SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS

919 118 14
                                    

*TSINTAR AYA*  FREE BOOK

    *BILLY GALADANCHI*

*SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS*

Mik'ewa yae yana zagayar wurin, kanshi ya d'auki zafi sosai, shin a ina Idan fada suka samo wannan yarinyar? Anya kuwa wannan mutum mace kuwa, gaba d'aya be fahimci zuwanta a rayuwar saba a baibai, ta hanasu fad'n abinda suka gani to kenan shiri take akan ta gaya musu da kanta amma se yaushe? Mesa zata hanasu magana akan hakan? Ba yau aka fara zuwa ace yana magana ba, ba yau aka soma ba'a gansa ba aje ace an gansa sabida kawai anaso a tabbatar da zargi, babban abinda yafi damunsa shine besan su waye idan fada ba, amma gashi Hafsat tace tasan su ita, idan har so take tayi wasa da hankalin sa akan idan fada, idan so take ta kwashe sirrin sa ta gayawa Idan fada to yanada maganin ta, zeyi amfani da ita shima, ze wasa k'walwar ta, dama burinsa yasan su waye idan fada, togashi tace ta sansu bara ya barta sesu buga wasan bari ya gani shida ita waye zeyi kaye.

*************
    Shiru d'akin taron ya d'auka ana jiran isowar shugaban k'ungiyar, mutane sunkai su ashirin kowa yayi tsit aciki  talatainin dare, se k'arfe biyu daidai sannan shugaban ya shigo ya nemi kukera ya zauna kowa ya mik'e seda ya zauna sannan auka zauna suka gayar dashi tammar yanda suke gayar da sarkin Daulatur Dinar, bayan yayi gyaran murya seya fara magana kamar haka

"Anyi sanya sosai da aikin da aka baiwa yarinyar nan, ance shekarunta 17 anya batayi k'ank'anta ba? Shiru shiru babu wani k'wak'waran bayani daga wurinta yanzu watannin su nawa kenan a k'asar, tahau jirgin banza taje tanashan sanyi a turai ana bata kudad'e amma aikinta sam baya gudu mekenan muke zaune wangale da baki muna jira? Bazata iyaba a datse mata hanyoyin sadarwa inaga yafi" Seda yayi shiru sannan wani daga cikin su yace

"Inaga ba haka zamuyi ba, zaburar da ita zamuyi, a firgitar da tunaninta yanda aka saba, kada muzo ya samu wani ci gaban amma bamu sani ba" Bece komai ba wani daga ciki ya kuma cewa

"Shugaba inaga a matsayin mu da manya masu kaifin tunani sanadi kawai zamuyi masa daze dawo Nigeria, sanda yake kusa damu ai munyi nasarar shiga tsakanin sa da mahaifinsa,kokuma mu kasheshi kamar yanda tun farko mukaso, a wannan karon semu kashe har sarkin sannan mu namu sarkin seya maye gurbin su, danmu har duniya ta nad'e kaine sarkin mu, kuma da izinin Allah kaine zaka zamto jagoran talakawa nanda lokaci k'ank'ani, ko babu komai mahaifinka shine da sarautar nan bashida wani magaji kuwa sekai" Murmushi yayi najin dad'i kafin yace

"Tabbas lokaci yayi dazan nunawa mutumin nan iyakar sa, nayita kallon hankalin sa akan ya bani sarautar nan tunda gadon ubanace amma shi ta kansa kawai yakeyi se d'an cikinsa, nikuma ya mayar dani ko oho, zargina akan tabbas Hammood yana magana yak'i ya tabbata tunda be tab'ayi agaban kowa na, ansha a bisa masallaci ko shago ko dai wani wurin daba gidaba amma sam baya magana, yanzu akwai mutanen mu a U.S takanas nayi sponsoring nasu suke bibiyar sa amma narasa gano kan yaran nan sunce har acen baya magana, sabida haka kasheshi kawai zamuyi, dama naso ace yana magana ne sena tabbatar sena kashe sa, yanzu kuwa kurman gaskene to kuma uban bashida niyyan hanashi sarautar dukda cutar kurumtar daya gada awurin uwarsa, gwanda baya doron k'asar, gwanda ya mutu in huta da zullumi, amma shin anan zamu kashesa kokuwa?" Wani daga cikin su ne yace

"Shi wannan mutumen dasuke kira sarki bashisa adalci kuma be cancanci ayi masa sassauci ba, mahaifinka rik'on k'warya kawai ya bashi se Allah yamai rasuwa shin base ya mayar maka ba?, A'a sabida zalunci seyayi tazarce yace kai yarone a wancen lokacin yanzu ka hayyafa kayi gemu harya fara zama fari amma yana ihun cewar d'ansa ne magajin sa wannan ai mugun xalincine dan haka jininsa dana d'ansa ya halasta, dama duk wanda yakeso ya gifta maka bayan su" Gyaran murya ya kumayi sannan yace

"A shirya masa mugunta, a shirya masa makirci, a lafta masa k'aya ayi duk yanda za'ayi ya dawo Nigeria shida iyalin sa da ajayi masa auren gata yana kurma, ita gaggawa aikine dake b'ata dukkanin shiri sabida haka bazamu aiki da gaggawa ba, amma iyalansa dayake aure zasu shiga cikin sahihin shirin salwantar mana da tunanin sa zuwa tafiya me gangara" Dariya sukayi dan kuwa duk sun gane yaren seda suka tsahirta yaci gaba

TSINTAR AYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora