SHAFI NA ASHIRIN

1.3K 129 31
                                    

  *TSINTAR AYA*   FREE BOOK

    *NA: BILLY GALADANCHI*

*Ohhhh gaskia Reader's kuna bani nishad'i, harga Allah inajin dad'in comment naku dakuma k'aunar dakuke nunawa wannan littafin na tsintar aya, Allah yabar tare..... Wannan shafin gaba d'ayan sa sadaukarwa ne ga duk wata me bibiyar littafin Tsintar Aya, kuyi yanda kukaga dama dashi.*

*SHAFI NA ASHIRIN*

  20.

Gabaki d'aya kanta ba k'aramin d'aurewa yayi ba, tayama za'ayi wannan maganar ta fita? Waye yaje ya buga wannan labarin meke damun wannan gidan jaridar dazasu buga labari kansu tsaye batare da wata hujjar ba? Mik'ewa tayi kawai tabar Fadar sarauniya cikin sassarfa har tana had'a hanya kai daga bisani ma da gudu ta had'a dashi, sedai lungu da sak'o na masarautar mutane sunyi gungu d'aya idan ba wayace a hannunsu  ba to jarida ce, wannan abin ne ya sanya ta k'arawa gudun gudu zuwa na fanfalak'i har zuwa lokacin data iso gidan Hammood, tana haki ta kalli hadiman dasuma jaridar suke kallo tace fuskarta a had'e

"Ina prince mood yake? Kallon ta sukayi sannan d'aya daga cikin su yace

"Ranki ya dade tunda ya dawo daga masallaci be fito daga ciki ba, kai tsaye b'angaren dayake mallakin sa ta nufa a k'ofar parlor sukayi karo yana sauri ze fita, hannun sa ta rik'o batare da b'ata lokaci ba ta juya ciki dashi, shikuwa haka ya dawo tamkar rak'umi da akala be iya hanata ba dukda so yake yaga k'arshen iyashegen ta dan ubanta... A tsakiyar d'akinsa ta sake masa hannu sannan ta waigo gaba d'aya suka fuskanci juna har lokacin huka take na gudun datasha dan haka seda ta d'anja fasali sannan tace

"Labarin dake yawo gaba d'aya a masarautar nan na tabbatar kaima ka ganshi, zuwa kawai nayi in baka shawara k'waya biyu, na farko idan ka fita waje pretend as if nothing happened, i mean bakaga komai ba zakayi kamar bakasan da wannan labarin ba, na biyu kuma karka k'aryata 'yan jarida, am only telling you this because i care in kayi sab'anin abinda na fad'a zaka wargaza komai, zaka basu lasisin ci gaba dayin barazana da rayuwar ka, bance dole sekayi abinda nace ba bankuma ce dole seka yarda daniba wata rana zaka fahimci inda na dosa" Tana kaiwa nan ta juya zata bar d'akin ya damk'o hannunta ya wulwulo da ita ta fad'a jikin sa suka tsaya kallon juna a hankali yace

"U really are a drama queen, so kike ki mayar dani sakarai ko? Aikinki yana kyau sosai, abu d'aya zan.....hannu takai ta rufe bakinsa sannan tace shhhhhhhhhh

"No where is safe in this palace, please no matter how angry you are karka kuma furta koda kalmar A ne a palace d'in nan" Tana kaiwa nan ta k'wace jikinta ta ruga gaba d'aya tabar cikin gida, amma me tana zuwa waje sega dandazon 'yan jarida sunkai su goma sha kowa yazo ne yin magana da Hammood, shi d'inma bayanta ya nufo tun daga bak'in k'ofa daya hangosu seyayi tsaye kawai ya jingina da k'ofar ya hard'e hannayensa  a k'irjinsa yana murmushin dake d'auke d'auke da ma'anoni daban daban....., tamkar wacce k'wai ya fashe a ciki haka ta dinga takawa harta isa gabansu,waigawa tayi ta kalle sa yanda yake murmushi ya matukar kashe mata jiki T bataso ya b'ata mata shirinta taga alamar zarginsa akanta me yawane baze tab'a saurararta ba. Kallon su tayi tace

"Waye ya bud'e muku main gate, kuma waye ya baku izinin zuwa nan ku tashi prince hammood daga baccin sa? Speakers suka kawo kusa da ita da masu waya kowa dai da abinda yake amfani wurin yim recording

"Ranki ya dad'e me zakice game da gaskiyar wannan al'amarin daya faru gameda jita jitan da aketa yad'awa akan k'aryata kurumtar Prince Mood da mutane sukayi? Bataso kulasuba amma bari ta ari action tayi acting kamar actrees ta indian film!!!

"Akan meyasa ku kuna aiki amma kwata kwata bakusan aikin kuba, ita kanta jaridara data buga wannan labarin k'aryar semunje kotu dasu, dan wannan labarine mara tushe? Idan tushensa ? Kuntab'a gani meji yana magana yayi kurumtar k'arya? Akan me sarki me jiran gado zeyi putting up wannan act d'in? Wannan labari ne ya samo tushene daga mak'aryata mak'iyan prince, kunsan duk inda mutum me babban matsayi irin prince yake dole seya samu mak'iya, sabida haka nake baku tabbacin wannan labarin k'aryane, kuma ni matar prince ce, sabida haka kunji daga bakina, koyazo bashida bakin baku amsa koda akwai wanda ya iya maganar kurame ne anan nakirashi seya muku bayani da kanshi? Wanine daga cikin 'yan jaridar yace

TSINTAR AYATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang