fulanin wuro me rasuwa, a yanzu haka ɗan sa ne akan  mulkin wato Arzika Modibbo Djoron daka faɗa, ita sunan mahaifin ta Modibo Djoro,abin ma daya ƙara kawoni shine akan matsalar ita Surbajon, sam bata maganar gida idan na mata maganar seta saka kuka tamkar dai am mata kurciya" Ɗan kallon Bahar yayi cikin mamaki sannan yace

"Kaina ya ƙulle sosai, tayaya haka zata faru? Babu shakka Ubangiji me girma da ɗaukaka ne, idan har ya zamana Hafsa jinina ce to ko tabbas zuwanta a rayuwa ta akwai wani dalilin, ambatar kalmar kamanin da kikayi tanayi da Surbajo seyaja tunani na zuwa ga kawo siffar Surbajo a kusa, tabbas murmushin su kaɗai yana kamancece niya dana juna" Nisawa Bahsr tayi ƙafin tace

"Maza tashi muje wurin.Momyn tata, inason sanin gaskiyar labarin" Miƙewa yayi  ya shiga ciki ya ɗakko key sannan yazo suka bar gidan.

**************
   Lokacin dana koma ƙauyen dana dakko hafsa da sunan zan bata haƙuri akan abinda ya faru senayi rsshin sa'a dajin akasin labarin abinda nake tsammani, gaba ɗaya Bilal ya lalata sunan Hafsa ta dawo mara tarbiƴa a idan dangin ta, haka fito gwiwa a sace sedai me kakarta wacce ta haifi ubanta wato Baba suwai seta janyoni gefe tace dani

"Barira akwai abinda nake so in gaya miki akan Hafsa" Nan take cewa dani,
"Yarona Kabir ya taso yana son kiwo sosai mu kuwa gaba ɗayan mu nan gidan maƙera ne bama noma baku ma kiwo. Yasha wahalar duka da kyare akan yaƙi gadon gidan su awurin mahaifin sa da kuma sauran ƴan uwan sa, amma sam.be saka yaja baya ba, ni kaina nayi dukan nayi faɗa amma a banza, dukda ni bawai na hanashi kiwo bane nace ne ya haɗa da ƙirar amma sam seyace bazeyi ba, nayi rashin sa'a ne Kabir yanada kafiya! Haka girma yazowa Kabeer yace tas matan garin nan bayaso kowa se wata Nufaina ƴsr ƙauyen tsallaken nan wacce gaba ɗaya mahaifinta da Jere me ƙira basa shiri haka yarinya ma ta kafe amma me se kawai suna zuwa da maganar iyaye suka ce basusan zancen ba, shekarar su biyu suna faman neman ysnda za'ayi amma ina kowa mahaufin sa ya dage. Wata rana muka tashi wuni cur ba kabeer! Babu wanda ya damu saini, dik rintsi  baya magarib a ko ina sai a nan gidan amma ranar shiru, muna nan sega samari maza daga ƙauyen mijiye sunzo neman wai ƴarsu da makmai akan Kabeer ya sace ta. Nan aka shiga nema da ban baki amma ssti guda ko labarin wanda ya gansu bamu jiba, hankalin kowa ya tashi akayi ta neman har aka haƙura babu labarin wanda ya gansu ma. Watanni suka wuce har wata goma sha ɗaya kullum ba dare ba kuma rana addu'a nake akan dawowar su, katsam rana guda sega su a gidan mu a tare amma tare da jinjira a hannu! Nan take ƙauyen nan ya ɗauka akan sunce sun dawo da shegiya! Sukayita rantse rantse babu wan ya saurare su seni bayan sati biyu na saurari kabeer sabida tausayin yarinyar datake a yashe kullum bame kulawa da ita, dana ɗauketa jere har sakina yayi naƙi in tafi ko ina, haka dai na saurari kabeer ga labarin daya bani.

TSINTAR AYAOnde histórias criam vida. Descubra agora